Sashe 68
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Jidda wai kunyata kike ji? Ina duk missing É—in da ake cewa an yi ko duk faÉ—a ne?" Murmushi Uwani ta yi ta ce.
"Da gaske ne mana!"
"Ni ban ga alama ba, tun da dama kin bar ni haka kamar maraya." Jafar ya yi maganar da alamar tausayi, ba ƙaramin dariya ya ba ta ba. A hankali ya fara aika mata sakwanni, a kunyace Uwani take mayar masa da martani. Ganin Jafar na neman mayar da lamarin babba ya sa ta ɗan janye jikinta tana faɗin.
"Ya Jafar mu je mu ci abinci ko?"
Idonsa a lumshe ya furta, "Da fatan dai kin sallami little Papa don kada ya hana ni rawar gaban hantsi. Don gaskiya yau dole ya ɗaga miki ƙafa ki ji da Papa." Jafar ya kashe mata ido bayan ya ɗago.
Rufe baki Uwani ta yi tana dariya ta ce.
"Wallahi Ya Jafar nema kake ka fi ƙarfina, ni kam yaushe idonka ya sake buɗewa haka."
"Wallahi duk yadda na zama ke ce sila, haka kawai aka ɗauko ni aka damƙa miki amana ina salihina, amma ƙiri-ƙiri kina neman lalata ustazun Daddy." Uwani ta zaro ido waje cikin wasa tana dariya ta ce.
"Ai shi ya sa na ga tashin farko ka bugo Hibban ko? Allah Ya shiryaka Ya Jafar." Fita suka yi falo Uwani ta haɗa musu tea suna cin abinci cikin kulawa da tsantsar soyayya. Suna nan zaune ta miƙa ta buɗe frige ta ɗauko wata jarka da Aunty ta ba ta, ta shanye gabaɗaya kamar yadda Aunty ta faɗa mata, komawa ta yi har za ta zauna ta sake jin motsin Hibban. Gyara masa kwanciya ta yi sannan ta dawo suka ci gaba da cin abinci.
Bayan sun gama cin abinci wanka Uwani ta tsala ta feshe jikinta da turarruruka masu ƙamshi, lokacin da Jafar ya fito daga wanka tana gaban mirror. Ta baya ya riƙo ta a hankali ya fara yi mata raɗa a kunne, da sauri Uwani ta ɗago tana zaro ido cikin wasa jin irin kalaman da yake furta mata tamkar ba Jafar ɗinta. Dariya suka saki lokaci ɗaya, ya ja hannunta suka wuce makwancinsu. Mabambamtan saƙwanni Jafar ya shiga aika mata, a wannan karon Uwani ta fitar da kunyarta ta nuna wa mai gidanta tsantsar kulawa da irin kewar da ta yi masa. Hakan ne ya sake birkita Jafar yana ci gaba da nuna mata soyayya, Uwani ta ji daɗi sosai da ta sake fahimtar yadda mijinta yake so da ƙaunarta. Ta shiga narkewa tana shagwaɓe masa shi kuma sai riritata yake yi, daren ranar haka ya zo musu da farinciki musamman Jafar da yake jin wannan daren ya zame masa ɗaya tamkar da dubu.
A ranar da Uwani ta koma gidanta bayan da Daddy ya koma gida, suna zauna shi da Aunty suna hira yake sanar da ita a washegari Mami za ta dawo. Aunty ta ji daÉ—i sosai don haka ta shiga yi musu addu'a da fatan zaman lafiya mai É—orewa. A take ya kira Mami ya ce mata ta shirya zai zo a gobe ya tafi da ita, saboda farinciki ranar ko baccin kirki Mami ba ta yi ba.
Kamar yadda ya faɗa a washegari bayan ya sauke Dada a gida ya wuce ya ɗauko Mami, sai sakin murmushi take yi ga wani irin nauyin Daddy da take ji. Ko da suka koma gida Aunty ta gama girki, duka suka baje a ɗakin Daddy suna cin abinci suna hira. Bayan an gama hira Aunty ta miƙe za ta yi musu sai da safe, Mami ta yi murmushi ta ce.
"Amma Auntyn yara tun yanzu kya tafi muna hira."
"A'a Mamin yara faɗi dai gaskiya, ina zan zauna na hana amare sakat kina ga Daddyn yara tun ɗazu sai satar kallonki yake. Ai gara dai na ba ku wuri tun Ango bai sallame ni ba."Aunty ta ƙarasa maganar cikin dariyar shakiyanci.
"Sharrin da za ki yi mana kenan?" Daddy ya furta yana murmushi."
"Ina fa sharri duba fa Daddy ka ga yadda ka kanainaye Mami, wallahi kada idanuna su ƙone bari na yi gaba." Aunty ta yi maganar tana nufar hanyar fita tana dariya.
"Wallahi ina nan zan rama Auntyn yara." Mami ta faÉ—a, da sauri Aunty ta dawo ta ce.
"Yawwa na manta Daddy na baka sati biyu cif ka gama cin amarcinka a toh kada ka dawo ɓanagrena kana leƙen sarautar mata kana haɗiyar yawu." Ganin Daddy ya taso da sauri ya nufo wurin Aunty ya sa ta fita da gudu tana dariya. Tura ƙofar Daddy ya yi ya koma kusa da Mami ya janyota jikinsa.
"Kwana da kwanaki na yi kewarki." Daddy ya raÉ—a mata a kunne, Mami ta zuba masa ido tana kallo. Tsohuwar soyayyar shekara sama da talatin da takwas da dawo mata.
