Sashe 65
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
Mutsu-mutsu Uwani fara yi tana kiciniyar ƙwacewa ta sunkuyar da kanta a ƙasa, saboda kallon Jafar da ta yi na ɗan sakanni ne ya nemi tarwatsa ƙwarin gwiwarta. Sake janyo ta ya yi jikinsa ya yi ya sa hannu ya ɗago fuskarta suna fuskantar juna, wani abu Uwani take ji na ratsa ta tun daga tafin ƙafarta har tsakiyar kanta. Cikin wata irin murya Jafar ya furta.
"Mene ne laifina da kike azabtar da gangar jiki da ruhina? A kullum kuma a kodayaushe na zama tamkar mahaukacin da ke turi, har ta kai mutane na yi mini kallon zautacce ko mai wata lalurar a kanki. Me ya sa kike nisanta kanki daga gare ni alhalin kin san ba zan iya jure rashinki ba, shin kin san adadin kwanakin da na yi ina bulayin nemanki? Kin san darare nawa na shafe ina mafarkin haÉ—uwa da ke? Kin san mutane nawa na dinga zuwa wurinsu ina cigiyar neman inda kika shiga?" Hawaye ne ya ciko idanun Uwani suka fara gangarowa ba tare da bin umarninta ba, Jafar ya sa hannu ya goge mata sannan ya kai hannunsa saman turtsetsen cikinta yana jin wani irin farinciki na ratsa shi.
"Shin kema kin amince a raba mu kenan Jidda?" Kukan da Uwani ke riƙewa ne ya kwace mata, jin shasshekar kukanta ya sa Jafar ya rungumo ta a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya.
"Ina sonki ina matuƙar ƙaunarki, na yi kewar wannan bakin tsiwar taki. Na yi kewar komai na ki, a kullin ƙaunarki ke nashe mini zuciya. Ko ba za ki amsa mini ba don Allah ki furta mini kalma guda da za ta sanyaya mini rai, ko zan samu sauƙin dafin da ke kwance a zuciyata Jidda."
Aunty da tun fitowar Uwani ta biyo bayanta don ta yi tsammanin Uwani tafiya za ta yi, ta goge ƙwallar da ta taru a idonta. Don Jafar da Uwani ba ƙaramin tausayi suka ba ta ba. Jafar ya haɗa hannuwansa biyu alamar roƙo sannan ya cigaba da cewa.
"Don Allah Jidda ki taimaki zuciyata da ke barazar tarwatsewa."
Uwani ta goge ƙwallar fuskarta ƙirjinta na bugawa, cikin tsantsar soyayya da kewar mijinta wani ta furta.
"Ina ƙaunarka Nur domin soyayyarka a cikin jinin jiki da ruhina take yawo." Uwani na gama maganar ta bi ta gefensa za ta gegare shi ta wuce. Safna da ke tsaye tun farkon fitowar Jafar ta fisgo Uwani da ƙarfin tsiya cikin tsananin kishi ta ɗauke ta da mari haɗe da hankaɗa ta da iya ƙarfinta. Bi sa tsautsayi Uwani ta bugu da jikin gate ɗin Hall ɗin ta faɗi a ƙasa, wata irin azaba ta ji a cikinta har zuwa mararta don haka ta ƙwalla wata irin gigitacciyar ƙara.
A haukace Jafar ya shaƙo Safna ya wanke ta da zafafan mari, idanunsa a rufe saboda ɓacin rai ya rufe ta da wani mahaukacin duka. Aunty da ƙawarsu Uwani Na'ima da ƙarasowarta kenan suka yi kan Uwani suna salati.
