Sashe 70
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ranar Juma'a bayan sallar Juma'a ne aka mayar da auren Safna da Jafar a masallacin Juma'a na Rjiyar Zaki, mahaifin Safna ban da godiya babu abin da yake yi wa Daddy. Ita kanta Mami ta sauko don da farko cewa ta yi ba ta lamince Jafar ya dawo da Safna ba, sai da Daddy ya yi mata nasiha sannan ta amince. Uwani ta dage sosai da sallar dare tana addu'ar Allah ya yaye mata zafin kishin da take da shi, don ta san abu ne da sai ta kai zuciya nesa kafin ta saba da shi.
Cikin abin da bai fi sati uku ba tuni Safna ta warke garau, jikinta har ya fara dawowa duk da dama can ita ba mai jiki ba ce. Kuma saboda yanayin rashin ƙwarin jikinta Daddynta ya ce sai bayan ta warware za ta tare. Jafar kusan kullin sai ya leƙa gidansu Safna ya duba jikinta, duk taku da sauyin Jafar Uwani na lura da shi sai dai ko a fuska ba ta taɓa nuna masa komai ba.
A satin da Safna za ta koma ne aka yi mata gyare-gyare a ɓangarenta, ita ma Uwani Jafar ya sauya mata abin da yake da hali har da ɓangaren suturu duk da tana da wadatattu.
"Uwar biyu wallahi duk wata addu'a da na sani babu wacce ba na yi amma har gobe babu abin da ya ragu a zuciyata. Ina son Ya Jafar ina matuƙar kishinsa, ban san son shi ya kai haka a zuciyata ba sai da na ji tariyar Aunty Safna." Uwani ta ƙarasa maganar ƙwalla na zuba. Auta da ke zaune da tsohon ciki ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Tun farko ke ce ba ki yi shawara da ni ba, matar da ta so halaka ki ita ce kike son a kwaso a dawo miki da ita kusa da ke. Yanzu dai tun da aikin gama ya gama shi kenan, addu'ar dai za ki ci gaba, ina da wasu addu'o'in zan turo miki ta Whatsapp In Shaa Allah."
"Idan ma ban ba shi shawarar dawo da ita ba Auta ban san nan gaba wacce Ya Jafar zai kawo mini ba, domin duk son da namiji yake yi maka É—ari bisa É—ari ba za ka ce da kai kaÉ—ai zai zauna a rayuwar duniya ba. Kuma ko ke shaida ce Safna da iyayenta sun matuar gane kuskurensu." Uwani ta furta a sanyaye. Auta ta jinjina kai, sannan ta cigaba da kwantar wa da Uwani hankali har ta ji damuwar da ke ranta ta yaye.
Bayan sallar Isha'i suna zaune suka ji motoci na shigowa, Auta ta dafa Uwani da idanunta suka ciko da ƙwalla ta ce.
"Don Allah kada ki ba ni kunya." Jinjina kai Uwani ta yi ta haɗiyi yawu mai ɗaci. Suna nan zaune suka ji an nufo sashenta, wasu dattawa biyu ne riƙe da Safna. Cikin karamci su Uwani suka karɓe su bayan sun gaisa suka wuce da Safna sashenta. Sai da duka mutanen da suka rako Safna suka watse sannan Jafar ya shigo gidan, kai tsaye sashen Uwani ya wuce Auta na ganinsa ta ce.
"Ya Jafar wai ina ka maƙale tun ɗazu fa Dr ke jirana."
"Ai mun gaisa da shi a bakin gate, zo ki wuce ku tafi gida." Jafar ya furta yana zama a kusa da Uwani. Da ƙyar Auta ta yunƙura ta miƙe, sai da ta yafa mayafi sannan ya ɗauki jakarta ta ja hannun Uwani suka wuce uwar ɗaki.
"Ke fa dama munafuka ce me za ki kitsa wa matata?" Jafar ya faÉ—a ganin sun shige É—aki.
"Ya Jafar saƙo za ta ɗauko mini." Auta ta faɗa tana turo ƙofar.
"Maman Hibban don Allah yanda kika yi jarumta ki ci gaba, trust me za ki ce na faɗa miki a nan gaba za ki yi alfahari da wannan ƙoƙarin naki. Ki fa tsare gida kin san ke ce babba kar ki sake ki yarda girmanki, kuma ko da wasa kar ki ɗauki raini, atoh don wallahi duk a yadda ta zo miki ku tafi a haka na san ki sarai 'Yar ƙashin gwiwa ban da case a nan fannin." Uwani da Auta suka saka dariya, Auta ta jima tana tausar Uwani sannan suka fito ta yi mata rakiya.
Sashenta ta koma ba ta samu Jafar a falo ba, ta zauna babu jimawa suka shiga shi da Safna. A mutumce Safna ta gaida Uwani, ita ma ta amsa mata fuska a sake har Uwani na zolayarta. Nasiha Jafar ya yi musu sosai kowacce ya nuna mata matsayinta, bayan ya gama Uwani ta lura da yadda Jafar yake jin nauyin ya ce Safna ta tashi su wuce sashenta.
"Ango dare fa yanayi, kaga akwai gajiyar taro amarya na buƙatar hutawa." A sanyaye Jafar ya kalle ta, sai a lokacin ya sake lura da 'yar ramar da ta yi. Miƙewa Jafar ya yi ya nufi hanyar fita Safna ta bi shi a baya. Suna fita Uwani ta jingina da ƙofar ta sauke ajiyar zuciya tana jin zuciyarta na zafi, motsin Hibban ta ji a ɗakinta da sauri ta ƙarasa wurinsa.