"Tabbas samun nagartacce kuma ingarman miji kamar kai ba duk maza ba, shi ya sa nake tsananin so da kishinka. Amma na tabbata addu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza tun da ta saita zazzafan baƙin kishin da nake da shi a kanka." Mami ta raya a ranta. Ganin ta yi shiru ya sa Daddy ya hura mata iska a fuska. A shagwaɓe Mami ta ce.
"Bayan yanzu ka daina sona?"
Zaro ido waje Daddy ya yi ya ce, "Wa ya gaya miki, ai ba a ƙin mutum sai dai a ƙi halinsa. Ballatana na rasa wa zan daina so sai Saratuna? Ke ce sarauniyar mata domin soyayyar da nake yi miki ta dabance, ba za ki gane ba amma wallahi na yi matuƙar kewarki a zuciyata." Mami ta ji daɗi sosai da yadda Daddy ya nuna mata kulawa, don haka ita ma ta shiga furta masa kalamai masu tausasa zuciya.
Su Jafar ba ƙaramin farincikin dawowar Mami suka ji ba, Mami ta kwantar da kanta suna zama lafiya da Aunty sosai. Haka ita ma Madina ganin mahaifiyarta ta watsar da makamanta ita ma ta sauke take ba wa Aunty girmanta, sai dai shaƙuwar da suka yi ba kamar Auta ba.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har Hibban ya kai wata shida, a lokacin ya yi wayo sosai kamanninsa da na mahaifinsa sun sake fitowa.
Watarana da daddare Uwani na kwance a cinyar Jafar suna hira ta tashi zaune cikin kulawa ta furta.
"Don Allah Ya Jafar ka dawo da Aunty Safna." Lokaci ɗaya ya haɗe fuska, a daƙile ya ce.
"Kin daina ƙaunata kenan?" Girgiza masa kai ta yi tana jin zuciyarta na bugawa, don idan ta ce ba ta jin kishinsa ta yi ƙarya.
"Na san kina son Jafar kuma kina kishinsa, amma hakan ba zai hana na ba ki shawarar da ta dace ba. Uwani ki samu mijinki ki ba shi shawara ya dawo da matarsa, domin matuƙar kika yi haka wallahi kin gama zama da kowacce irin kishiya ce ba ma Safna ba. Na farko shi kansa mijin sai ya jinjina miki da wannan namijin ƙoƙarin da kika yi, sannan kuma ko ba a gabanki ba na tabbata idan ya dawo da ita sai ya faɗa wa matarsa ke ma kin taka muhimmiyar rawa wurin dawowarta cikin gidan, don haka duk abin da take taƙama da shi za ta sauke. Ki danne kishinki ki nusar da mijinki don wallahi a yanzu na tabbata yarinyar nan ta gama gane kuskurenta. Saboda ba na son a dinga yawo da tambarinki, ana cewa saboda ke mijinki ya saki matarsa duk da abin da ta yi ba na hankali ba ne."
Uwani ta tuno nasihar da mahaifiyarta ta yi mata a ranar da ta je gaishe ta, numfasawa ta yi ta furta.
"Ba haka ba ne Nur, Aunty Safna ta yi laifi. Amma tun da ka ga mahaifanta da ita kanta sun sauke komai, sun zo har gidanku sun ba da haƙuri na tabbata ta gane kuskurenta. Allah ma fa muna yi masa laifi..."
ÆŠaga mata hannu ya yi fuska a haÉ—e ya furta.
"Dakata! Daga yau ba na buƙatar jin wannan maganar a bakinki, idan kuma ba haka ba ranki zai ɓaci." Shiru Uwani ta yi, ita kanta ba yin kanta ba ne don dai kawai Innarta ta shawarce ta ne. Shi kansa Jafar a wannan lokacin lumshe ido ya yi, yana jin wani abu na fisgarsa akan Safna. Idan har ya ce ba ya ƙaunarta ko babu ɓurɓushin soyayyarta a ransa to tabbas ya yi ƙarya.
Safna ta sauya kamar ba ita ba, ba ta da aiki sai zaman ɗaki. Ta rame ta yi duhu sosai, silar haka ne lokaci ɗaya ta wayi gari da ciwon zuciya. Kusan asibiti uku suka kwanta kuma kowanne da ciwo ya ɗauko warkewa sai ya dawo baya, wannan lamarin ya ƙara ɗaga hankalin mahaifanta. Mahaifiyarta na zaune a gefenta ta ɗago da murya a can ciki ta ce.
"Mummy don Allah ki kira mini Jafar, domin a yanzu na yanke ƙauna da sake zama da shi. Ina son ganinsa ko da sau ɗaya ne kafin numfashi ya bar gangar jikina." Hawaye ne ya zubo mata, ta yi wani tarin mai haɗe da kakin jini. Mummynta ce ta taimaka mata ta kwanta tana share ƙwalla, sannan Safna ta ci gaba da cewa.
"Don Allah ki ce Jafar ya zo mu yi bankwana da shi." Wayarta Mummynta ta ɗauko ta neman lambar Jafar a sanyaye don ko ta kira ba ya ɗagawa. Kamar almara a wannan lokacin ta ji ya ɗauka, muryar Mummy har rawa take suka gaisa. A nan ta zayyana masa halin da Safna ke ciki da asibitin da take kwance. Duk maganar da suke yi Uwani na zaune a gefe, yana shirin magana da sauri Uwani ta karɓi wayar ta yi sallama. Ƙirjin Mummyn Safna sai da ya buga don ta yi tsammanin rashin mutumci Uwani za ta yi mata. Sai da suka gaisa, sannan Uwani ta nemi address ɗin asibitin ta ce za su zo duba Safna.
Bayan sun gama wayar da kanta ta matsa wa Jafar ya shirya ba don ya so ba, kai tsaye asibitin suka nufa. Suna zuwa bakin gate Mummyn Safna ta fito ta shiga da su ciki.