← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 71

Sashe 8

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baba ni fa gani nake wannan abin da aka yi musu kawai tsoratarwa ne wani ke yi musu, idan aljanun gasken ne ai da tuni sun É—auki mataki. Kada a yi wasa da hankulan mutane a dai duba lamarin." Jafar ya yi maganar yana zuba wa Uwani kallon tuhuma, don yadda ya ga tana sakin murmushi ya ji sam bai yarda da ita ba.

"Koma dai mene ne ai babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji Jafaru. Allah Ya yi mana maganin wannan masifa." Baba Mustafa ya faɗa, gabaɗaya suka amsa da Amin. Uwani na haɗa ido da Jafar ta sakar masa harara, haɗe da murguɗa masa baki.

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA BIYAR

Kasancewar sunan gidan baba Isuhu ya zo a lokacin hutun zangon karatu ya sa ilahirin zuri'ar gidan sun hallara, musamman da ya kasance baba Mamman ya dawo gida ne gabaɗaya domin lokacin ritayarsa ta kusa. Kuma a wannan kwanakin ne yake shirin tarewa a katafaren gidan da ya gina a nan cikin Unguwar rijiyar zaki da ke jihar Kano. Hajiya Saratu da iyalanta sai shan ƙamshi suke yi suna kallon mutane ɗaiɗai, don ko maganar arziƙi ba ta cika haɗa ta da sauran facalolinta ba. Sanin halinta na raini da wulaƙanci ya sa suma sauran mutanen gidan suke kama mutumcinsu ba tare da sun shiga sabgarta ba.

Asalin Tarihinsu

Malam Haruna mai shanu shi ne ainihin cikakken sun marigayi malam mahaifin su baba Isuhu. Asalinsa mutumin garin Rigana ne da ke cikin ƙauyen lambar ƙunci, ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyukan da ke jihar Kanon Dabon Najeriya. Sunan mai shanu ya samo asali ne tun a wurin mahaifinsa kasancewarsa fitaccen bafulani a wannan ƙauyen, duk girman garin Rigana babu mai albarkar shanu da dabbobinsa. Yana da matar aure ɗaya da 'ya'ya biyu sakancewar duka maza, Malam Haruna shi ne babba sai ƙaninsa mai bin sa Sa'idu wanda bayan su mahaifinsu bai sake haihuwa ba. Bayan mahaifiyar su malam mahaifinsu ya auri mata biyu sai dai ko ɓatan wata babu wacce ta taɓa yi. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna samari yayin da mahaifinsu ya rasu bayan da kowannen su ya yi aure a lokacin Malam haihuwarsa biyu.

Baffajo tun da ƙuruciyarsa yakan ɗebi shanu da awakinsa su tafi garuruwa kiwo bayan wani lokaci sai ya dawo gida, hakan yake yi har zuwa lokacin da su Malam suka zama samari suma yake nuna musu hanyar kiwon shanu. Sai dai tun suna yara ya fahimci sam ba su da ra'ayin kiwace-kiwacen shanun da yake yi, bayan da mahaifinsu ya rasu sai suka ɗora daga inda ya tsaya sai dai su ba kamar Baffajo ba. Don tun bayan da ya rasu bai fi sau uku zuwa huɗu suka fita da shanu zuwa wasu garuruwan ba.

A wannan lokacin ne kuma watarana bayan malam ya fita da shanun su da suka gada a wurin mahaifinsu, ya yi nisa sosai da garinsu sai ya faɗa tarkon wasu 'yan fashin daji. Kasancewar kuma sarkin yawa ya fi sarƙin ƙarfi sai suka yi masa ƙwacen shanu da yawa, kaɗan ya rage ba su hallaka shi ba ya dawo gida da tsirarun shanun da ko goma ba su kai ba. Wannan yanayin da suka shiga wasu sun dasa zargin har da saka hannun mutanen garinsu, yayin da wasu kuma suka ce jarabta ce kawai daga wurin Ubangiji.

Dalili kenan da ya sa bayan da malam ya warke suka haɗa kai shi da ɗan uwansa suka bar garin gabaɗaya tare da sayar da shanunsu, suka dawo wani ɗan ƙauye a nan garin Kura suka kafa kasuwancin su. Kuma cikin hukuncin Ubangiji sai Allah ya saka musu albarka.

Hauwa kulu Ibrahim mai allo shi ne cikakken ainihin sunan Dada asalinta mutuniyar garin Bauchi ce, baƙar bafulatana ce tana da kyau daidai gwargwado. Mahifinta Malamijo ɗan gidan malamai ne domin a rigarsu gidan su Dada ba ɓoyayyan gida ba ne. Mahaifinta yana da mata biyu da 'ya'ya bakwai. Musa shi ne ainihin sunan malam na Madina, kuma shi ne babban yayansu Dada uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Ya auri matarsa bayan zamansu mai tsawo Allah Ya yi mata rasuwa, sai dai bayan ita ya yi aure-aure da dama bai taɓa samun haihuwa ba. Dada ita take bin shi sai kuma Fatsime take bin Dada sai dai akwai tazara sosai tsakanin Dada da Fatsime. Fatsime ta rasu a wurin haihuwa, ta rasu ta bar 'yarta Abuwa dalilin da ya sa Dada ita da na Madina kaɗai suka rage waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya.

A lokacin da mahaifiyar su Dada ta haifi Fatsime har ta cire rai da sake samun haihuwa.
Hasiya, Safare, Sule da Gali sune sauran 'yan uwan Dada da suke Uba É—aya.

