← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 71

Sashe 71

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kamar yadda Safna ta saba, Uwani da Jafar suna kwance wayar Jafar ta fara ringing. A hankali Jafar ya janye hannunsa daga jikin Uwani, sai da ya ja blanket ya rufe jikinsa sannan ya ɗauki wayar. Takaici goma da ashirin ya lulluɓe Uwani, saboda ɓacin rai miƙewa ta yi ta janye blanket ɗin jikinta. Towel ta ɗaura sannan ta faɗa toilet ta tsarkake jikinta, doguwar rigarta ta saka ta koma kan stool ta zauna tana sauraron Safna da ke faɗin.

"Baby wallahi tsoro nake ji sai na ji kamar ana tafiya, ga shi yanzu haka cikina wani irin ciwo yake yi." Safna ta ƙarasa maganar tana shasshekar kukan ƙarya. Jin haka ne ya sake rikita Jafar a gaggauce ya ce.
"Gani nan zuwa bari na zo."

Kashe wayar ya yi ya faɗa toilet sai da ya yi wanka sannan ya zura jallabiyya yana shirin fita Uwani ta miƙe ta ce.
"Bari na raka ka Ya Jafar don ni ma fa da rana sau biyu na ga ana giftawa, ko kuma na ji ana kiran sunana. Gaskiya ina zargin gidan nan akwai motsi a cikinsa." Tare suka fita Jafar sai zuba sauri yake, suna gab da fita saga sashenta Uwani ta dafe kai tana faÉ—in.

"Wash kaina ya sara mini Ya Jafar, kamar an buga mini guduma." Riƙo ta ya yi yana mata sannu, za ta yi kusan sakan ashirin dafe da kai sannan ta ɗago suka ci gaba da tafiya.

Uwani kallon Jafar ta yi sai kawai ta zaro masa ido haɗe da kyalkyalewa da dariya. Mamaki ne ya kama Jafar ganin abin da Uwani take yi, cikin ƙarfin hali ya basar kamar bai ganta ba. Suna gab da shiga sashen Safna Uwani ta cafko hannu Jafar tana ƙyaƙyata dariya ta ce.

"Matar Tummo."
Da sauri Jafar ya waiga suna haÉ—a ido da Uwani ta gwalo masa idanu tana ta sake cewa.
"Matar Tummo" Jikin Jafar ne ya fara rawa, a hankali ya fara son ƙwace hannunsa Uwani ta riƙe shi ƙam. A ransa yana maimata sunan matar Tummo.

A haka suka ƙarasa sashen Safna, Safna a tunaninta Jafar ne don haka tana zaune daga ita sai wani ɗan matsattsan three quater wando. Ganin Uwani ya sa ta yi turus tana haɗe fuska, Jafar na shirin tambayar Safna jikin nata suka ga Uwani ta buga wata uwar sufa ta nufi kan dianning ɗin Safna, da sauri ta fisgo gwangwanin madara ta cire murfin ta ɗaga kai tana zazzaga garin madarar a bakinta har zuwa fuskarta. Sai kuma ta waigo wurin Jafar ta wani zare ido ta ce.

"Yar bugus uwar 'yan iskan aljanun zamani zo kin ga mijinki can wanda ya koma ɗan shafi mu lera." Uwani ta gama maganar tana yin wurin su Jafar da gudu, a guje Jafar da Safna suka matsa Uwani ta gimtse dariyarta ta maƙale murya ta ce.

"Ki bar Ɗan Tummo wallahi zan biyo shi sai na mayar da bakinsa ƙeya."
"Jidda lafiya mai yake faruwa?" Jafar ya faɗa yana daga ƙarƙashin dianing. Watso masa manyan idaunta ta yi ta ce.

"Kai ne mijin Yar bugus da ka ɓata wa 'Yar autar mai martaba rai." A razane Jafar ya ce. "Waye 'yar bugus da mijinta kuma? Ni kamar yaya?"

Uwani ta fakaici Safna ta buga wata uwar sufa ta fusgo gajeren wandonta, nan take silla-sillan siraran mazaunan Safna masu kama da sandar ba'are suka bayyana, Uwani da Safna suka hau kiciniya kowacce tana fusgar gajeren wandon. Cikin tashin hankali Safna ta fasa ihu tana faÉ—in.

"Baby ka taimaka mini don Allah, wallahi za ta yi mini tumɓur."

Jafar da ya ja kwanuka ya sake rufe kansa da su plates ya ce. "Wallahi ba zan iya ba lamarin nan ya fi ƙarfina Dear."

"Ba dai so kike ki hana 'yar autar mai martaba jin daɗin zaman aure ita da mijinta ba? Wallahi kema sai mun haɗa ki da mijin 'Yar bugus ya shafe miki hallitun jikinki sai mu ga ta faɗin makirci." Uwani ta faɗa tana zuba wa Safna duka a cinya da mazaunanta. Hawaye shaɓe-shaɓe a fuskar Safna ta ce.

