← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 71

Sashe 39

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Don Allah kira mini Dada mu yi bankwana da ita."
"Bankwana wane iri?"
Uwani ta cusa kanta a cikin cinyoyinta ta sake rushewa da kuka, Jafar tashi ya yi ya leƙe banɗakin ya gama haske-haske da dube-dubensa bai ga komai ba. Yana nan zaune Uwani ta miƙe ta furta. "Tun da ba za ka kira mini ita ba bari na je Aunty Zainab ta kira mini ita, tun da dai dama kai ne za ka yi sanadiyyar mutuwata." Kan Jafar ya sake ɗaurewa Uwani za ta fita ya yi saurin dawo da ita, wayarsa ya ɗauko ya latsa lambar Dada ko uffan bai ce ba ya miƙa wa Uwani. Daga can ɓangaren Dada ta furta.

"Waye haka ya kira ni da farar safiya? Ni dai na san Mamman ba ya yi mini wannan kiran ballantana ya tashe ni daga bacci, wai Jafaru bashi na ci ban biya ka..." Jin kukan Uwani ya katse maganar Dada, da sauri ta ce.
"Wa nake ji yana kuka kamar Uwani, ina ce dai Mamman da iyalansa duk lafiya ƙalau suke ko?" Uwani ta tsagaita da kukan ta ce.
"Ni dai ki yafe ni Dada, wallahi mantawa na yi shaf da gargaÉ—inki har na ba wa Ya Jafar fuska yanzu ga shi alamun mutuwa sun bayyanar mini yau da safe." Uwani na gama magana ta rushe da kuka.
Dada ta yi jim sannan ta ce, "Ke Uwani ita mutuwar ce ta nuna miki alamu kamar ta haɗa iri da Umaru?" Uwani ta ja majina ta ce, "Wallahi da gaske nake miki mutuwa zan yi Dada, tun ɗazu alamomin mutuwar suke ƙara bayyanar mini." Dada da sauri ta ce.

"Maza miƙa wa Jafaru wayar." Ba musu ta miƙa masa wayar Dada ta tambaye shi, shi kansa iya abin da ya sani ya sanar da ita, Dada ta ce maza ya kaita wurin Abuwa ƙila ta faɗa mata abin ke damunta. Sai da Dada ta katse Uwani ta tashi ta sake faɗa wa banɗaki, bayan ta fito ta je kan kujera ta sake rushewa da kuka. Jafar Ya yi mata magana suka nufi sashen Aunty a lokacin Mami na ɗakinta, a falo Jafar ya zauna jikinsa a sanyaye don kalaman Uwani ba ƙaramin faɗar masa da gaba suka yi ba.

Sai da suka gaisa ta ga Uwani fuska a kumbure, Jafar ya zayyane mata komai. Aunty ta sake tambayar Uwani, sai da Uwani ta sake goge ƙwallah a lokacin fitowar Daddy kenan ta fara magana.

"Wallahi tun da na zo duniya ban taɓa tunanin Ya Jafar riƙaƙƙen ɗan iska ba ne sai yau!" Rass! Ƙirjin Jafar ya buga, a hankali Jafar ya saci kallon Daddy. Ita kuwa Uwani ta ci gaba.
"Dama da daɗewa Dada ta ce mini ba a ba wa maza fuska wallahi tsautsayi ya sa nake kula Ya Jafar, to ni dai ga abin da Dada ta faɗa ya zo kaina dama ta ce duk mace mai kula maza 'yar iska take zama, kuma alamun mutuwa na bayyana a jikinta shi kenan a ranar za ta mutu." Kuka ya ci ƙarfin Uwani, Daddy na shirin yin magana Uwani ta share hawaye ta ci gaba da cewa.

"Tun da garin Allah ya waye nake fitsarin jini, kuma dama Dada ta ce wannan ne alamun mutuwa na farko jinina yana ƙarewa shi kenan sai dai a ɗauki mushena a kai daji a wurgar kura ta cinye." Uwani na zuwa nan a maganarta ta sake fashewa da kuka, cikin kuka ta furta. "Ni dai Ya Jafar ya cuce ni ya cuci rayuwata shi kenan Dada ba za ta ga 'ya'yana ba, wayyo Allah mutuwa za ta ɗauke Uwani." Tun da Uwani ta fara magana da Daddy ya fahimci inda zancen ta ya dosa yake murmushi don ba ƙaramin dariya ta ba shi ba, kuma wannan ya sake tabbatar masa da irin zaman da suke yi ita da Jafar. Kallon Aunty zainab ya yi da ke riƙe da baki ya furta.

"Auntyn yara ga 'yarki nan ki ji da ita, kai Jafar ta so mu je." Tamkar kazar da aka tsamo daga ruwa haka Jafar ya miƙe yana sunne kai ƙasa, don da ya san abin kunyar da Uwani za ta yi kenan da ko harabar gidan ba zai biyo ta ba. Suna fita Aunty Zainab ta ja Uwani ɗaki ta furta, "Uwani wallahi yau na sake tabbatar da har yau da sauranki, gaskiya riƙon kaka daban yake. Amma hakan ma da Dada ta yi miki duk cikin tarbiyya ne." Nan da nan Aunty Zainab ta yi wa Uwani duk bayanin da ya dace, da yadda za ta gyara jikinta. Sai bayan da Uwani ta gama sauraronta ta ce.

"Wai Aunty dama wannan shi ne duk bayanin da Malam Gali yake yi mana a Ahalari?" Aunty Zainab ta gyaÉ—a mata kai.

