← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 71

Sashe 2

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Uwar garkeeeeeena! Baba Isuhu ne uwar garkenaaaa." Dada ta zaro ido waje. "Ke Uwani ko dai gamo kika yi ne? Shi Isuhun ne ya zama uwar garke? An ya lamarinki Uwani babu jifa a ciki?" Dada na gama magana ba ta ji daga bakin Uwani ba ta fashe da kuka tana faÉ—in.

"A'ubikalimatillahi tamma min sharrin ma kalaƙa. Aniya bi aniya wallahi aniyar kowa ta bi shi, Allah Ya kai mu wayewar gari wallahi sai na je gidan Sarkin aska na karɓo miki ƙaiƙayi, ni za a kashe da ƙullutun baƙinciki..." Uwani ta katse Dada daga dogon jawabin da take yi.

"Dada wallahi ganin idona Baba Isuhu ya ɗauke mini uwar garke ya miƙa wa Mai gari ta katanga."
"Ke yarinyar nan ki ji tsoron Allah, shi Isuhun nawa ne kike jifa da sata? Isuhun da ko yatsa ba za a saka masa a baka ya tauna ba?" Ganin haka ya sa Uwani ta fice daga ɗakin tana faɗin, "Wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ka dawo mini da uwar garkena. Wayyo Allah garkeruruna!" Jikin Dada nan take ya ɗauki karkarwa don haka ta miƙe cikin sauri ta bi bayan Uwani.

Kafin wani lokaci wasu daga cikin mutanen gidan suka fara fitowa, kowa ya tambayi Uwani amsa ɗaya take bayarwa 'Uwar garke, Baba Isuhu ya miƙa wa mai gari ta katanga.' Carko-carko suka yi domin ga dukkan alamu sun fara aminta da kalaman Uwani, sakamakon sun duba garken awakinta sun ga babu uwar garke.

"Ina shi Isuhun ne?" Baba Idris ya tambaya. Kallon juna suka shiga yi don haka ya bayar da umarnin a je sashen shi a kira shi.
Sahabi da Tasi'u ne suka nufi sashen Baba Isuhu, sun jima suna buguwa sannan ya buɗe ƙofa, yamutsa fuska ya hau yi tamkar wanda aka tasa yana bacci ya ce. "Kai waye a tsohon daren nan yake mana bugu haka?"

"Baba Isuhu dama Baba ne ya ce a taso ko?" Suka amsa masa.
"Ni kuma? A tsohon daren nan? Ko ciwon Yaya ne ya tashi?" Baba Isuhu ya jefa musu tambayoyi kamar bai san abin da yake faruwa ba. Girgiza masa kai suka yi, suka wuce gaba yana biye da su a baya. Yana zuwa ya samu mutane a tsaye carko-carko, tun daga nesa gabansa ke dukan uku-uku amma gudun tonuwar asirinsa sai ya yi hanzarin aro mayafin jarumta ya lulluɓa wa jikinsa. Ya sake aro fuskar mamaki ya ɗora a saman tashi, cikin mamaki ya furta.

"Yaya lafiya na ganku haka a tsohon daren nan?"

"Uwani ce ta zo mana da wata magana..." Duk abin da ya faru Baba Idris sai da ya zayyane masa sannan ya ɗora da cewar, "Ina Uwar garke take?" Duk da ƙirjinsa bugawa yake amma bai hana shi fututtukewa ba ya ce. "Haba Yaya yanzu duk faɗin gidan nan a rasa wanda za a laƙa wa sata sai ni? Me zan yi da wata uwar garke? Shekarar uwar garke nawa a gidan nan? Amma kawai don yarinyar nan ta shirya ƙaryarta sai a hau kai a zauna, shi kenan tun da ni ne ɓarawon da kuke zargi a faɗa mini nawa ne kuɗinta zan biya."

Ganin yadda ran Baba Isuhu ya ɓaci ne ya sanyaya jikin ilahirin mutanen da ke wurin, Dada ta zauna daɓar haɗe da rushewa da matsanancin kuka.

