← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 71

Sashe 57

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Mun yi mata gwaje-gwaje da hotuna so yanzu akwai result da muke jiran fitowarsa anjima. Idan ya fito ne In shaa Allah za mu san halin da abin cikinta yake ciki, gwaji na farko ya nuna mana Positive daga ba ya kuma ya nuna mana negetive." Wani irin gumi ya shiga karyo wa Jafar, sai da ta gama yi musu bayanan da ya dace sannan suka fice daga ofis É—in. A harabar asibitin suka hango Aunty a zaune kusa da Dada, Daddy ne ya samu Dada ya kwantar mata da hankali don har lokacin ban da kuka babu abin da Dada take yi.

"Maza kira mini Maryama na sanar da ita halin da ake ciki." Dada ta faɗa tana miƙa wa Aunty wayar.
"Amma Dada da an bari aga yanayin jikin nata kada a tayar mata da hankali." Daddy ya faÉ—a.
"Idan kuma ta mutu sai mu ce ta zo ta ɗauki gawar 'yarta ko? Mamman ka fita idona na rufe." Dada ta faɗa rai a ɓace.

Aunty ce ta kira Maryama tana ɗauka ta miƙa wa Dada, sai da Dada ta share hawaye sannan ta ce mata Uwani babu lafiya suna asibiti. Da yake Maryama mace ce mai kara sai cewa ta yi tun da su suna wurin ita ba sai ta zo ba, jin haka ya sa Dada ta rufe ta da faɗa don haka ta ce gata nan zuwa. Aunty ce ta karɓa ta yi mata kwatancan asibitin sannan suka yi sallama.

Cikin ɗakin da Uwani ke kwance Jafar ya shiga, tana kwance tana sauke numfashi sama-sama. Kallon halin da take ciki ya sa Jafar ya ji zuciyarsa na zafi, tabbas uwa-uwa ce amma a wannan karon bai ji daɗin abin da Mami ta yi masa ba. A hankali ta fara motsa hannunta, ya ƙarasa gaban gadon da sauri. Buɗe idonta ta yi tana kallon saman silin ɗin ɗakin, Jafar ne ya matsa ya riƙo mata hannu suna haɗa ido ta ɗauke idonta. Nan take komai ya dawo mata, wata irin tsanar Mami ta ɗarsar mata.

"Sannu!" Jafar ya furta a sanyaye.

"Ka kai ni wurin Dada!"
Dam! Ƙirjin Jafar ya buga.
"Me kike so na yi miki?"

"Wurin Dada nake son zuwa!"
"Dada tana waje!" Ya bata amsa. Fita ya yi yana kiranta, jin Uwani ta farka ya sa farinciki ya mamaye Dada.

"Sannu Uwanita!" Jin muryar Dada ya sa Uwani ta fara ƙwalla, ta ɗan runtse ido jin ƙasan mararta da jikinta har lokacin na ɗan yi mata ciwo.

"Ki daina kuka kin ji Uwanita, yanzu me kike so?" Uwani ta girgiza wa Dada kai sannan ta ce.
"Kawai ki zauna a nan." Da sauri Dada ta amsa mata.

Abin duniya goma da ashirin ya haÉ—e wa Jafar don ya lura Uwani ko kallonsa ba ta son yi, ko sannu ya yi kata ba ta amsawa. Ruwan tea Auta ta kawo aka ba wa Uwani ta sha kaÉ—an, bayan wani lokaci nurses suka zo suka sake yi mata allurar bacci.
Cikin kwana uku jikin Uwani ya yi kyau, kuma duk gwaje-gwaje an yi mata an tabbatar da cikin jikinta na nan bai ɓare ba. Sai dai an gargaɗe su sosai a kan su dinga kula da ita, kuma kada ta dinga aiki kowanne iri har zuwa lokacin da cikinta zai kai wata shida.

Tun lokacin da Dada ta ji an sallame su ta ce da Daddy ya wuce da su Kura gabaÉ—aya, jin haka ya sa gaban Jafar ya faÉ—i amma sai ya danne don ba shi da bakin magana. Har za su shiga mota Dada ta dubi Jafar ta ce, "Ka kira mini uwarka a yanzu ta same mu a Kura ina son ganinku gabaÉ—aya." A sanyaye Jafar ya amsa, sannan Dada ta shige cikin mota.

Zuwan su Dada gida ya sa gabaÉ—aya iyalan gidan suka shiga aka ci gaba da sake duba jikin Uwani, sai da duk suka watse sannan Dada ta ja Uwani É—aki fuska a haÉ—e ta furta.

"Uwani!" Jin yadda Dada ta kira sunanta ya sa Uwani ta fahimci babu wasa a maganarta, Uwani ta amsa sannan Dada ta ci gaba da cewa.
"Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, a yau zan zartar da wani hukunci wanda na san ba lallai ya yi miki daɗi ba. Amma ni zan aiwatar da shi ne don na ƙwato miki 'yancinki, domin Saratu ta kai ni magaryar tuƙewa. Ba zan zura ido ta zo ta kashe mini ke a banza da wofi, wallahi idah kika sake kika ba ni kunya sai ranki ya yi mugun ɓaci. Kuma sai ki je ta kashe ki ta kashe banza." Tun da Dada ta fara magana ƙirjin Uwani ya buga, cikin ƙarfin hali ta amsa mata.

Gabaɗaya 'ya'yanta sai da ta sa Baba Inusa ya tara mata su, ta sa aka kira mahaifiyar Uwani, Jafar da Uwani suna zaune a gefe kowa da abin da yake saƙa wa a ransa. Sai da Dada ta dube su ɗaya bayan ɗaya ta yi musu sallama fuska a haɗe, don haka suka amsa mata kowa ya sha jinin jikinsa musamman Daddy don ya san wannan zaman ba lallai ya haifar da samun ɗa mai ido ba.

