Sashe 63
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ina fatan dai ba jikin ba ne? Ko kin fara jin wani ciwon ne?" A madadin Uwani ta ba wa Aunty amsa sai hawaye ne ya fara bin gefen fuskarta, rungumo ta Aunty ta yi tana buga bayanta. Jin Uwani na kuka ya sa Aunty ta É—ago ta furta.
"Yanzu so kike ki ɓata kwalliyar ta ki tun ba a gama taron ba?" Uwani ta girgiza kai ta ce. "Aunty ba ni key ɗinki zan wuce gida." Kallon tsaf Aunty ta yi mata ta sannan ta ce.
"Kada dai saboda kishiyarki ta zo wurin nan kike zubar da ƙwallarki a banza? Uwani wai yaushe za ki yi wayo ki bar sakarcin nan?" Shiru Uwani ta yi Aunty ta miƙa mata tissuee sannan ta ci gaba da cewa.
"Wallahi tun wani bai gani ba gara ki gyara fuskarki, salon a ga yanayin da kike ciki wani ya je ya kai mata rahoto ko? Ungo hoda maza gyara fuskarki ki wuce mu je, yanzu idan Auta ta ji kin wuce gida za ta ji daɗi ne?" Jiki a sanyaye Uwani ta karɓa ta shiga gyata fuskarta, sai dai har lokacin wani irin raɗaɗi take ci a cikin ranta. Aunty ta ci gaba da ƙarfafa mata gwiwa sai da ta saita nutsuwarta sannan suka koma cikin hall ɗin.
Can filin da amarya take zaune Uwani ta nufa, wasu ƙawayensu na makaranta suka mara mata baya. Hotuna da video sauka shiga yi da amarya, sannan aka sakar musu kiɗa. A hankali Uwani take takawa, Auta ta sunkuya saitin kunnenta ta ce. "Maman baby wallahi na haƙura da rawar nan kada ki hautsina mini yarinya." Hararar wasa Uwani ta yi mata Aunty da ke gefe ta ce.
"To sababbu a nan ɗin ma yi za ku yi?" Uwani ta saki murmushi ta ce. "Yarinyar kin ci sa'a yau ranar taki ce. Da ko hmmm." Uwani ta yi ƙwafa tana ci gaba da rawa.
Uwani ta jima tana ɗan tattakawa sannan ta koma ta zauna, tana daga kujerarta take kallon yadda 'yan mata ke girgijewa. Tana zaune ta ji Mc ya ba da sanarwar amarya ta dawo cikin fili, zai lissafo sunayen mutanen da za su fito su nuna mata ƙauna. Murmushi Uwani ta yi don ta san duk salon samun kuɗin liƙi ne, bayan Auta ta fita cikin fili Mc ya kira sunan Shukra, Aunty, Mami sai ita. Duk da ƙafarta ta gaji hakan bai hana ta yunƙurawa da ƙyar ta miƙe ba, ta zaro kuɗi daga cikin jakarta bandir ɗin ɗari bibbbiyu sai na ɗari biyar guda ɗaya. Tun kafin ta ƙarasa Mami da Aunty suka fara yi wa Auta ruwan liƙi, ta yi mamaki sosai ganin yadda Mami ke sakar mata fuska tana yi mata murmushi, duk da ba wata doguwar alaƙa da ta shiga tsakaninsu amma ta ba ta girmanta na matsayin mahaifiyar mijinta.
Uwani ta ƙarasa wurin a lokacin Aunty da Mami suka matsa gefe. Uwani ta ɓalle bandir ɗin 'yan ɗari biyar-biyar tana liƙawa. Aunty na tsaye ta hango Jafar shi da Safna sun tunkaro wurin, ita ma Safna hannunta ɗauke da bandir ɗin kuɗi. Aunty ce ta ƙarasa wurin Mc ta yi masa raɗa a kunne, tana matsawa ya saki wani sabon kiɗan yana faɗin.