"Tsakanina da wannan ɓarawon ni kam sai na kai kukana gaban Ubangiji, ina zaman zamana zai haɗa mini husuma a cikin zuri'ata." Baba Mustafa ya ɗago Dada sannan ya ce, "Yanzu dai duka mu bar maganar nan ni nan zan sayo miki wata ƙatuwar tinkiyar da ta fi uwar garke girma kin ji Uwani." Jin haka ya sa Uwani ta rushe da kuka.

"Wallahi ni uwar garke nake so, kuma ko kur'ani aka ba ni zan dafa ganin idona na ga Baba Isuhu da uwar garkena..." Baba Mustafa ya yi saurin katse ta don haka kawai ya ji ya yi na'am da kalaman Uwani, don haka ma ya ce. "To shi kenan ba tinkiya kaɗai zan saya miki ba, kina son ɗan maraƙin sa ko?" Ba don Uwani ta daina jin zafin rashin uwar garke ba ta amsa, sai don son da take wa ɗan maraƙin sa. Saboda haka ta gyaɗa masa kai tana goge hawaye, a gefe ɗaya tana kuma ƙudurtar irin fansar da za ta ɗauka a kan Baba Isuhu don ta yi rantsuwa da Allah jinin Uwar garke ba zai tafi a banza ba. Daga haka gabaɗaya kowa ya watse, Uwani da Dada suka yi sashensu sai dai buta ta sake ɗauka ta fito kamar za ta banɗaki kai tsaye ta wuce sashen Baba Isuhu cikin sanɗa, ta ci sa a bai rufe ƙofa ba don haka tana laɓe daga bakin ƙofar ɗakinsa ta ji Lami na faɗin.

"Isuhullena ai ka birge ni da ka ƙaryata shegiya, haka kawai da tuni da tozarta ka a gaban mutane." Baba Isuhu ya saki dariya ya ce. "Ke zan cen da nake miki gobe warhaka mun riga da mun gama ɓarje dabgen kan uwar garke." A gefe ɗaya ta ji muryar Goggo Sala na cewa. "Yanzu dai tun da aikin gama ya gama ai sai ku ja baki ku yi shiru, amma dai Isuhu dole ka badda kama idan za ka shigo da uwar garke don ka san dole a saka maka idanu." Baba Isuhu ya fashe da dariya yana shirin yin magana daga can bayan ƙofa suka ji muryar uwar garke ta ce. "Meeeeeeeeh." A zabure suka kalli juna cikin tashin hankali.
"Kukan uwar garke nake ji a tsakar gida Isuhu leƙa ka gani..." Lami ta faɗa da sauri.

"Ba ki da hankali Lami, ya za a yi ganin idona Talle ya tafi da uwar garke kuma na ji muryarta ke ki leƙa mana..." Kalaman bakinsa suka katse sakamakon sake jin kukan Uwar garke ta ce, "Meeeeesuhuuuu."

Wani abu ne ya tsargawa Baba Isuhu tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa.

"Isuhu kamar sunanka na ji a cikin kukan uwar garke." Lami ta faÉ—a a tsorace.

"Meeeeeesuuuhuuuu." Uwani da ke laɓe ta sake maƙale murya ta faɗa da yanayin kukan uwar garke, tana gama faɗa ta dokon ƙauren ɗakin da suke ciki. A zabure Lami, Isuhu da Goggo Sala suka faɗa uwar ɗaki, Goggo Sala da ke ɗaure da ɗaurin ƙirji tun a falo zanin jikinta ya faɗi ba tare da ta sani ba. Goggo Sala da baba Isuhu suka shige bayan ƙofar uwar ɗaki ita kuma Lami ta maƙale a gefen gado, shirun da suka ji ba a ƙara kukan tinkiyar ba ne ya sa suka fara dawowa hayyacinsu. Goggo Sala ta kai idonta jikinta sai a lokacin ta yi ido biyu da tsurar ɗan fatarin (Under wear) da ke ƙugunta, ga ƙirjinta zube a saman kan Baba Isuhu da ke tsugunne a ƙasa. Sai a lokacin ta lura da hannuwan baba Isuhu da ke riƙe da ɗan fatarinta. Cikin matsananciyar kunya ta ce.