"Wayyo cikina! Innalillahi wa inna'illahir raji'un! Wayyo marata." Uwani ta furta cikin tsananin azaba. Wasu Police da ke jikin gate ɗin hall ɗin a tsaye ne suka ƙwace Safna daga hannun Jafar ganin yana neman illatata, a haukace ya yo kan Uwani yana kiran sunanta. Ganin halin da take ciki ya sa Jafar ya kinkime ta ya saka ta a motarsa. Kafin wani lokaci tuni 'yan biki sun fito waje carko-carko jin labarin abin da ya faru, Aunty da Shukra ne suka shiga bayan motar da Uwani ke kwance cikin galabaita. Jafar gudu yake kamar zai tashi sama a haka suka ƙarasa wani private hospital da ke titin state road. Da zuwansu babu jimawa aka shiga da Uwani domin ba ta agajin gaggawa, Dr Sadik ne ya fito yana sharce gumi Jafar na ganinsa ya ƙarasa wurinsa.
"Ya ake ciki Dr? Zan iya shiga na ganta?" Girgiza masa kai Dr Sadik ya yi ya ce.
"Yanzu haka za ka yi signing ne saboda dole sai dai mu yi mata aiki mu ciro abin da yake cikinta." Aunty da Shukra jin haka ya sa jikinsu ya sake sanyi, Aunty ban da kuka babu abin da take yi.
"Dr zan yi indai za ta samu lafiya a ciro babyn. Don Allah ka taimaka mini wallahi ina ƙaunar Jidda!" Jafar ya faɗa cikin tashin hankali.
"Ka kwantar da hankalinka In Shaa Allahu za mu yi mata aikin cikin nasara, fatan dai ku yi mata addu'a ba kuka ba kamar yadda na ga sisters ɗinta suna yi." Wayar Aunty ce ta fara ƙara sai da ta share hawayenta sannan ta ɗauka.
"Zainabu a wanne asibitin kuke?" Daddy ya furta daga can ɓangaren, da yake a ruɗe take sai da ta tambayi wata nurse sannan ta yi masa kwatancan asibitin.
Jafar na gama signing aka shiga da Uwani É—akin tiyata, Jafar ban da kaiwa da kawowa babu abin da yake yi. Mami ce ta kira shi a waya ta tambaye shi asibitin da suke, Jafar ya kwatanta mata ta ce masa gata nan zuwa.
Bayan wani lokaci Dr Husna ta leƙo fuska ɗauke da fara'a, suna ganinta gabaɗaya suka yi wurinta suna jera mata tambaya.
"AlhamduLillah! Mun samu nasarar yi mata aiki, kuma ita da baby suna cikin ƙoshin lafiya." A take Jafar ya tsugunna ya yi sujjada, a daidai wannan lokacin Daddy ya ƙarasa hankali a tashe. Yana zuwa ya samu kyakkyawan labari, cikin farin ciki ya shiga ɗaga hannu yana godiya ga Ubangiji. Mami ce ta yi sallama jiki a sanyaye kamar kazar da ta taka wuƙa, ko kallon kirki Aunty ba ta yi mata ba. Jafar ta tambaya jikin Uwani nan yake sanar da ita haihuwar Uwani. Sai dai likitoci sun tabbatar musu sai an gama gyara ta da jaririn za a kai su ɗakin da kowa zai iya shiga ya gansu. Jafar saboda farin ciki ya kasa zaune ya kasa tsaye ji yake kamar ya yi tsuntsuwa ya faɗa ɗakin, yana nan tsaye ya ciro wayarsa. Misscall ɗin Auta ya gani rututu yana shirin kiranta ya ji Aunty na waya da ita.
"AlhamduLillah an yi mata aiki ita da babyn suna cikin ƙoshin lafiya, eh sun ce namiji ta haifa." Ihu Auta ta saki ta ce gata nan zuwa, don dama tun bayan abin da ya faru da Uwani babu jimawa aka tashi daga dinner.
"Am yanzu za ku iya shiga ku ganta kafin mu yi mata allurar bacci, but please ba ta buƙatar hayaniya da yawa. And ba ma buƙatar a daɗe saboda tana buƙatar hutu." Dr Sadik ya furta yana nuna musu wani ɗaki da ke kallo su, Jafar bai tsaya jin ta bakinsa ba ya nufi ɗakin cikin sauri.