"Kamar yadda kuka sani a baya, a wannan wurin da muka zauna a shekarun baya na zartar da umarnin auren Uwani da Jafar. To a yanzu kuma a nan wurin za a warware auren a gabanku." Wani abu ne ya tsarga wa Jafar tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa, lokaci ɗaya ya ji wata irin juya na fisgarsa.

"Ba tun yau ba Saratu na san irin ƙiyayyar da kike nuna wa Uwani, to ki sani Jafar ba shi ne autan maza ba wallahi Uwani ba na haufin za ta samu wanda ya fi shi komai a gaba. Duk abin da kika yi mata ki je ke da Allah, amma aure da Jafar har abada Uwani ta gama zama da shi. Yanzu haka saura kwana goma ko takwas ne aurensa da yarinyar da kike so ko? To ya je ya auri zaɓinki, amma ina me tabbatar muku da Jafar zai rubuta wa Uwani takardarta, Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alheri." Gabaɗaya ɗakin tsit ya yi kowa ya fara karanta wasiƙar jaki. Dukkansu sun san abin da Mami ta yi sam ba ta kyauta ba amma kuma shi Jafar mene ne laifinsa?

"Don Allah Dada ki yi haƙuri..."
"Dakata Mamman kada ka faÉ—a mini maganar banza, saboda ba 'yarka ba ce ko? Tun da kai ka zama sallamamme ba ka isa da gidanka ba Uwani ba za ta zauna matarka ta kashe ta ba, Jafar ko shi kaÉ—ai ya rage a duniya Uwani ba za ta koma gidansa ba." Dada ta furta a zafafe.
Baba Inusa shi ma haƙuri ya ba wa Dada gabaɗaya ta rufe su da faɗa, tabbas sun san halin Dada idan ta kafe a kan magana ɗaya babu mai juya ta. Duk yadda suka so shawo kanta lamarin ya gagari Kundila, Jafar ya haɗiyi yawu mai ɗaci zuciyarsa na bugawa ya miƙe zai fita.

Dada ta dubi Daddy ta ce, "Idan har na haife ka na isa da kai, wallahi ka sa Jafar ya ba ta takardarta. Idan ba haka ba kuma zan kai shi kotu ya ba ta a can. Kuma umarni ne zan bayar kada na sake ganin ƙafar Jafar a gidan matuƙar ba takardar Uwani ce za ta kawo shi ba, idan har ya kawo mata takardarta to ba zan yi masa iyaka ba.." Jafar bai ƙarasa jin kalaman Dada ba ya fice daga ɗakin rai a ɓace, Daddy ya dubi Mami cikin ɓacin rai ya furta.

"Yadda Uwani za ta zauna a gaban Dada kema ki wuce gidan mahaifinki, har sai ranar da Jafar zai ba wa Uwani takardarta zan kawo miki taki. Ki saurare ni da kyau, wallahi kin ji na rantse miki mutuwar auren Uwani daidai yake da naki mutuwar auren." Shi ma Daddy yana gama magana ya fice daga ɗakin, ganin da gaske Daddy yake ya sa Mami ta fashe da kuka sai dai babu wanda ya bi ta da kallon arziƙi.

A cikin mota Daddy ya samu Jafar ya kifa kai da sitiyarin mota, murfin motar Daddy ya buÉ—e yana ambatar sunan Jafar. Yana É—agowa ya ga hawaye bibbiyu na bin fuskarsa.

"Kada ka ga laifin Dada, duk abin da ya faru laifin mahaifiyarka ne. Ka je ka yi addu'a idan zamanka da Uwani ne mafi alheri Allah Ya daidaita ya sanyaya zuciyar Dada, idan kuma babu alheri Allah ya zaɓa muku mafi alheri. Aurenka da Safna saura kwana takwas, idan Allah Ya kaimu aure babu fashi tun da ita ce wacce mahaifiyarka take so." Daddy na gama magana ya saki murfin motar ya wuce tashi motar, kai tsaye gida ya wuce zuciyarsa na suya.

Sai da kowa ya watse Uwani ta kwanta a kan gado hawaye na bin gefen fuskarta, tabbas ita kanta a yanzu auren Jafar ta haƙura da shi tun da ta lura mahaifiyarsa rayuwarta take nema ido rufe. A ɓangare ɗaya ta ji wata irin soyayyarsa na nuƙurƙusar zuciyarta. Ta shafa cikinta tuna hirar da suka yi da yake ta zuba mata hirar idan ta samu ciki da irin tarairayar da zai dinga yi mata. Don tun da ta fahimci tana da ciki ta ɓoye masa, ta ci alwashin sai cikinta ya kai wata uku za ta sanar da shi.

Koda Jafar ya koma gida falonsu ya wuce, kwanciya ya yi a kan kujera ya zurfafa dogon tunani. Don yadda yake ji ko me za a yi masa ba zai iya rabuwa da Uwani ba, kiran Safna ne ya shigo masa waya a daƙile ya ɗauka murya babu walwala. Jin yanayin muryar Jafar ya sa ta fahimci akwai abin da yake damunsa, tambayar duniya ta yi masa ya ce mata babu komai. Maganar event-event ɗin da za su yi ta yi masa tashin farko Jafar ya ce mata ba zai samu halarta ko ɗaya daga ciki ba, alhalin ba haka suka tsara da shi ba a baya ba. Jin haka ya sa Safna ta rushe da kuka, sannu a hankali ya runtse idonsa yana jin kukanta har cikin ransa.
Chapter 57 · 0% Book details