"Don Allah ku yi mini rai kada ku shafe mini hallituna." Uwani ba ta bi ta kan Safna ba ta waiga wurin Jafar da ke ta haÉ—a gumi ta gwalo masa ido waje tana zaro harshe ta ce.
"Kai ma so kake ka zama marar adalci ko? Wannan munafukar matar taka babu abin da yake damunta amma kullin sai ta yi ƙaryar ana tsoratata ko ba ta lafiya da dare. Wallahi kai ma babu abin da zai hana ba mu shafe hallitunka ba, ko kuma a yanzu mu mayar maka da hallitar matarka jikinka ita kuma mu mayar mata da naka. Kai idan har muka ji daga bakin 'Yar auta ko mata-maza take so tsaf za mu mayar da kai." Hankalin Jafar ba ƙaramin tashi ya yi ba, musamman da ya tuna abin da ya faru da Lado a kan awakin Uwani. Da sauri Jafar ya kai hannu ya fara shafa ƙirjinsa sai da ya ji shi a daidai yake, sannan ya sauke ajiyar zuciya ya ce.

"Don Allah ku faÉ—i abin da kuke so idan laifi ne muka yi muku ba za mu kuma ba."

"Mu ba za mu faɗa ba sai dai matarka ta faɗa da bakinta, ke munafuka ki faɗa da bakinki shin mu jinsin Aljanu mun taɓa tsorata ki, ko kuma akwai wani ciwo da yake damunki ban da makirci irin naku na mata?" Safna ta share ƙwalla jiki na rawa ta shiga wassafa duk irin ƙarairayin da take yi, sannan ta ɗora da cewa.
"Don Allah ku gafarce ni wallahi ba laifina ba ne har da zugar ƙawaye, sune suka ɗora ni a wannan turbar." Daga Jafar har Safna ban da haƙuri babu abin da suke ba wa Uwani, Uwani ta ɗauke kai gefe tana gimtse dariyarta ta ce.

"Wallahi kun ci sa'a 'Yar autar Mai martaba na da sauƙin kai, kuma Ɗan Tummo sabon ɗan shafi mu leran cikin jinsinmu ba ya nan, za mu ɗaga ƙafa domin mu gani idan da gaske kike kin yi nadama. Kai ma kuma za mu ci gaba da bibiyarka, idan ka sake yin rashin adalci wallahi sai mun shafe hallitarka ta koma kamar bayan babe." Uwani na gama faɗar haka ta saki jiki ta faɗi ƙasa yaraf, irin faɗuwar da ta yi duk wanda yake wurin ba zai taɓa tsammanin aljanun ƙarya ta yi ba. Ita kanta ta bugu sosai, amma ganin yadda daga Jafar har Safna suka tsorata ta san ba za su sake yi mata iskancin da suke yi mata ba. Atishawar ƙarya Uwani ta fara jerawa, a daidai lokacin Jafar ya ƙarasa ya taimaka mata, sai dai har lokacin ta lura a tsorace yake.

"Ya Jafar mene ne wannan kamar madara a jikina?" Uwani ta tambaya kamar ba ta san komai ba.

"Ni na zo ɗauko madara zan haɗa wa Safna tea madarar ta ɓare ta zubo miki a jiki. Ta so maza mu koma sashenki ai jikin nata da sauƙi ta samu lafiya." Uwani ta saci kallon gefen wurin da Safna ke zauna, ta ga ta yi zumu-zumu ta saki murmushi a fakaice cikin ranta Uwani ta furta.
"'Yar iskar ƙarya da ni za ku dinga yi wa iya shege, Allah ya taimake ku ba bulala na sa na zane ku ba."
Tun da Uwani ta yi wa Safna haka shi kenan ta samu 'yanci ranar kwananta, a ɓangare ɗaya kuma shakkar Uwani ta mamaye ta. Daga ƙarshe ma sai Safna ta watsar da komai, suka cigaba da zama lafiya da kwanciyar hankali.

Tammat Bi HamduLillah

A nan labarin UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA ya zo ƙarshe. Kuskuren da yake ciki Allah Ya yafe mana, darussan da ke ciki Ubangiji ya ba mu ikon ɗauka.
A kullum ina faɗa muku ni ma 'Yar adam ce tara nake ban cika goma ba, idan an ga kuskure a yafe mini. Kuma ina fatan Ubangiji Ya yafe mana bakiɗaya.👏🏻
Mu tara a cikin ci gaban littafin SHU'UMAR MASARAUTA 2 ku kuma haɗo da addu'ar Allah ya sa na juri typing ɗinsa😂 ga dai labarin da komai na gama tsarawa sai dai typing ɗinsa kamar an saka mini hannu.

Ina yi muku fatan alheri da godiya musamman waɗanda suka fitar da kuɗinsu suka sayi littafina, Allah Ya saka da alheri Ubangiji Ya bar zumunci. Idan akwai ƙorafi a game da labarin Uwani ina sauraro, kuma a shirye nake na bada amsoshin a kan kowacce tambaya.

Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624 Littafi ya kammala cmplt doc 800 ne.

#Ummou Aslam Bint Adam🌚
Chapter 71 · 0% Book details