← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 71

Sashe 69

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da Jafar ya tsoma ƙafarsa ɗakin ƙamshin turarensa ya buge ta, idanunwanta suka sauka a kan na shi. Wani irin bugu ƙirjinsa ya yi da ƙarfi, soyayya da tausayin Safna suka taso masa lokaci ɗaya ganin wata irin muguwar ramar da ta yi.

Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan number 07062062624 Idan littafi ya kammala cmplt 800 ne☺️

#Ummou Aslam Bint Adam🌚
Cike da rashin tsammani Safna ta dasa ƙwayar idonta a kan Jafar, ba ƙaramin kyau ya yi mata ba don ta ga ya yi haske sosai har wata 'yar ƙiba ya yi. Daga bayansa ta hangi Uwani cikin doguwar rigar abaya, hannunta ɗauke da Hibban. Wani abu ta ji ya tokare ta a ƙirji, kishin Jafar da soyayyarsa suka shammace ta. Sunkuyar da kanta ƙasa ta yi wasu zafafan hawaye suka fara gangorawa daga idanunta. Daga Uwani har Jafar ba ƙaramin mamankin kammanin Safna suka yi ba, ta rame sosai ta yi duhu. A sanyaye Jafar ya furta.

"Safna ya jikin?"
Saukar kalaman Jafar ya yi daidai da bugun zuciyarta, ta shiga maimaita sunanta a saman harshenta tana mamakin yadda Jafar ya iya furta sunanta kai tsaye saɓanin daɗaɗan sunan da yake furta mata a baya.

"Aunty Safna ya sauƙin jikin?" Uwani ta furta ita ma a sanyaye.
Sai a lokacin Safna ta É—ago fuska É—auke da hawaye ta amsa.
"Jiki da sauƙi."

"Allah Ya ƙara afuwa." Suka furta mata cikin haɗin baki. Shiru ɗakin ya ɗauka hakan ya sa Uwani ta juya za ta fita don ta ba su wuri ko akwai abin da za su tattauna.
"Jiddah don Allah ki dakata ina son magana da ke." Safna ta yi maganar cikin karyewar zuciya. Dawowa Uwani ta yi ta zauna a kujerar da ta tashi sannan Safna ta ci gaba da cewa.

"Don Allah ki yafe mini abin da ya faru, dama na aikata ne bisa kururuwar shaiɗan. Ki yarda da ni, wallahi har ga Allah a lokacin ban san ke matarsa ba ce." Kuka ya ci ƙarfin Safna.

"Koda can ma ni ban riƙe ki da komai ba Aunty Safna, ba ni kaɗai ba ma, a dalilin rashin sanin da ba ki yi ba ne ya sa hatta su Dada suka yi miki uzurin haka. Allah Ya yafe mana gabaɗaya." Uwani ta yi maganar tana sake miƙewa ta fita don ba za ta juri ganin irin narkakken kallon da Jafar yake aikawa Safna mai cike da zallar tausasawa ba.
"Don Allah ka yafe mini Daddyn Hibban."
Jafar ya yi mamakin yadda aka yi Safna ta san sunan little Umar, ajiyar zuciya ya sauke ya ce.

"Na yafe miki Safna, Allah Ya yafe mana gabaÉ—aya."

"A yanzu na gama yanke ƙauna da rayuwa, don haka zan nemi wata alfarma a wurinka. Don Allah idan ba na raye ka taimaka ka yi mini takwara a cikin 'ya'yanka idan ka yi mini haka na san har abada ba za ka manta da ni ba. Domin na san a yanzu ka wuce ajina, ka ga kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa." Ƙirjinta ta ji ya yi mata wani irin nauyi, lokaci ɗaya ta fara kakarin amai. Da sauri Hajiyanta ta ƙarasa bakin gadon ta ɗauko ƙaramin bokiti ganin tana kiciniyar tallafo Safna ya sa Jafar ya yi saurin riƙe mata bokitin, ɗago Safna ta yi ta fara kelaya aman jini. Sai da ta gama sannan mahaifiyarta ta saka tissue ta goge mata baki, jikin Jafar har rawa yake da ya ga halin da Safna take ciki. Sai da Hajiyanta ta kwantar da ita sannan ta fita ta sake kiran Likita, da sauri likitocin suka shigo sauka buƙaci su Jafar da su fita waje.

Jafar na fita ya samu Uwani a reception a zaune, ganin sanyin jikinsa da na Hajiyan Safna ya sa ta shiga jera musu tambayoyi. Jafar ne ya yi mata bayani mahaifiyar Safna ban da kuka babu abin da take yi, suna nan tsaye bayan wani lokaci likitocin suka fito. Kusan su ukun da sauri suka tare su da tambaya.

"Jikinta ne ya sake dawowa, amma Hajiya tun jiya da kuka zo asibintin nan mun ce miki akwai wani abu da yake damun yarinyar nan, da ya dace a zauna a tattauna da ita don a ji me take buƙata amma har yanzu shiru." Hajiyan Safna cikin kuka ta ce.

"Likita abin da Safna take so ne ba za ta samu ba, don haka babu fa'idar sake tattaunawar."