Sai da ta gama ba wa Hibban ya sha ya koma bacci sannan ta faÉ—a toilet ta watsa ruwa, ta saka rigar bacci tana fitowa Falo ta ga Jafar a zaune.
"Me ya dawo da kai kuma?" Uwani ta furta tana É—an zaro ido waje.
Hannu ya buɗe mata yana murmushi, maƙale kafaɗa Uwani ta yi ta nuna masa ƙofa da hannunta.
"Aunty Safna na can tana jiranka fa!" Tasowa ya yi ta matsa gabanta, rungumo ta ya yi ta shiga kiciniyar zillewa.
"Ya Jafar..."
Kalamanta suka katse sakamakon mayar mata da su da ya yi da bakinsa cikin bakinta.
Da ƙyar ta samu ta ɗago Jafar ya marairaice murya ya ce, "Jiddah yau kora ta kike yi?"
"Saboda lokacin amarya ne! Wallahi ba za ka zo ka birkita ka tafi..." Shiru ya yi yana kallonta, tausayinta yake ji don ya san wace ce ita da irin zafin kishinta. Amma ta yi matuƙar birge shi ganin yadda take iya sarrafa kishin nata.
"Jidda kin fitsare idonki a gabana kike faÉ—ar zan yamutsa ki?" Hijabinta ta janyo ta zura ta ja hannunsa tana faÉ—in.
"Wallahi dare na yi ba za ka bar mana amarya ita kaɗai ba." Har sashen Safna ta kai shi a bakin ƙofa ta tsaya ta ce.
"Sai da safe Nur!" Ta furta a sanyaye. Janyota ya yi ta faÉ—o jikinsa ya bi gefen kunenta ya furta.
"Allah Ya yi miki albarka Jiddah, ina ji a jikina ke 'yar Aljannah ce. I always love you." Ya yi maganar yana sakar mata fake a goshi. Idanunta suka ciko da ƙwallah jin wani irin kishi da soyayyarsa na taso mata.
"I love you too Nur." Ta furta, har ta fara tafiya Jafar ya riƙe hannunta yace zai yi mata rakiya. Sai da ya sake raka ta bakin ƙofa ya dawo yana jin zuciyarsa wani iri.
A gurguje Uwani ta shiga cikin É—akinta ta faÉ—a kan gado ta fashe da wani irin kuka mai cin zuciya. Sai da ta yi mai isarta sannan ta je ta É—auro alwala ta fara gabatar da sallah, ta jima tana kai kukanta wurin Ubangiji bayan ta gama ta koma gado tana lazumi a haka bacci ya yi awon gaba da ita.
Lokacin da Jafar ya shiga Safna har lokacin na zaune a wurin da ya bar ta, sauke mata mayafin jikinta ya yi yana lakutar hancinta. Murmushi ta saki, ya ja hannunta suka ɗauro alwala bayan idar da sallar suka zauna suna cin kazar amarci. A kunyace Safna take ci har suka gama, sannan Jafar ya fara aika mata da saƙwannin soyayya.
Ya yi mamakin irin nauyinsa da Safna take ji, Safna ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin yadda Jafar ya nuna mata kulawa da soyayya. Hakan ne ya sa ta samu ƙwarin gwiwar mayar masa da martani.
Washgari tun asuba Uwani ba ta koma bacci ba, ita ta haɗa musu kayan breakfast. Nata ta ɗora a kan dianing ta ajiye, na su Jafar ta saka musu a basket ta ajiya. Sai da ta zo gyaran falo ta tuna da kazar da Jafar ya ba ta, kitchen ta kai sannan ta shiga wanka bayan ta gama shirya Hibban. Shiryawa ta yi cikin doguwar rigar jar atamfa, ɗinkin ya mata kyau sai dai fuskarta ta yi fayau. Ta fito falo kenan ta ji shigowar Safna da Jafar, tana ganinsu ta ji wani abu ya tokare ƙirjinta.
"Innalillahi wa inna'ilahir raji'un."
Ta furta don ta ji sanyi a ranta. Ta ƙarasa fuska ɗauke da fara'a ta tarbe su, sai da suka gaisa ta miƙa musu abincin breakfast. A kan dianning Jafar ya ɗora ya shiga zuba musu don ya ce a nan za su ci tare. Safna ba ta saki jikinta ba, don yanayin yadda Jafar ke kallon Uwani yana janta da hira ne ya ɗan sosa mata zuciya, sai da suka gama sannan suka koma sashesu.
A haka kwanaki suka ci gaba da tafiya kullin Uwani ke yi musu girki har tsawon kwana ukun da musulunci ya wajabta ga bazawara, sannan suka fara rabon kwana bibbiyu a tsakaninsu.
Da farko zaman Safna da Uwani lafiya ƙalau suke yi kowa yana takatsantsan wurin shiga haƙƙin ɗan uwansa, daga baya sai zaman ya fara sauya salo musamman idan Jafar yana ɗakin Uwani. Duk ranar girkin Uwani sai Safna ta tsiri rashin lafiya ko ta ce tsoratata ake yi tana jin tsoro, musamman da a wannan lokacin Uwani ta lura kamar Safna na da ƙaramin ciki. Sau tari idan Safna ta yi haka sai dai Jafar ya tafi sashenta don ya taya ta kwana, wani lokacin kuma cikin dare za ta yi masa waya ta saka kukan wai tana jin tsoro. Tun abin ba ya damun Uwani har ta lura abin kissa ce ga shi idan ta yi magana sai Jafar ya fara faɗan ba a son barin mai ciki cikin damuwa. Wannan ya sa Uwani ta fara wata irin rama a tsaye, ganin abin ba na ƙare ba me ya sa ta ƙudurta a ranta za ta ƙwatarwa kanta 'yanci a cikin ruwan sanyi.