← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 71

Sashe 51

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shi wannan wankan da muke yi miki magana a kai ba kamar yadda ake wankan soso da sabulu ba ne, sunansa wankan haila/janaba kuma ya kasaace kala biyu. Akwai siffatul Ijza akwai kuma siffatul kamala. A wankan janaba ta siffarsa ta kamala za ki tanadi ruwa mai tsarki, sai ki karkato da ruwan ki wanke hannunki sau uku. Ki kula! Ba kina zuwa za ki tsumbula hannunki a cikin ruwan ba, sai kin wanke hannunki za ki sake ɗebo ruwan ki wanke al'aurarki tare da ƙudure niyyar irin wankan da za ki yi. Idan wankan haila ne za ki ƙudurta shi, idan na janaba ko na biƙi ne duka za ki ƙudurce niyyarsa. Bayan kin gama za ki ɗaura alwala irin wacce muka koya miki, amma ba za ki wanke ƙafa ba. Abu na gaba da za ki yi sai ki kanfato ruwa da hannunki ki murmurza gashin kanki har sau uku, ki cakuɗa shi sosai yadda ko ina za ji. Sai ki ɗebi ruwa ki wanke jikinki gabaɗaya, sannan kina iya fara wanke ɓangaren dama. Idan kin gama da shi ki wanke na hagu, daga ƙarshe sai ki wanke ƙafarki tun da idan ba ki manta ba mun ce miki alwalar da kika yi a farko ba za ki wanke ƙafa ba." Yarinyar ta jinjina kai cike da gamsuwa. Auta ta ɗora da cewar.

"To kin ga wannan shi ne wanka janaba, ki riƙe bayanin sosai domin babu sallah ga wanda ba shi da tsarki." Godiya sosai yarinyar ta yi musu, cikin ƙarfin hali Auta ta buɗe akwatin Shukra ta zaro pad guda uku ta ba wa yarinyar, ta sake jadadda mata muhimmancin tsaftace jiki a lokacin jinin haila.

Sallah suka tayar ita kuma yarinyar ta fice domin gyara jikinta, tana mamakin irin duhun jahilcin da ta dinga aikatawa a baya.

"Maganar gaskiya iyaye da yawa sai sun tsaya a gaban Ubangiji, ki duba ki ga yarinya kusan shekara goma sha bakwai amma ba ta san yadda za ta aiwatar da ibada a karan kanta ba?" Auta ta yi maganar a lokacin da suka ƙarasa can reception, Uwani ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Gaskiya dai kam da matsala, abin takaicin ma wai wani can tsoho mai mata za a aura mata. Kuma a ɓangaren iyayen aikin nasu su ma suna da laifi wallahi, yaro ko ba kai ka haife shi ba atleast ka ba shi ilimi ko iya na addini ne. Ki duba fa ki gani, sallah wannan ba ta gama sanin yadda ake yin ta. Allah Ya kyauta." Uwani ta ƙarasa maganar tana tsaki.
Kiran Aunty ne ya shigo tana tambayar jikin Shukra, sannan ta ce Uwani ta kwatanto mata asibitin za ta ƙaraso idan ya so su sai su koma gida.

Shukra na zaune ta fara jin ƙasan mararta da bayanta yana ci gaba da karta mata, sannu a hankali take jin ciwon na ƙaruwa. Lokaci ɗaya wani gumi ya shiga karyo mata, jin zafin ciwon ya sa ta katse video call ɗin da suke yi da Salim wacce suka shafe sukan awa guda suna hirar soyayya. A daidai wannan lokacin ne Dr ya shigo, sai da ya yi wa Shukra sannu sannan ya ƙarasa wurin ɗayar matar don ta galabaita sosai. Safar hannu ya sa ya duba matar sannan ya ce.
"Sannu kin ji, kina gab da sauka In shaa Allah nan ba da jimawa ba." A wahalce matar ta É—ago shanyayyun idanunta ta ce.

