← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 71

Sashe 12

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ja'irin yaro wannan doron da ya yi yana yin aure zai miƙe, na san yau kwanan farinciki zai yi yoo aure wasa ne." Dada ta bushe da dariya.

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA BAKWAI

Kamar Jafar zai tashi sama haka ya nufi sashen mahaifiyarsa saboda ɓacin rai ko gabansa ba ya gani sosai, da ƙarfi ya doka ƙofar falon Mami da su Shukra na zaune. A zabure duka suka miƙe Mami ta dube shi ta ce.

"Hankalinka ɗaya kuwa Jafar? Saurin me kake yi haka?" Jafar bai tanka mata ba ya wuce kan kujera ya zauna yana furzar da iska mai zafi. Sai da ta ƙare masa kallo sannan ta ƙarasa kusa da shi ta furta.

"A kullin ina gaya maka ka dinga rage wannan baƙar zuciyar taka. Me aka yi maka?"

"Mami me ya sa Daddy ba ya son farin cikina ne?" Shi ma ya jefa mata tambaya.
"Me ya sa ka faÉ—i haka?"
"Yanzu Mami da girmana ni ba ƙaramin yaro ba a ce za a wani nemar mini matar aure, saboda Allah an yi mini adalci kenan? Atleast ko shawarata ai sai a nema." Nan take Mami ta haɗe fuska sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta.
"Ina tunanin dai wasa yake yi maka, amma kuma ban da abin ka Jafar ka sani ko 'yar manya ce ita ma. Duk da dai na san kun gama daidaitawa da Safna ai ita ma wannan sai mu ji waye ubanta."

Tun da Mami ta fara magana wani ƙululun baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi, "Mami ko 'yar gidan uban waye ni fa idan ba na sonta ba zan aure ta ba. Kuma Daddy ya rasa wa zai haɗa ni da ita sai waccen kucaka, sakarya kuma ƙazamar yarinyar can Uwani."
A zabure Mami ta miƙe tsaye har ba ta san lokacin da wani ashar ya suɓuce mata ba. "Uban waye zai haɗa ka da wata Uwani? Yarinyar da ko a mai aiki ba zan ɗauke ta ba. Ba zai taɓa yuwu ba wallahi, wannan ma ai shiga haƙƙi ne ina kai ina wata jakar yarinya Uwani." Jin haka ya ƙarfafa gwiwar Jafar nan ya kwashe duk yadda aka yi ya sanar mata, tun ba ta gama jin jawabinsa ba ta dakatar da shi tare da faɗin.

"Bari na je na samu Dada wallahi ba zai taɓa yuwu ba wankan kuturu da sabulu." Fuuuu Mami ta wuce su Shukra na daskare mamaki ya mamaye su.

"Waye haka mai ƙirar samudawa ya yi mini gandandan a tsaye?" Dada ta furta tana ƙare wa Mami kallo da ta yi tsaye a bakin ƙofa. Mami ba ta amsa ba ta wuce ta zauna a kan hannun kujerar Dada, tana cika tana batsewa.

"Sannu da gida Dada."
Mami ta furta a daƙile. Dada ta bi ta da kallo sai da ta taɓe baki sannan ta ce.
"Sannunmu dai."

"Dada a gaskiya ba a yi mini adalci ba, saboda Allah wai a rasa da wa za a haÉ—a Jafar sai da wata Uwani. Yaron nan fa namiji ne ko mace ba za a yi wa dole ba, gaskiya a duba lamarin nan don ko kaÉ—an ba su dace ba. Wai Jafar ne da Uwani yarinyar da ko wanka ba ta yi, ga rashin nutsuwa yarinya kamar rainon gwaro, ko tashin gidan mahaukata."
Mami ta yi maganar tana haki. Baki sake Dada ta bi Mami da kallo har ta gama jawabi sannan ta ce.

"Uwata kin gama magana ko da saura? Ke Saro amma dai ba ki da kunya kuma ko kaɗan ba ki da mutumci, yanzu ni kike gaya wa haka?Maganar auren yaran nan tamkar yau kika san da ita? Ina ce tun ranar da Uwani ta zo duniya aka ajiye ta. Ki saurare ni da kunnen basira, wallahi ko mutuwa na yi ban amince su Mamman su aura wa Uwani wani mijin ba Jafaru ba. Ke har kya yi zancen ƙazanta Saratu? Kin manta lokacin da kike fama da tsamin kai da na hammata? Ko kin manta lokacin da Mamman yake tasa ki zuwa banɗaki da soso ya tilasta miki ki yi wanka?"
Mami ranta ya yi ƙololuwar ɓaci, a fusace ta ce.
"Koma dai mene ne ni na ɗauki cikin Jafar na haife abina, don haka babu wata ƙatuwa da ta isa ta yi mini iko da shi wallahi duk ƙarfin ikonta..." Cikin sauri Dada ta katse ta.

"Iyeee rashin kunya za ki yi mini Saro? To ni kuma ni na haifi Mamman kuma zan nuna miki ƙaryar gadarar da kike yi. Wallahi idan har ni na ɗauki cikin Mamman wata tara na haife shi sai an ɗaura auren Jafar da Uwani a yau, idan kin isa ki sa Jafar ya warware shi a yau ɗin nan kema." Dada ta ƙarasa maganar cikin ɓacin rai. Mami ta miƙe tsaye jikinta har rawa yake saboda ɓacin rai ta ce.

