← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 71

Sashe 55

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yaya Jafar ni ce." Guntun tsaki ya saki ya zura doguwar rigarsa sannan ya buɗe ƙofar sai dai bai ba wa Autar dama shiga ba saboda yanayin shigar da ke jikin Uwani.

"Mami ce take kiranka Ya Jafar." Amsa mata ya yi sannan ta wuce, tura ƙofar Jafar ya yi ya koma wurin Uwani ya zauna a kan doguwar kujerar da take kwance.

"Jikin naki da sauƙi ko?" Da yake Uwani ta ji maganar da suka yi da Auta ya sa ta ɗan langwaɓe ta ce. "Wallahi har yanzu da zafi, ga kaina ciwo yake." Kanta ta ɗora a cinyarsa, Jafar ya shafa ɗakalallan saman cikin Uwani a ransa ya raya wani tunani. Murmushi ya saki Uwani na shirin magana suka ji shigowar Mami kamar daga sama, da yake Uwani ta tsorata maƙale Jafar ta yi ta saki ƙara da ƙarfi. Ya rungume ta tsam a jikinsa don shi kansa ba ƙaramin tsorata ya yi da bugun ƙofa haɗe da shigowar Mami ba.

Turus Mami ta yi tana bin Uwani da wulaƙantaccan kallo, ganin figigiyar rigar da ke jikinta ko cinya ba ta rufe mata ba. Ta saki dogon tsaki ganin irin ruƙon da Jafar ya yi mata.

"To bita zaizai sai ka taso mu je, wato sabida ka saka mace a gabanka na aiko kiranka ka share ko?" Sai a lokacin Jafar ya iya motsawa, ya miƙe da sauri ya ɗan tsaya ta gaban Uwani don ya kare ta. Sam bai ji daɗin abin da Mami ta yi ba, murya a maƙoshi ya ce. "Dama yanzu zan fito Mami."

"To wuce mu je." Mami ta furta tana nuna masa hanya. Jafar har ya yi gaba Uwani ta tashi zauna tana faÉ—in, "Wash Allahna, wallahi Ya Jafar da ciwo." Waigowa ya yi da sauri ya ce.
"Bari na dawo sai na karɓo miki magani."

Ganin irin rawar jikin da Jafar yake yi da Uwani ya sa Mami ta fahimci mai afkuwa ta gama afkuwa tsakaninsa da Uwani. Saboda haka koda suka fita ta rufe shi da faÉ—an babu gaira babu dalili.

"Ka buɗe kunnenka da kyau ka saurare ni, ba za ka mayar da ni ƙaramar mutum ba. Ina aka kwana a magaar sa ranar aurenku da Safna?" Jafar ya ɗan sosa kai, don sai a lokacin ya tuna rabonsa da waya da ita tun daren jiya.
"Maganar tana nan Mami..."

"To a yau ka je ka samu mahaifinka ka sanar da shi kana son ya kira mahaifin Safna domin su je a tsayar muku da lokacin aure, wallahi-wallahi Jafar idan ba ka same shi a yau ba sai ranka ya yi mummunan ɓaci. Sakare ina ganin ka mai hankali ashe na banza ne, har za ka zauna yarinya ƙarama tana wasa da hankalinka. Me aka yi, aka yi Uwani? Wacce tsiyar za ka tsinta a jikinta? Tun wuri ka fita daga idona na rufe, idan ba haka ba sai na ɓata maka rai." Jafar shiru ya yi yana jin kalaman mahaifiyarsa na saukar masa tamkar maɗaci, sai da ta yi ta gama sannan ta sallami Jafar ya koma sashensa.

Ganin yadda Jafar ya koma a sanyaye ya sa Uwani ta sha jinin jikinta, a wannan karon zuciyarta ta kai wuya da abin da Mami ta yi mata. Sai da ya zauna sannan ta zauna a kusa da shi, idanunta cike da hawaye.

"Tun da ƙuruciyata kafin hankali ya ratsa ni na gama tantance so da ƙiyayya na fara fuskantar tsana daga wurin mahaifiyarka, ba tun yau ba na san mahaifiyarka ba ta sona kuma ba ta ƙauna ba. Ya Jafar!" Uwani ta kira shi da wata irin murya, kallonta ya yi ta ci gaba da cewa.

"Idan har zamantakewa ta da kai ba za ta haifar da samun ɗa mai ido a tsakaninka da mahaifiyarka ba don girma Allah ka sawaƙe mini. Na sani ka sani a lokacin da aka aurar da mu babu mai son ɗaya daga cikinmu, ni da kai auren haɗi ne. Mahaifiyarka ba ni take muradi ta kasance abokiyar rayuwarka ba, ina ganin zai fi dacewa ka ba ni takarda ta, ka auro Safna idan ya so ni ma zan samu wanda zai so ni kuma mahaifiyarsa ta ƙau..." A hargitse Jafar ya buga mata wata mahaukaciyar tsawar da ta sa ta katse kalaman bakinta.
"Kina hauka ne? Ni kike faÉ—a wa ki je ki auri wani namijin? Na faÉ—a miki zan iya rayuwa babu ke?" Jin haka ya sa Uwani ta rushe da matsanancin kuka, jikinsa ne ya yi sanyi don haka ya janyota jikinsa don ya san duk kalaman da ta faÉ—a a kan mahaifiyarsa daidai suke. Amma ta yi wa zuciyarsa adalci idan har ta ce ya rabu da ita?

"Duk maganar da za ki faɗa mini ki faɗa amma kada ki sake faɗa mini kalmar rabuwa." Uwani ta ɗago cikin hawaye ta ce. "Amma me ya sa Mami ba ta ƙaunata? Me ya sa duk kyautatawar da zan yi mata ba ta yi mini kallon soyayya sai na tsantsar ƙiyayya? Me ya sa..."