"Dr ni dai don Allah ka yi mini CS ko na huta da wannan wahalar."
"Yanzu haka kina 8cm fa In shaa Allah nan ba da jimawa ba za ki iya sauka. Zan turo nurses yanzu idan na fita, za su tsaya a kanki." Ba ta iya amsa masa ba don saboda zafin ciwo komai da kowa ma haushinsa take ji. Gaban gadon Shukra ya ƙarasa, a lokacin da ya tsaya ta jiƙe sharkaf da gumi. Ga man da aka lafta mata a wurin gyaran kai sai gangaro mata yake yi, tun da ya ƙarasa ya cire safar hannunsa ya sauya wata take bin sa da harara a fakaice.

"Hajiya kwanta zan duba ki." Shukra ta watsa masa harara ta ce.
"Ka yi mini uwar me? An gaya maka ni ma shegiya ce da zan zauna wani ƙato ya gane tsiraicina?" Safar hannunsa Dr Hussain ya zare ba tare da ya tanka mata ba, ya saki murmushi sannan ya fice daga ɗakin. Yana fita Shukra ta bi shi da harara ta ce.

"Don Allah dube shi kamar wani mutumin arziƙi ashe ƙwallan ɗan iska ne." Fitar Dr babu jimawa wani azababban ciwo ya baƙunci Shukra, a galabaice ta fisge ɗan kwalin kanta haɗe da ribon ɗin ta yi wurgi da shi. Cikin azaba ta dafe baya tana faɗin.

"Ya hayyu ya ƙayyum, wash! Wayyo bayana zai ɓalle." Ana cikin haka sai kakar matar da suke ɗaki ɗaya da ita ta shiga, da yake gadon Shukra daga bakin ƙofa yake. Sai da ta yi wa Shukra sannu sannan ta ɗago jarkar hannunta tana faɗin.

"Halima ga tofin nan na karɓo miki maza ki ɗaga kanki ki shanye, cikin ikon Allah an ce kina sauke robar sai haihuwa." Dattijuwar na gama magana tana shirin ƙarasawa gaban gadon jikar tata, Shukra ta fisgo jarkar da sauri cikin jin zafin ciwo ta murɗe murfin ta ɗaga kai tana ɗaɗɗaka. Da sauri Dattijuwar ta warto jarkar da tuni Shukra ta kusa shan rabi, ganin haka ya sa Shukra ta fashe da kuka mararta na karta mata ta ce.
"Iya don Allah ki ban na shanye na haihu yanzu na huta." Dattijuwar ko ta kan Shukra ba ta bi ba ta miƙa wa Halimatu ta ɗaga kai ta shanye.

Nurses ne suka shigo kuma a wannan lokacin ne jaririn Halimatu ya faɗo, da sauri suka shiga hidimar gyara ta da jaririn da ta haifa. Ana cikin haka sai ga Dr Hussain ya shiga, Shukra na ganinsa ta fisgo hannunsa har sai da ya kusa faɗuwa kanta. Ta yi shame-shame a kan gado ta wara ƙafafu tana faɗin. "Don Allah zo ka duba ni Dr, ni ka cire mini jaririn ma gabaɗaya na huta." Dr Hussain ya yi murmushi ya ce.

"A'a Hajiya ai ni 'yan iska kawai nake dubawa ke da ba 'yar iska ba..." Da sauri Shukra ta katse shi.
"Wallahi Salim shi ne babban ɗan iska Malam Dr, don Allah Malam Dr ka zo ka duba ni." Shukra ta ƙarasa maganar tana fusge zanin jikinta. Dr Hussain na duba ta ya ga ta kai 5cm don haka ya ce mata ta yi haƙuri ita ma tana gab da haihuwa, ban da gyaɗa kai babu abin da take yi. Shukra tana haɗa ido da kakar Halimatu ta ce.