"Ke kin haifa kuma kin isa ki yi gadara da ɗanki to wallahi ni ma zan nuna miki Jafar ba rainonsa na yi ba, naƙudar abina ni ma na yi na haifa don haka mu zuba mu gani." Daga haka Mami da buga wa Dada cinya haɗe da tsaki ta fice daga ɗakin.

Daidai lokacin da Mami za ta fita Uwani ta kawo kai, duk da Uwani ba wani shiga sabgar Mami take ba amma ganin ta ya sa ta ce.
"Ina wuni Mami."
Ko ƙurar da ta ajiye Uwani Mami ba ta kalla ba ta wuce sashenta, Uwani ta taɓe baki ta faɗa ɗakin Dada. Tana shirin yin magana Dada ta katse ta.

"Ke Kulu maza je ki kira mini Mamman shi da 'yan uwansa."
Jin yadda Dada ta kira sunanta da Kulu ya sa ta sha jinin jikinta don ta lura ran Dada ya ɓaci sosai. Kai tsaye Uwani ta wuce sashen su Mami da sallama ta shiga ɗakin sai dai gaba ɗayansu babu wanda ya tanka mata, sai ma wani kallon tsana da suke bin ta da shi.

"Dada ta ce Baba Mamman ya zo."

"Sai ki neme shi a É—akin uwarki."
Mami ta furta.

"Uwata fa? Me na yi miki za ki zage ni?"
"To ko za ki rama ne? Mami ta katse ta.

"Ba zan rama ba amma wallahi kada ki sake zagina ban yi miki komai ba, don uwa ba ta fi uwa ba..."
Kafin ta rufe baki Shukra ta sauke mata tagwayen mari biyu a fuska.
"Rashin kunya za ki yi wa Mami don ubanki, shegiya ƙazama baƙa mai baƙar aniya." Uwani riƙe da kumatu ta ce.

"Kan uba marina kika yi?" Uwani na cikin magana Shukra ta sake sauke mata wani marin a fuska. Jin zafin marin ya sa Uwani ta yi tsalle sai ji kake tass a fuskar Shukra Uwani ta rama.

Cikin ɓacin rai Mami ta fisgo Uwani da ƙarfi, ita kuma Shukra ta yi mutuwar tsaye tana mamakin marin da Uwani ta yi mata.
Kamar haɗin baki Mami da Shukra suka rufe Uwani da duka tun tana ihu tana kuka har ta ja bakinta ta yi shiru saboda galabaita, sai da suka gaji don kansu sannan Mami ta koma kujera tana haki. Shukra na kan Uwani Daddy ya shigo cikin gidan, ganin irin dukan da take yi wa Uwani ya sa Daddy ya ɗauke Shukra da mari. Da kansa ya ɗago Uwani lokaci ɗaya fuskarta har ta sauya saboda kukan da ta ci. Ya lallashe ta sosai sannan Uwani ta faɗa masa saƙon Dada, a haka ta fara dafa bango ta wuce wurin Dada. Shi ma Dadday bai tsaya bi ta kan su Mami ba ya rufa wa Uwani baya.

Ganin a yanayin da Uwani ta koma ya sake ɓata ran Dada, nan take ta sa Baba Mammam ya kira mata sauran 'yan uwansa. Suna zama ta wassafa musu duk abin da ya shiga tsakaninta da Mami, ta kuma nuna musu Uwani da irin dukan da suka yi mata. Daga ƙarshe ta ɗora da jawabin ɗaurin auren su Uwani a ranar, duk yadda suka so shawo kan Dada a kan a bari zuwa nan da watan Maulidin ma fir ta ƙi yarda. Sai ma ta nuna musu ana idar da sallar Isha'i su tabbata da sun ɗaura wa Uwani da Jafar aure. Dada ta dubi Baba Mamman ta ce.

"Kai Mamman tun da ka zama sakarai sai ka bari Jafaru ya saki Uwani tun da uwarsa ta yi rantsuwa ba zai aure ta ba, to ka sani matuƙar Jafaru ya saki Uwani wallahi sai dai ka nemi wata uwar ba ni ba. Kuma a take kai ma ka miƙa wa Saratu takardarta ta saki. Na gama magana ku tashi ku ba ni wuri." Babu wanda ya iya tankawa haka suka fice ɗaya bayan ɗaya kowa zuciya babu daɗi.

Uwani tun da ta kwanta zazzaɓi mai zafi ya rufe ta har sai da Dada ta ba ta magani ta sha, don haka da dare ko fita wasan dare ba ta yi ba. A ɓangaren Jafar ma tun da ya tashi daga falon Mami ya biya wasu almajirai suka gyara masa ɗaki, tun da ya shiga ɗakinsa sallah ce kaɗai take fito da shi. Daddy kuwa ko da ya fito daga sashen Dada sun jima suna tattaunawa da 'yan uwansa sannan kowa ya kama gabansa.
Chapter 12 · 0% Book details