A kwance ya same ta da jaririnta a gefenta, wani irin farin ciki ke ratsa shi ya ƙarasa bakin gadon ya sumbaci goshinta.
"Yanzu wannan ɗana ne Nue?" Jafar ya furta da wani irin yanayi, murmushi Uwani ta sakar masa, ya riƙo hannunta ya sumbuta yana jera mata sannu. Jaririn ya ɗauka ya rungume shi tsam yana jin soyayyarsa a cikin ransa, tabbas ko makaho ya shafa fuskar jaririn sai ya tabbatar da matsananciyar kamar da suke yi. A haka su Daddy suka ƙarasa ɗakin, suka karɓi jaririn suna yi wa Uwani sannu. Wani irin nauyinsu take ji don haka ta gagara haɗa ido da su, jaririn sai tsotsar hannu yake. Daddy ya ƙura masa ido yana sake jaddada godiyarsa da Ubangiji ya nuna wa Mami ranar da Uwani ta sauke cikin Jafar.
"Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai ya yi, tabbas duk abin da ka ga Ubangiji ya ƙaddara ya fi mu sanin alkairinsa a gaba. Yau dai ga jinin Jafar ya fito ta jikin Uwani kai Allah mun gode maka." Aunty ta yi maganar cikin farin ciki. Jikin Mami ba ƙaramin sanyi ya yi ba, wata irin kunya ta kamata. A kunyace ta ƙarasa ta ƙarɓi jaririn tana jin soyayyarsa a ranta, ta ƙura masa ido ta kallon zallar kamar da su da Jafar. Ba su jima ba suka fita suka bar Jafar a ɗakin kowanne zuciyarsa fal da farin ciki, a kujera Jafar ya zauna a matsa kusa da Uwani ya riƙo hannunta yana jin ƙaunarta a zuciyarsa.
"Ya Jafar me na yi wa matarka da take yunƙurin hallaka rayuwata da ta abin cikina?" Uwani ta furta a hankali.
"Shiiiii ba na son jin komai yanzu, kin ga jikinki babu ƙwari ko kina son ki sa wa kanki damuwa?" Jafar ya yi maganar kamar da ƙaramar yarinya yake, Uwani ta girgiza kai sannan ya ce.
"Na yi waya da wani yarona Sargent Musa yanzu haka tana can a hannunsu, ki kwantar da hankali kin ji Jiddona." Gyaɗa masa kai Uwani ta yi yana nan zaune wasu Nurse suka shiga, suka buƙaci da ya fita za su yi mata allurar bacci.
"In dai nine ba ku da damuwa zan zauna na kula da baby." Jafar ya furta yana sake rungume jaririn, murmushi ɗayar ta yi ganin yadda yake ƙara riƙe babyn gam kamar wani zai ƙwace masa shi. Yana nan zaune aka saka wa Uwani allurar a cikin drip tun Nurse ɗin na cikin ɗakin wani bacci mai daɗi ya yi awon gaba da ita.
Su Mami suna zaune a reception kiran Hajiyan Safna ya shigo wayarta, gabanta ne ya faɗi jiki na rawa ta ɗauki wayar ta matsa can nesa daga cikinsu Aunty ta nufi ƙofar fita.
"Hello Hajiya..."
"Dakata! Babu wani abu da za ki faɗa mini, azzaluma macuciya. Ashe dama munafurtata kike Saratu ban sani ba sai yau da Allah ya tona asirinki? Wallahi kin ba ni mamaki. Ashe mu kika mayar 'yan iska da ba ki taɓa sanar mana Jafar yana da mata ba shekara da shekaru, to ga ɗanki nan ki kwaɗa shi ki cinye wallahi ko shi ne autan maza Safna ta haƙura da shi. Munafukar banza kwaɗayayya..." A zafafe Mami ta katse Hajiyan Safna don kalamanta ba ƙaramin ɓata mata rai suka yi ba.