"Kai Isuhu wanne irin iskanci ne haka saboda Allah za ka nemi shigewa cikin fatarina, ni fa ƙanwar mahaifiyar matarka ce ." Cikin rashin sani Baba Isuhu ya miƙe tsaye sai jin ƙirjin Goggo Sala ya yi a saman fuskarsa, yana ɗagowa suka haɗa ido da ita. Ganin abin kunyar da aka tafka cike da borin kunya ta ce, "Amma dai Isuhu yadda ka kwaso mini ƙirji ina a matsayin sirikarka Allah Ya kwashe maka albarka."

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA BIYU

Uwani da ke laɓe tana jin su sai da ta saki murmushi sannan ta wuce ɗakin da Lami da Goggo Sala suke kwana, tana shiga ta samu mai sunan malam yana kwance yana bacci. A hankali ta ɗauko shi sai da ta zo tsakar gida, ta saka shi a cikin ƙatuwar tukunyar da ake dafa wa Lami ruwan wanka amma babu ruwa a ciki. Ta saka hannu ta ɗan jijjiga shi don ya tashi, saboda dama ta jima da sanin Baba Isuhu matsoraci ne na bugawa a jarida, don haka ta gano lagonsa.

Baba Isuhu ba ƙaramin ɗacin kalaman Goggo Sala ya ji ba, ya saci kallonta rai a ɓace ya ce.

"Allah Ya kwashe mana dai, ni allan-musuru ne na san ke ce a wurin? Wallahi ni da na ji na ɗebo abu a kaina na ɗauka hannuwan Lami ne." Baba Isuhu ya ƙarasa maganar yana fitowa falo. Ya bar Goggo Sala a tsaye cike da takaicin abin ya faɗa.

"Tsabar iskanci da wulaƙanci har ƙirjina ya yi lalacewar da za a ɗebo su aka a ɗauka hannuwa ne?"
Goggo Sala ta ayyana a ranta.

Yana zuwa ya ji mai sunan malam ya tsanyare da kuka. Kusan tare suka kalli juna shi da Lami, sai dai jin shiru babu kukan uwar garken ya sa suka ɗan saki jikinsu. Cikin sanɗa suka fara takawa a hankali har suka fita tsakar gida, suna yunƙurin tafiya ɗaki suka ji kukan mai sunan malam a cikin tukunya ga shi kuma tukunyar a rufe. Lami ce ta yi ƙarfin halin buɗewa nan take ta yi tozali da shi.

"Isuhu akwai abin da yake shirin faruwa wallahi." Lami ta faÉ—a murya na rawa.
"Lami ko dai a garin ɗaukar uwar garke ne na tako aljanu? Na shiga uku kada su taɓa mini mai sunan malam." Baba Isuhu ya ƙarasa maganar cikin kuka, Goggo Sala na ƙarasowa suka wassafa mata abin da yake faruwa.

"An ya kuwa Isuhu uwar garken ka ɗauka ba aljanu ba kuwa? Gaskiya ruwa ba ya taɓa tsami banza."
Cikin Baba Isuhu ya sake ɗurar ruwa, ya waiga a hankali yana kalle-kalle daga can kusurwar bango ya hango kamar mutum a tsaye, Uwani da ke raɓe ganin kar ya gano ta ya sa ta yi wata girgiza haɗe da cewa.

"Meeeeesuuuuhuuuu zaaaaan cinyeeeeee idoooonnnnkaaaaa."

Jin abin da aka faÉ—a ya sa Baba Isuhu da su Lami suka faÉ—a É—akin da su Lami suke jego. Uwani ta samu ta saÉ—aÉ—a sannan ta wuce sashen Dada tana sakin murmushi, ko ba komai ta gano lagwansu da yadda za ta dafa su a ruwan sanyi.
Chapter 2 · 0% Book details