"An gaida Hajiya Hauwa'u mai hadarin nairori, wai na ce duk cikin filin nan Jiddah ce ce za ta nuna mata ƙauna ne? Ki taka lafiya Hajiya Maijidda, ni na san idan an haifo ɗan baby za a gayyoto ni nazo taya murna." Uwani ta saki murmushi tana ɗan tattakawa a hankali ta yi wa Auta ɓarin kuɗi ita ma Auta ta fara yi mata.
"Allah sarki ita ma amarya ta ce ba za a barta a baya ba, kai da ganin waɗannan manyan matan ka san akwai ƙauna da zumunci mai ƙarfi a tsakaninsu. A gaskiya na yaba kuma ko gobe zan sake dawowa bikin ko sunan gidan Mai shanu" Wannan kirari da Mc yake yi ya ja hankulan mutane da dama, hakan ya sa wasu daga cikin 'yan biki suka fara matsowa cikin fili, kamar almara Jafar na kai idonsa wurin Auta karaf suka sauka a kan Uwani. Dam! Ya ji a saman kansa tamkar an kwaɗa masa guduma, Uwani jim bayanta ya gaji ya sa ta ɗago za ta bar cikin filin idanunta suka sauka a kan Jafar. Kusan mutuwar tsaye suka yi ƙirjinta ya shiga bugawa da ƙarfi, Auta ce ta lura da halin da take ciki ganin Jafar Uwani ke kallo ya sa ta saki ajiyar zuciya cikin farinciki don dama abin da take jira kenan.
Ganin Jafar ya tsaya cak ya sa Safna ta waiga tana faɗin, "Baby mu ƙarasa mana." Da mamaki take bin sa da kallo, ta juya tana kallon wurin da yake kallo. Jikin Uwani ban da karkarwa babu abin da yake yi, cikin hanzari ta bi ta cikin rurumar mutane ta fice daga cikin filin. Kai tsaye ɗakin da suka ajiye gift ta faɗa tana jin zuciyarta na wani irin harbawa.
Kamar zautacce haka Jafar ya fisge hannunsa daga riƙon da Safna ta yi masa yana faɗin.
"Jiddah! Jiddah!"
Sototo Safna ta yi da mamaki tana bin sa da kallo, ganin ya shiga cikin filin a haukace yana dube-dube da sunan da yake ambata. Cike da tsananin tausayi Auta ta bi shi da kallo har ya ƙarasa cikin filin, da yake Mc ya daɗa sakin wani kiɗan ya sa Jafar ya ja hannun Auta can gefe, jikinsa na rawa ya furta.
"Ina Jiddah take?"
Auta kamar ta yi masa bayanin Uwani sai kuma ta tuna alƙawarin da suka yi mata.
"Ban san inda ta yi ba, amma da tana cikin wurin nan Ya Jafar?"
"Amma kin san ta zo wurin nan shi ne ba ki sanar da ni ba?" Jafar ya tambaye ta a zafafe.
"Zuwanta kenan Ya Jafar..."
"Rufe mini ba ki." Jafar ya katse ta a hargitse yana ci gaba da dube-dube a haukace. Da Ido Auta ta bi shi da kallon tausayi, ganin ba shi da niyyar dawowa wurinta ya sa ta koma kujerar da aka tanada domin ta ta zauna a sanyaye.
Da yake securites ɗin da ke gadin ɗakin da aka ajiye gift sun gane Uwani ya sa ba su dakatar da ita ba, don kusan ita ta bada umarnin duk yadda za a ajiye kayan ba tare da an hargitsa wasu ba. Uwani na shiga ɗakin ta turo ƙofa ta jingina a jikin ƙofar hawaye na bin fuskarta. Kuka take sosai saboda yadda zuciyarta ke yi mata, duk yadda ta so dakatar da zubar hawayenta abin ya ci tura. Sai da ta ci kuka mai isarta sannan ta warware ɗaurin ɗankwalin da aka yi mata, ta yafa mayafinta. Har za ta fita ta ɗauko waya ta kira Aunty, sai da ta katse har sau biyu sannan Aunty ta ɗauka. Sanar da ita wurin da take ta yi, babu jimawa Aunty ta ƙarasa.