Malam ya haɗu da Dada ne a lokacin da suka tafi kiwo garin Bauchi tun mahaifinsu na raye, don haka ba a ɗauki lokaci ba aka tsayar da maganar aure bayan wani lokaci aka ɗaura musu aure. Da yake Dada nesa da garinsu za a kai ta sai mahaifinta ya haɗa ta da ƙanwarta Fatsime, a kan bayan wani lokaci idan Dada ta saba sai Fatsime ta dawo. Sai dai ko da Malamijo ya buƙaci Fatsime ta dawo malam da kanshi ya je har garin Bauchi ya roƙi arziƙin a bar musu Fatsime a wurin su. Ganin yadda malam ke kula da Dada da kuma girman da yake ba shi sai ya kawar da kai ya haƙura ya bar masa ita.

Dada da malam sun haifi 'ya'ya tara bakwai maza sai biyu mata. Baba Yunusa (Soja ne), baba Mustafa (Road safety ne), baba Idris (Malamin makarantar secondry ne), baba Mamman (ÆŠan sanda), baba Rufa'i (Likita), Atika, Halimatu, marigayi Umaru wato mahaifin Uwani sai kuma Baba Isuhu (Sayar da itace yake yi).

Baba Sa'idu (Ƙanin malam) Yana da mata ɗaya da 'ya'ya biyar. Biyu maza sai uku mata. Ya auri matarsa ne tun a garin Rigana, kuma tin bayan komawarsu Kura da suka fara kasuwanci shi da ɗan'uwansa, sai ya fara tafiye-tafiye zuwa garuruwa. Sannu a hankali sai nemansa ya fi ƙarfi a garin Zaria, don haka ya ɗauki iyalinsa suka koma can da zama. Cikin ikon Allah kowannensu ya ci gaba da zama da iyalinsa. Da yake Dada kwanika ta dinga yi gabaɗaya 'ya'yanta tazarar su babu yawa, kuma a lokacin da take da cikin Baba Isuhu ne Allah ya yi wa malam rasuwa. Kafin rasuwarsa ne ya biya mata Makka, zuwan farko umara ta je ta yi sai zuwa na biyu da suka je tare suka yi aikin Hajji.
Malam Sa'idu ya kaɗu da rashin ɗan uwansa domin ko mutuwar mahaifinsu ba ta bige shi haka ba, daga nan kuma ya riƙe dukiyar ɗan uwansa da amana yana juya musu. Kuma ya ci gaba da tallafa wa Dada ita da yaranta, ya tsaya musu kai da fata suka samu ilimin addini da na zamani kuma har Allah ya ci da su suka samu aikin yi. Sai dai ba da aikin Gwamnati kaɗai suka dogara ba domin suna harkar kasuwancin kayan robobi da harkar kayan abinci.

Baba Mamman yana da matar aure ɗaya Hajiya Saratu da yara biyar. Jafar shi ne babba, Ibrahim, Shukra, Jidda, sai Mufida wacce suke kira da Auta. Hajiya Saratu 'yar aminiyar mahaifin baba Mamman ce, ba ta da son mutane ko kaɗan. Mace ce mai faɗin rai da taƙama uwa-uba tana da son kanta, ga ta da tsananin kishi sannan akwai ta son hulɗa da matan masu kuɗi. Wannan halin na ta ya sa ko kaɗan ba ta jituwa da Dada, kuma kusan halayenta ne su Shukra suka kwasa gabaɗaya. Jafar da Ibrahim ne ba su da irin halinta sai Auta don haka har sun fi su Shukra sabo da mutanen cikin gida.

Gidan marigayi malam Haruna mai shanu gidan gandu ne da ya haɗa kakanni, iyaye, jikoki da kuma 'ya'yan jikoki. Baba Mamman da Baba Yunusa ne kaɗai ba sa zaune a cikin gidan, kasancewar yanayin aikinsu da sauye-sauyen garuruwan da ake yi musu a wurin aiki. Amma kowannensu yana da ɓangarensa a cikin gidan, idan suka zo hutu suna sauka da iyalansu a ciki.

Marigayi Umaru Haruna Mai shanu shi ne mahaifin Uwani, ya rasu tun mahaifiyar Uwani na da cikinta wata bakwai sakamakon hatsarin mota. Maryama Shu'aibu shi ne ainihin sunan mahaifiyar Uwani, dalilin mutuwar mahaifin Uwani ya sa Dada da su Baba Mamman suka ci gaba da kula da ita. Bayan wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta haifi jaririyarta, ta ci burin idan namiji ne ta mayar da sunan mijinta Umaru. Amma da ta haifi mace su Dada suka tambaye ta sunan da take son a raɗa wa jaririyar, da kanta ta ce a saka sunan Dada saboda irin karamcin da suka nuna mata, sai ake kiranta da suna Uwani. Bayan da aka yaye Uwani ne mahaifin Maryama ya nemi da ta dawo gabansa da zama, domin zawarawa suna ta zuwa kai masa gaisuwa da nuna ƙoƙon bararsu a kan aurenta. Ranar da za ta tafi ne Dada ta nemi da ta bar mata Uwani saboda soyayyar da take yi wa mahaifinta, idan tana ganinta za ta dinga jin daɗi. Bayan komawar mahaifiyar Uwani gidansu ko shekara ba ta rufa ba aka ɗaura mata aure da wani mutum, a lokacin yana da aure da mata ɗaya da yara huɗu. Maryama ta aure shi ne ba don tana son shi ba, sai don kawai ta yi wa mahaifinta biyayya amma har lokacin zuciyarta na ga mahaifin Uwani. Garin da take aure yana nesa da garin su Uwani sosai, kuma ta haifi yara biyu da malam Salihu mace da namiji, sai dai ko kaɗan ita da kishiyarta ba sa jin daɗin zama da shi sakamakon mugun halinsa.
Chapter 8 · 0% Book details