← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 71

Sashe 40

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Watarana kimanin ƙarfe biyun dare Lado ya fito cikin sanɗa ya nufi garken Uwani, don a wannan ranar Mami ta ba shi dubu biyar ta ce ya ɗauki ɗaya daga cikin awakin Uwani ya ba ta guba. Lado cikin sanɗa ya a jiye kofin da yake kaɗa shinkafar ɓeran a ciki, ya shiga cikin garke a lokacin awakin duk suna kwance. Lado na ɗagowa ya ga wani ɗan bunsuru ya ƙura masa ido yana kallo, Lado ya waiga hannu da dama sannan a hankali ya furta.
"Wato kai don ubanka kallona kake yi ko? To alƙur'an yau kwananka zai ƙare, shege kana fama da ƙwala-ƙwalan ido kamar gurjiyar lahira." Lado na gama magana ya kai wa ɗan akuyan duka a kanda, sai kuma shi ma Lado ya ji kamar an shafo masa ƙeya ta baya, da sauri ya waiga amma bai ga kowa ba.
Sunkuyawa ya yi ya cicciɓo ɗan bunsurun, ga mamakinsa ya ji shi da wani irin nauyi tamkar wanda ya ɗauki ƙatuwar tinkiya, Lado yana tafe yana nishi har zai fita daga cikin garke ya ji bunsurin ya ce.
"Idan ka fitar da ni daga cikin garken nan kai ma sai ka ci ubanka Lado. Kuma ka sauke ni daga kanka ka ga idan za ka iya." Lado na jin haka ya fara fitsare wandonsa cikin tashin hankali, ya sunkuya zai sauke shi ya ji bunsurun ya manne da wuyansa. Dariya ya ji bunsurin ya saki ya ce, "Ai ni da kai mutu ka raba Ladodo." Bunsurun na gama magana ya zura hannu yana shafa ƙirjin Lado sai kuma ya ce, "Ni Lado ko haike maka zan yi ne ma tun da kai ka kawo kanka?"

Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala 800 ne 🫠

#Ummou Aslam Bint Adam🌚
Wasu 'yan tagwayen ƙwalla ne suka zubo wa Lado jin abin da bunsurun ya faɗa, jiki na karkarwa ya furta. "Don Allah ka yi haƙuri ka yi mini rai ka rabu da ni. Wallahi ba zan sake taɓa ku ba." Bunsurun ya yi kasaƙe yana sauraronsa sannan ya kai hancinsa ya fara sunsunar gefen wuyan Lado, har zuwa wurin kunnuwansa sannan ya furta. "Ai na riga da na gama magana Ladodo, idan kuma ka bari na sauka daga bayanka waccen gubar da ita zan shayar da kai." Tashin hankalin da Lado ya shiga ne ya sa ƙafafuwansa suka yi masa sanyi, ya tsugunna a cikin garken awakin hawaye na zuba. Bunsurun ya sake sansano wuyan Lado sannan ya ce. "Lado ka yi auren fari kuwa? Don na ji ƙamshin samartaka kake yi" Lado ya fara girgiza kai yana hawaye, bunsurun ya zura ƙafarsa ta gaba cikin rigar Lado yana shafa ƙirjinsa, wani abu ya ji ya tsire shi kamar an caka masa allura, lokaci ɗaya ya ji ƙirjinsa ya yi nauyi ya kuma yi masa ƙababa. Lado na kai kallonsa sai gani ya yi mama ya cika masa ƙirji, ya ta ƙarƙare ya fasa ihu hankalinsa a yanzu har ya fi na kowanne lokaci tashi. Fuska cike da hawaye ya ce, "Na shiga uku an mayar da ni mata-maza, don Allah ka yi mini rai ka mayar fa ni yadda nake wayyo Allahna!" Sai a lokacin bunsurun ya sauka daga bayan Lado, ya fara tafiya yana kaɗa masa jela sannan ya ce. "Lado duk fa ihun da za ka yi babu mai jin ka, don haka idan ka na son na mayar da kai daidai sai ka kawo mini Saratu a daren gobe."

Tun bai gama magana ba Lado ya fara gyaÉ—a kai ya ce, "Wallahi ko yau kake so na kawo ta zan kawo maka ita." Bunsurun kunnen Lado shafa da kofatonsa ya ce.
"Ko mu mayar da kunnuwanka na giwa ne?" Da sauri Lado ya ce. "Don Allah ku bar ni haka wallahi wannan ma ban san ina zan kai ƙirjin nan ba." Bunsurun ya furta. "Ai ni da na dasa maka na san yadda zan yi da su, kai dai ka kawo ido ka sa ka gani ka ji Lado." Daga haka bunsurun ya tasa Lado a gaba ya saka shi tsallen kwaɗo, Lado yana yin tsallen kwaɗo bunsurun yana ranƙwala masa kofotonsa a fuska da kansa. Sai da Lado ya gama galabaita sannan ya nemi bunsurun sama da ƙasa ya rasa, shafo ƙirjinsa Lado ya yi ya ji yana nan kamar na mata ai kuwa ya rushe da kuka. Ga fuskarsa duk ta kumbure ta yi ja abin ka da farin mutum, saboda har marinsa bunsurin ya dinga yi da kofato. Ganin kukan ba zai kai Lado ba ya sa ya faɗa ɗakinsa ya haɗa kai da gwiwa, yana da-na-sanin zuwansa aiki gidan Daddy.