Ko da Uwani ta koma sashenta ganin babu fuska a wurin Jafar ya sa ta taɓe baki ita ma ta fara ɗaure fuska, don gudun kada ya rainata. A haka dai rayuwarasu ta ci gaba babu yabo babu fallasa, kwanan Jafar bakwai a Kano su Daddy suka je gidan yayan mahaifin Safna da ke Unguwar sallari suka kai kuɗin auren Jafar da ita. Farinciki wurin Mami ya ƙi musaltuwa don hatta Daddy ya lura da yanayin da take ciki, a ɓangare Jafar da Safna kuwa bakinsu ne ya ƙi rufuwa. Uwani ta yi mamakin sauyin da ta gani a wurin Jafar, duk da bai ce mata uffan ba amma ta fahimci yana cikin farinciki. A ranar da magriba Uwani ta je wurin Aunty Zainab don shi ma Jafar yana wurin Mami, Aunty ta lura da yanayin Uwani da alama ba ta san abin da yake faruwa ba don haka ta same ta tana faɗin.

"Uwani ina son ki buÉ—e kunnenki da kyau ki saurare ni, kuma duk abin da za ki ji ba na son sakarci ko shashanci." Uwani ta gyaÉ—a kai gabanta na faÉ—uwa.

"Ɗazu Daddynku yake ce mini shi da su Yaya Inusa sun kai kuɗin auren Jafar da Safna." Dam! Ƙirjin Uwani ya buga, Aunty Zainab ta lura da yanayin da ta shiga ta ci gaba da cewa.

"Don haka ina son kin kwantar da hankalinki hakan ba yana nufin mijinki ba ya ƙaunarki ba, shi ya sa a kullin nake son ki ajiye wannan sakarcin na ki a gefe ki kama mijinki ta yadda ko wata ta zo ba za ta nuna miki komai ba, Jafar namiji ne kuma mijin mace huɗu ko bayan ya auri Safna yana da damar auro wasu matan biyu. Ba a tsayar da lokacin auren ba tun da na ji Daddynku ya ce za ta je ƙaro karatu India, za ta yi shekara ɗaya da rabi zuwa biyu sai ta dawo za a yi bikin." Hawaye bibbiyu ne suke bin fuskar Uwani saboda wani irin ɗaci da take ji a ranta, amma da za a tambaye ta ita kanta ba ta san dalili ba.

"Ni fa ban zaunar da ke domin ki yi mini kuka ba, ke ma fa mace ce Uwani. Shawara É—aya zan ba ki da ki jajirce wurin neman ilimi tun da kin ga abokiyar zamanki ba ta zauna ba, ko kina son ki zama koma baya ne?" Uwani ta girgiza kai tana share hawaye, ta dubi Aunty Zainab ta ce.

"Amma Aunty bai gaya mini ba fa! Abin da ya ba ni haushi kenan." Uwani ta faɗa tana ƙoƙarin kare kanta, don ba ta son a fahimci saboda zai yi auren ne take kuka. Aunty Zainab ta jima ta yi wa Uwani nasiha sosai sannan ta ɗan fara jinta da hira, saboda ta kawar mata da damuwar da ta ga tana ciki. Uwani ko da ta koma ɓangarenta ba ta nuna wa Jafar ta san da maganar ba, shi ma kuma bai sanar da ita ba. A haka har ya ƙare kwanakin hutunsa, da zai koma ne Daddy ya sa shi ya saya wa Uwani waya don su dinga magana da ita.

Sannu a hankali rayuwa ta ci gaba da tafiya, Uwani ta watsar da koma ta kama karatunta sai kuma kiwon awakinta da take yi. Abin da ya fara damunta bai wuce sabon al'amarin da ya fara ɓullowa a cikin kejin awakinta ba, ranar wata talata ta dawo daga makaranta kafin ta shiga sashenta ta leƙa kejin su Lawan da kuma awakinta. A wajen kejin ta hangi wata baƙar kazarta da take yin ƙwai a sheme a ƙasa an yanka ta, tana shirin shiga sashen su Mami Lado ya ƙarasa ya furta.

"Barka da shigowa Uwani, dama na ji shigowarki ina banɗaki. Ɗazu Hajiya ta kira ni ta ce a yanka kazar nan saboda wannan 'yar baƙar za ta kasa, ga ta nan da alama tana da albarka amma lokaci ya yi." Saboda takaici Uwani ba ta tanka masa ba ta yi sashen Mami, tana tambayarta. Abin da Lado ya faɗa mata shi ta maimaita mata, haka ne ya dinga faruwa sai Uwani ba ta nan ko tana cikin sashenta sai a kira ta a ce ga kaza ko zakara can an danne za a yanka saboda sun kasa. Da Uwani ta nuna ba ta son a dinga yanka mata, sai kuma ta koma ganin gawar kaza ko zakara a cikin kejin, a wannan lokacin hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba saboda kajinta da suka ɗauko hanyar ƙarewa. Aunty ce ta ci gaba da tausarta tana ce wa ta ci gaba da addu'a tana faɗa wa Allah kukanta, tun da idan ba ka iya kama ɓarawo ba sai shi ya kama ka. Saboda har kawo lokacin ba a san musababbin mutuwar kajin ba.

Shi kuma Lado abin da ya sa yake bin dare yana É—aukar kaza ko zakara yana ba su guba bai wuce 'yan kuÉ—aÉ—en da Mami take ba shi ba, shi ya sa Uwani ta yi masa tambayar duniya ya nuna mata shi taimakonta dama yake yi da yake yankawa kafin su mutu amma tun da ba ta so shi kenan.
Chapter 39 · 0% Book details