"Saboda a faɗin duniya ba kowa ne Allah Ya ƙaddara zai so ka ba, daga ni har ke haka abin yake a gare mu. Don Allah kada ki damu da wannan, halin Mami ba baƙo ba ne a wurinki don haka kada ki ƙara wa kanki ciwon kai." Jafar ya jima yana lallashin Uwani har sai da ya ga ta huce sannan suka ci gaba da hira, a ɓangare ɗaya yana ayyana hanyar da zai bi domin ya sanar da Safna alaƙar da ke tsakaninsa da Uwani. Don a yadda yake jin ta a ransa ba zai iya rabuwa da ita ba, ita ma kuma Safna wata sashe ce a cikin zuciyarsa. Laifin Mami yake gani ƙarara, don da ta bi ta shawarasa da ya ce a sanar da Safna da hakan duk ba ta faru ba.

Uwani sai da ta kwana biyu cir ba ta leƙa sashen Aunty ba saboda rashin ƙwarin jiki da irin kulawar da yake ba ta, don gabaɗaya wata irin kunyar Aunty take ji.
"'Yata ai tun jiya muke kewarki ni da Auta, na ce Jafar dai ya ɓoye mini ɗiya." Uwani ta sunne kai a kunyace, sai da Auta ta fita daga ɗakin sannan Aunty ta ce. "Ina fatan dai duk huɗubar da na yi miki ba ta tashi a banza ba?" Uwani ta gyaɗa kai tana murmushi.
"Ai na ga alama ga shi kwana biyu amarci ya karɓe ki har wani fresh kika yi." Aunty ta faɗa cikin sigar zoyala.
"Kai Aunty wallahi kina ba ni kunya." Uwani ta furta. Hira suka sha daga baya Auta ta dawo tana tsokanar Uwani, magriba na ƙaratowa Aunty ta kora Uwani sashenta.

Sannu a hankali wata irin shaƙuwa da soyayya mai ƙarfi ta ƙara shiga tsakanin Uwani da Jafar, a yanzu kam sosai Uwani take zagewa tana faranta ran mijinta, wani lokacin har tsokanarta yake ya ce kamar ba ita ke jin kunyarsa a baya ba.
Jafar ya samu Daddy da maganar auren Safna, a nan Daddy yake ce masa ya bari a ƙarasa yin fulastar gidansa idan aka yi fenti sai a tsayar da lokacin aure, don ba ya son daga baya a ɗaga saboda sha'nin gini da kashe kuɗi. Lokacin da Jafar ya ga tsarin ginin da Daddy ya yi masa ya ji daɗi sosai, sai dai a ranar da su Mami suka je suka gano gidan kwana ta yi tana yi wa Daddy sababi. Wata irin tsanar Uwani ta sake mamaye ta don gani take ba ƙaramin tozarci ta ja Daddy ya yi mata ba, a ce wai kamar Safna ce za a haɗa ta zama da kishiya. Babban tashin hankalinta ma bai wuce ta wacce hanyar za ta sanar da Hajiyan Safna ba, ga shi Daddy ya ce Uwani ce za ta fara tare wa a gidan kafin a ɗaura aurensa da Safna.

Watan Jafar guda da dawowa Uwani ta fara wani irin ciwon kai da zazzaɓi, kasala yawan bacci da tashin zuciya. Hatta abinci idan ta girka shi ba ta iya ci, don haka kusan koyaushe tana can sashen Aunty. Da yake ita ma cikinta ya tsufa sosai Auta ce take hidima da su, a hankali Aunty ta fara fuskantar kamar ciki ne da Uwani amma sai ta bar abin a ranta. Ita kuwa dama Auta tuni ta ranfo jirgin Uwani hakan kuma ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, sai ta yi kamar ta sanar da Mami sai kuma ta fasa don ta san ba za su wanye lafiya a kan maganar ba. Watan Jafar biyu cif da dawowa aka tsayar da ranar aurensa da Safna sati huɗu masu zuwa, kuma a ranar ne Allah Ya sauki Aunty lafiya ta haifo jaririnta ƙato kyakkyawa. Cike da zumuɗi Shukra ta zo gidan a lokacin 'yarta ta yi wayo sosai, Mami gabaɗaya ta tarkata su a gefe don ta ce asirin da Aunty take yi musu ita da Madina ne kaɗai bai kama ba. Kasancewar jinkirin haihuwar da Aunty ta yi ya sa lokaci ɗaya dangi, 'yan uwa da abokan arziƙi aka shiga turuwar zuwa yi mata barka. Uwani ita da Auta kuwa tamkar su haɗiye jaririn.

Tun ana saura kwana biyu su Daddy za su je saka ranar aurensa d Safna yake cikin fargaba, damuwarsa ɗaya yadda Uwani za ta karɓi Safna da ita kanta yadda Safna za ta karɓe ta. Dawowarta daga sashen Aunty ta same shi ya yi shiru yana nazari, dama ta fahimci yana cikin damuwa a 'yan kwanakin nan.

"Me yake damunka Nur?"
"Zauna mu yi magana" Zama ta yi a sanyaye don ta san wata muhimmiyar maganar zai yi mata.

"Ɗazu su Daddy sun je an tsayar da ranar aurena da Safna nan da sati huɗu masu zuwa, kuma an kai har da kayan lefe. Ke ma zan tura miki kuɗin da za ki sayi duk abin da kike buƙata, na san Mami ba za ta yarda ta haɗa miki ba shi ya sa ban ba ta ba." Dam ƙirjin Uwani ya buga, wani irin yammmm ta fara ji a saman kanta. Ƙirjinta na bugawa ta fara maimaita sunayen Allah a cikin ranta.
Chapter 55 · 0% Book details