Yanda Lado ya ga rana haka ya ƙarasa ganin darensa, sai da aka yi assalatu bayan gari ya yi haske sannan ya samu ya faɗa banɗaki ya ɗauro alwala ya yi sallah. Jingina ya yi da bango da ya kai kallo kan ƙirjinsa sai kawai ya ɓarke da kuka, tashi ya yi ya tuɓe rigar jikinsa ya ciro wata rigar sanyin sa ya saka sannan ya ɗauko wata rigar shadda ya ɗora a kai. Da yake lokacin zafi ne nan take ya fara sharɓa gumi, bai damu da gumin ba tun da ya samu ƙirjin ya rufe ba za ka fahimta ba idan ba ƙura masa ido ka yi ba. Tun da ya ga gari ya yi haske yake alla-alla Mami ta fito don ya san ƙaryar da zai yi mata, wacce za ta sa da daddare ya kai ta tirken Uwani.

Ƙarfe shida daidai na safe Salim ya kira Mami hankali a tashe sakamakon rashin lafiyar da Shukra take fama da ita, da yake Daddy ba ya gari a gagguce Mami ta shirya sai da ta je bakin gate, sannan ta leƙa ɗakin Lado ta hango kwance yana kallon silin da alama ya lula duniyar tunani. Har Mami ta fice daga gidan Lado bai sani ba, kai tsaye Mami ta wuce asibitin Noor clinic inda aka kai Shukra. A lokacin da Mami ta je ta samu bacci, sai da suka gaisa da Salim ta fara tambayarsa abin da yake damunta. Salima sai da ya sosa kai sannan ya furta.

"Dama ciwon ciki take yi Mami, sai ciwon ƙirji da yawan amai. To kuma yau sai muka tashi numfashinta na ɗaukewa." Salim ya sake sunne kai ƙasa yana shafa kai ya ce, "Likita kuma ya ce tana da juna biyu." Washe baki Mami ta yi ta furta. "Kai AlhamduLillah, na yi farincikin wannan labarin. Allah Ya raba lafiya "

Mami zama ta yi sai bayan wani lokacin Shukra ta farka, aka haÉ—a mata ruwan shayi. KaÉ—an ta sha saboda tashin zuciyar da take fama da shi, duk da a haka ma an yi mata allurar tsayar da amai. Ganin yanayin jikin Shukra ya yi kyau ya sa aka sallame ta, sai dai a nan take Mami ta kira Auta ta ce mata ta ba wa Uwani waya, saboda ita ko lambar Uwani babu a wayarta.
Lokacin da Uwani ta karɓi wayar Mami ta ji ta furta. "Maza ki haɗi kayan sakawarki da uniform ɗin ki, Auta za ta rako ki gidan Shukra ba ta jin daɗi za ki dinga tayata aiki."

Da yake har Aunty na zaune Mami ta faɗi haka, saroro Uwani ta yi. Yanayinta kawai Aunty ta kalla ta miƙa hannu ta karɓa ta ce. "Aunty Saratu ashe Shukra ce ba ta ji daɗi ba a wane asibitin kuke?" Mami ta saki guntun tsaki ta ce, "Da sauki." Aunty na shirin sake magana Mami ta katse kiran. Uwani ba don ta so ba Aunty ta sa ta haɗa kayanta, don ba ta son abin zai dinga haɗo ta Mami ballantana watarana ta yi mata sharri. Auta ma ta saka kayanta a jaka kamar yadda Uwani ta sa duk da Mami ba ta ce ita ma ta haɗa ba. Suka yi wa Aunty Sallama suka wuce can gidan Shukra.

Lokacin da su Uwani suka ƙarasa gidan Shukra su Mami ba su jima da ƙarasawa ba, Shukra an yi ɗaiɗai sai juya idanu ake lokaci-lokaci ta tashi ta zubar da yawu. Su Uwani na shiga Mami ta shiga aikawa da Auta harara, ita kuma ta kawar da kanta kamar ba ta san abin da Mami take nufi. Saboda Salim yana wurin ya sa Mami ba ta yi magana ba, da mamaki Salim yake bin Uwani yana ganin kamar ya taɓa sanin fuskarta. Bayan da Salim ya fita ne Mami ta dubi Auta ta ce,
"Ki taso mu wuce gida, kin san ba a garin gaɓa-gaɓa muke ba da za ku zo har ku biyu ku zaune mata a gida." Auta na shirin magana Mami ta buga mata tsawa babu musu Auta ta ɗauki jaka, suka fice ko sallama ba ta yi wa Shukra ba. Mami har ta yi wa Shukra sallama ta waiga wurin Uwani ta ce.

"Kin ga dai halin da take ciki, ki tabbatar kina yi mata duk wani abin da ya dace. Idan ba haka ba ranki ne zai ɓaci, saura kuma ki dinga saka mata ido da waɗannan ƙwala-ƙwalan idanun na ki idan tana hira da mijinta." Uwani ta amsawa Mami sannan ta yi gaba.

A hankali Uwani ke bin falon Shukra da kallo tun da dama ba ta taɓa zuwa gidan ba.

"Wannan kalle-kallen ba zai ƙare miki ba tun da abin kallon yana da yawa a gidan nan, da alama babu a ɗakin gyatuma ne? Ki tashi ki je ɗakina akwai kayan da na ɓata ɗazu kafin mu je asibiti ki wanke su." Ƙurr Uwani ta yi tana kallon Shukra, sai da ta haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ta furta.
Chapter 40 · 0% Book details