Ganin yanayin Uwani ya sanyaya mata jiki, don tun barin Uwani daga wurin ta lura da halin da Jafar yake ciki wanda hakan ne ya sa ta fahimci ya yi tozali da Uwani.
"Aunty ki ba ni mukullin sashenki zan wuce gida." Uwani ta furta murya a dashe.
"Ba zan bari ki tafi ke kaɗai ba, ki bari zan je na damƙa wa Shukra komai tun da dama an kusa tashi sai na dawo mu wuce gida.
"Aunty ba na son Ya Jafar ya sake ganina ne." Da kallon tausayi ta bi Uwani ta ce.
"Uwani mijinki yana sonki yana ƙaunarki, da za ki ga irin abin da yake yi a wurin can sai kin matuƙar tausaya masa. Ko kaɗan kada ki ƙullace shi ko ki ga laifinsa, abin da nake so da ke ki ci gaba da addu'a." Wasu zafafan hawaye suka sake zubo mata musamman da ta tuna yadda Jafar ya sako Safna a gaba suna tafe suna sakin murmushi.
"Haba Aunty ta yaya za ki ce Ya Jafar na sona bayan ya samu wata ya manta da ni?" Uwani ta raya a ranka. Kamar Aunty ta san abin da yake cikin zuciyar Uwani ta furta. "Don Jafar ya auri wata matar ba shi yake nuni da cewar ya daina sonki ba, kamar yadda kike matarsa haka ita ma Safna matarsa ce. Ki ci gaba da addu'a Allah ya zaɓa abin da ya fi zama alheri." Wani abu mai nauyi ya sake danne zuciyar Uwani, ta amsawa Aunty sannan ta fice daga ɗakin.
Haka Jafar ya gama karaɗe cikin hall ɗin da neman Uwani amma bai ganta ba, hakan ne ya sa ya nufi wurin da Dada ke zaune ita da ƙawayenta tsofaffi cikin wani irin yanayi ya ce mata.
"Dada ina Jidda take?" Da mamaki Dada ta dube shi ta É—an yamutsa fuska ta ce.
"Wata ce kuma haka?" Jafar ya haÉ—e fuska ya ce.
"Matata nake nufi tana ina?" Baki sake Dada ta ce.
"To yaushe kuma matar so ta zama Jidda, wa take da suna Safya ko Safiya?"
"Uwani nake tambaya wallahi ganin idona na ganta a wurin nan." Sai a lokacin Dada ta gane wacce yake nufi, ta yamutsa fuska ta ce.
"Wani sabon munafurcin ka ƙullo Jafaru da ka sauya wa Uwani suna zuwa Jidda? Yo to don ka ganta sai me? Saboda kai za ta ƙi zuwa bikin 'yar uwarta ne?" Takaici ya sake mamaye Jafar ganin idanun mutane ya fara dawowa kansa, a lokacin Safna ta ƙarasa wurin cike da damuwa ta ce.
"Baby lafiya wai me kake yi haka? Wace ce Jidda da kake neman tuburewa a kanta?" Jafar ya saki tsaki ya bar Safna da ke tsaye sororo, Dada ta riƙe haɓa jin sunan da Safna ta kira Jafar da shi.
"Kai idan kana duniya za ka ga lalata iri-iri, ban da ɗaurewa iskanci wai Jafaru ake cewa Baby. Garsamemen ƙaton da zai iya zubar da maza biyar, Allah ya sawaƙewa lalacewar zamani." Safna ta gama kai wa wuya, don haka ta wuce fuuu ta bar wurin ba tare da ta tanka wa Dada ba.