"Iya don Allah kada ki sake haihuwa, wallahi haihuwa mutuwa ce." Dattijuwar ta ƙumshe dariyarta ta ce.
"Yarinya ni kuwa tsofai-tsofai me zai haɗa ni da haihuwa?" Runtse ido Shukra ta yi tana jin wani zummm a ƙasan mararta, sai da ta yarfe hannu sannan ta sake cewa. "Wai Iya kin san ma me ake nufi da haihuwa? Wayyo marata!" Dattijuwar ta ce. "Yar nan ina zan san haihuwa tun da ta zo kan 'yan zamani." Ta yi maganar tana sakin murmushi sannan ta fice daga ɗakin.

Kafin wani lokaci tuni an gyara Halimatu da ɗanta har an sauya mata ɗaki, abin duniya goma da ashirin ya sake rufe Shukra ga Nurses ɗin sun ƙara duba ta sun ce ta ɗan jira da saura haihuwarta.

Uwani na gama kwatantawa Aunty asibitin ta dubi Auta ta ce.
"Auta mu leƙa mu ga halin da Aunty Shukra take ciki don..." Auta ta katse ta da sauri.
"A'a Uwani kedai ki shiga wallahi ba zan iya shiga labour room ba tsoro gare ni." Uwani ta miƙe ta nufin ɗakin da Shukra take ciki.

Tun daga bakin ƙofa ta fara jiyo ihu da salatin Shukra, da sallama ta shiga ɗakin tana shiga ta ci karo da ɗankwalin Shukra a bakin ƙofa. Gashin kanta duk a hautsine ta yi zuru-zuru, jiki a sanyaye Uwani ta ce.
"Sannu Aunty Shukra!" Don yanayinta ba ƙaramin tausayi ya ba wa Uwani ba.

"Uwani ina Salim?"
"Wai Babynki?" Uwani ta faÉ—a, takaici ya sake rufe Shukra ta ce.

"Ke da babyn na ci banten ubanku! Wallahi ki je ki ce masa idona idonsa sai dai wani ba shi ba."
Uwani duk yadda take cikin jamami sai da ta saki mutmushi, ganin haka ya harzuƙa Shukra ta ɗauki jakarta ta wurga mata. A guje Uwani ta fice tana dariya, don abin na Shukra abin tausayi abin kuma ban dariya. Tana tafe kiran wayar Jafar ya shigo mata, baki ɗauke da sallama ta ɗauka. Bayan sun sake gaisawa ya tambaye ta jikin Shukra, Uwani na shirin ba shi amsa daga bayanta ta ji alamun gudu da ihun Shukra tana faɗin.

"Wayyo Allah jama'a!" A guje Uwani ta ƙara gaba don ta ɗauka wani abin ne ya koro Shukra daga ɗakin, ganin gudun da Uwani da Shukra ke yi ya sa wasu mata masu ciki su biyu, wani magidanci, Salim sai kakar Halimatu suma suka ɗiba a guje suka yi gaba.

"Jama'a kowa ya yi ta kansa ga haihuwa nan tana bin maza da mata, wayyo Allah! Haihuwa ta kawo mini farmaki."

A wahalce Shukra ta ƙarasa reception a daidai wannan lokacin wani Alhaji na tsaye ta ƙarasa wurinsa ta cikwikwiyo rigarsa ta ce, "Dr zo ka zaro mini ɗan nan ko hannu ko ƙafarsa ka samu ka fisgo shi ko na huta." Da sauri mutumin ya kawar da kansa gefe ganin Shukar daga ita sai doguwar rigar atamfa, kai ba ɗankwali sai pant ɗin da ta ɗora a kanta a madadin ɗankwali.

"Subhanallah hajiya ni ba likita ba ne." Alhajin ya furta cikin muryar ustazai.
"Ƙarya kake ba kai ne ka duba ni ɗazu ba? Wallahi mu je sai ka haife mini cikin nan. Ko kuma ka mayar mini da naƙudar."
Chapter 51 · 0% Book details