"Amma Hajiya wanne irin abu ne haka? Kuma kun taɓa jarrabawa ba ku sama mata shi ba?" Likitan ya tambaya. Hajiyan Safna ta gyaɗa kai tana goge hawaye.
"Allah shi ya ba mu Safna ita kaɗai, kuma ina ganin wannan na daga cikin layin ƙaddararta ne. Idan tana da kwana a gaba sai ka ga ta tashi, idan kuma babu haka Allah ya ƙaddara." Shi kansa jikin Likitan ya yi sanyi, ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Idan kin gama ina son ganinki a office." Daga haka ya wuce.
Sallama Hajiyan Safna ta yi wa su Jafar sannan ta bi bayan Likitan, jiki a sanyaye suka nufi mota babu mai iya magana a cikinsu.
Tabbas so ba ƙarya ba ne, Jafar tuƙi kawai yake amma hankali da zuciyarsa na wurin Safna. Kamar Uwani ta san abin da yake zuciyarsa ta furta.

"Nur!"
Waigowa ya yi ya kalle ta ba tare da ya amsa ba.
"Safna na buƙatar kulawarka! Ya zame maka wajibi ka yi wannan jihadin ko don ceton rayuwarta. Tana cikin mawuyacin halin da duk rashin imanin mutum dole ya tausaya mata, duk wannan ka san mene ne sila?" Ta wurga masa tambaya. Girgiza mata kai ya yi.
"So da ƙaunarka sune silar faruwar halin da take ciki, belive me idan har ka ce za ka dawo da ita za ta samu lafiya cikin yardar Ubangiji." Shiru Jafar ya yi ya mayar da kansa titi zuciyarsa na juya maganganun Uwani.

Washegari da sassafe Daddy ya kira Jafar a waya yana yi masa faÉ—a game da halin da Safna take ciki, dalilin wayar da suka yi shi da mahaifin Safna musamman da ya ji irin mawuyacin halin da take ciki. Sun jima suna waya sannan suka yi sallama, shiru Jafar ya yi hakan ya sa Uwani ta tisa maganganun da ta yi masa a game da Safna.
Uwani da kanta ta shirya Jafar ta ƙarfafa masa gwiwa ya tafi asibitin. A lokacin da ya je asibitin Hajiyan Safna na ganinsa bayan sun gaisa ta haɗa hannuwa biyu alamar roƙo ta ce.

"Mun gode ƙwarai Jafar da kulawar da ka nuna wa Safna, amma don Allah kada ka kuma zuwa wurinta domin ganinka ya jefa ta cikin mawuyancin hali. Ina fatan za ka yi mini kyakkyawar fahimta, domin a kullin ta yi tozali da kai yana tayar mata da mikin da ya haddasa mata lalurar da take ciki." Ta ba shi tausayi matuƙa sai da ya gama sauraronta ya ce.

"Mummy na zo ne domin na sanar da Safna zan mayar da ita, In Shaa Allahu jibi Juma'a za a mayar mana da aure..." Tun bai gama magana ba Mummy ta riƙo hannunsa tana tattaɓawa.
"Da gaske Jafar kai ne kuma abin da kake faɗa haka ne?" Gyaɗa mata kai ya yi, suna nan jikin ƙofar suka ji motsin Safna.
Jafar ne ya shiga tana ganinsa a wannan karon ma kallonsa take tana hawaye. Sai da ya ja kujera ya zauna ya sunkuyar da kansa daidai fuskarta ya sakar mata murmushi sannan ya furta.

"Goge hawayenki Cutiena!" Kamar a mafarki ta ji kalaman nasa, take ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri. Hannu na rawa ta goge fuskarta, har lokacin kallonsa take murya a sanyaye ta ce.
"Ya Allah idan mafarki nake yi kada ka sa na farka a yanzu."
"Ba mafarki kike ba Habibty!" Jafar ya faÉ—a yana sakar mata murmushi. Hannu ta kai ta shafi fuskarsa don ta tabbatar da kokontanta.

"Ina farincikin sanar da ke ranar Friday su Daddy za su mayar da aurenmu." Da sauri ta zaro ido waje hakan da ta yi ba ƙaramin birge shi ya yi ba, iska ya hura mata a fuska ya kashe mata ido ɗaya. Kunya ce ta kamata ta yunƙura da ƙyar za ta tashi, Jafar har zai taimaka mata ya tuna a wannan lokacin ba matarsa ba ce. Hajiyanta ya fita ya kira ta zo ta taimaka mata, fita ta sake yi ta ba su wuri.

"Amma maman Hibban ta san da haka kuwa? Gani nake kamar ba za ta..." Da sauri Jafar ya katse ta da faÉ—in.

"Jidda ce ta ƙarfafa mini gwiwar da na iso wurinki a safiyar nan cike da ƙwarin gwiwa, Jidda ta dabance a cikin mata domin tana da kyakkyawar mu'amala, sai kun zauna za ki fahimci haka saboda ita mutuniyar kirki ce. Kuma jajirtacciya 'yar aljanna."

"Jafar da ko hirar wata 'ya mace bai taɓa yi mini ba amma yau shi ne yake yabon matarsa a gabana, tabbas jiya ba yau ba ce." Safna ta raya a ranta. Murmushin ƙarfin hali ta saki sannan ta ce.
"Ko a jiya na fahimci haka."
Jafar ya jima a wurin Safna yana janta da hira, hatta ruwan tea shi ya ba ta da kansa. Sai kusan Azahar sannan ya bar asibitin. Likitan da ke duba Safna ba ƙaramin mamakin sauyin da aka samu ya yi ba, shi kansa Daddy ya ji daɗin ganin yadda ya je ya same ta a zaune har suka yi hira. Kuma tun daga ranar jikin Safna ƙara gaba yake yana yin kyau, saboda kullin sai Jafar ya je asibitin sun yi hira ya ɗebe mata kewa.
Chapter 69 · 0% Book details