← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 71

Sashe 24

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tass! tass! Jafar ya sauke wa Uwani wasu tagwayen mari biyu a fuska, cikin ɓacin rai ya furta. "Uban waye ya ce ki fita? Ba ki da hankali za ki fita da waɗannan kayan?" Ganin yadda Jafar ya hargitse mata lokaci ya sa nan take jikinta ya fara karkarwa, ya rufe ta da faɗa tamkar zai rife ta da duka daga ƙarshe ya faɗa toilet ya bar ta a zaune. Bai jima ba ya fito har lokacin ransa a ɓace yake ya furta.

"Ki shiga ki yi wanka za mu wuce gida yanzu." Zani uwani ta É—auka ta faÉ—a ban É—aki kafin ta fito har Jafar ya gama shiryawa, gefe da gefen fuskar Uwani har ya É—an kumbura don har lokacin ba ta daina hawaye ba.

Jafar na zaune a gefen gado ya hango Uwani ta fito don ita ta manta ko hula ma ba ta saka ba, a razane yake bin ta da kallo baki sake. Ganin irin kallon da Jafar yake bin ta da shi ya sa Uwata ta sha jinin jikinta, tana sake tunkaro shi Jafar ya zabura a guje ya nufi ƙofa yana faɗin.
"Wayyo Allah! Jama'a ku taimaka mini sun biyo ni nan ma!" Da yake ya manta ya datse ƙofar haka ya yi ta murɗawa ta ƙi buɗuwa. Cikin rashin fahimta Uwani ta ɗan waiga ta ce.
"Wai ya Jafar me yake faruwa ne?" Laƙwas Jafar ya yi ya zauna a ƙasa kamar mutum-mutumi yana kare mata kallon, tamkar ya ga sabuwar hallita. Uwani ta shiga goge kanta da towel ko a jikinta ta ce. "Malam ka fita zan shirya."

Har lokacin Jafar mamakin Uwani yake, ya shiga tariyo abin da ya dinga faruwa a cikin dare. Uwani ta fahimci sarai in da Jafar ya dosa, ta fito da kayan da za ta saka ta sake furta. "Don Allah ka fita zan shirya."

"Uwani ina gashinki?" Cikin halin ko in kula ta ce. "Dada ta aske mini tun rannan."

Miƙewa ya yi ya tako gabanta sannan ya furta. "Wato iskanci ne ya sa kika dinga tsora ta ni ko? Wallahi za ki shiga hannuna da ni kike zancen." Take dariyar da Uwani ke gimtsewa ta suɓuce mata. Jafar ya saki wani malalacin murmushin mugunta yana ayyana irin azabar da zai yi mata cikin ruwan sanyi ba tare da Daddy ya gane ba. Daga haka Jafar ya fice daga ɗakin, Uwani ta saka kayanta sannan ta haɗa ragowar kayanta da ke warwatse ta saka a jaka.

Ba su ɗauki lokaci ba suka shirya suka fito Jafar ya ƙarasa gaban ma'aikatan da ke reception ya biya duk abin da ya suka kashe, sannan ya yi musu sallama suka fita da yake akwai Manajan wurin da shi a ka kai Alhaji can police station. Domin a cewar Manajan Alhajin na ƙarƙashin kulawarsu dole ne su san halin da yake ciki.

Lokacin da su Uwani suka ƙarasa gida mommy ta rako ƙawarta Hajiya Binta bakin gate, ganin su Uwani ya sa Mami ta yi turus tana faɗin.

"Ya aka yi Jafar?" Jafar ya É—an sosai, sannan ya gaida Hajiya Binta da ke bin sa da kallon tuhuma.

"Ƙawata wai kar dai raɗe-raɗin da nake ji a kan auren Jafar haka ne?" Hajiya Binta ta tambaya tana satar kallon Uwani. Ras! Gaban Mami ya faɗi, ta ɗan basar tana ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce. "Haba Hajiya Binta kina ganin akwai yarinyar da Jafar zai aura a duniyar nan bayan Safna? Ai me aiki ce ya taho mini da ita daga Lagos, a bakin gada take kwana shi ne ta roƙe shi Allah-Annabi wai ta dinga yi masa aiki. Da ya sanar da ni na ce idan zai taho ya kawo mini ita, kin san ɗa na kowa ne ƙawata." Cikin gamsuwa Hajiya Binta ta bi Uwani da wulaƙantaccen kallo ta furta.

"Ban da taɓarɓarewar zamani yanzu wannan yarinyar har ta isa kwanan gada, mtsww Allah Ya sawaƙe." Mami ta furta. "Amin dai, yo yaran da maza ke ba su ɗari biyar suna sa su a ɗaki ina za ki yi mamaki?" Kalaman Mami da ƙarshe da ta jefi Uwani da su ba ƙaramin zafi suka yi masa ba, don haka ko sallama bai yi wa Hajiya Binta ba ya wuce. Ita kanta Uwani kusan daskarewa ta yi a wurin jin irin munanan kalaman da Mami ta jefe ta da shi, tunanin da ta zurfafa ciki ne ya sa Jafar ya wuce ba tare da ta sani ba. A ɗan tsawace Mami ta ce.
"Tsawar me kike yi a gabanmu ne?" Babu yadda ta iya haka Uwani ta ja jaka jiki a sanyaye ta wuce ciki, kai tsaye sashensu ta shiga idanunta cike da ƙwallah.

Sanin Daddy ba ya gidan ya sa Mami kai tsaye ta wuce sashen su Jafar, a falo ta same su duka ta dubi Jafar ta ce.
"Wai fasa tafiyar ka yi ne Jafar?" Bai É—ago ya kalle ya ba ya furta, "Eh Mami." Jim ta yi tana nazartarsa ta furta.

"To haka za ka zauna ana tsorata ka har a sabauta mini kai?" Jafar ya furta. "Ai na biya ta Islama Islamic Center na karɓo magani, kuma ya ce mini za a dace In shaa Allah." Jafar shi kansa ya yi mamaki yadda ya tsara wa Mami wannan jawabin, Mami ta wurga wa Uwani mugun kallo ta ce.
"Wuce mu je akwai aikin da za ki yi mini." Babu musu Uwani ta bi bayan Mami, Jafar ya kwanta a kan doguwar kujewa. Haka kawai ya ji yana kewar Safna, don haka ya zaro waya ya kira ta suka fara hira.

Mami na shiga sashensu ta haÉ—o wa Uwani wanki duk da a lokacin magriba ta fara kawo kai, bayan gida ta zuba mata wankin ta yadda koda an yi a arashi Daddy ya dawo ba zai ganta ba ballanta ya yi mata faÉ—a. Kuma dama ta san ba ya gari, don haka za ta ci karenta babu babbaka akan Uwanin.
Cikin wankin da Mami ta haÉ—o wa Uwani har da labulaye da zannuwan gado, tun Uwani na wankin cikin daÉ—in rai har ta fara galabaita tun da ko a wurin Dada ba ita take yin wankin kayanta ba. Lokacin da aka kira sallar magriba Uwani wucewa ta yi sashenta don ya gabatar da sallah, tafiyarta babu jimawa Mami ta zagaya ta ga wurin wayam. Sai tsirarin kayan da ta shanya ga waÉ—ansu nan a cikin ruwa.

Uwani na zaune tana zaman tahiya Jafar ya shiga ya zaune yana kallonta, a yadda ya lura da Uwani duk hatsabibanci da ƙiriniyarta ba ta wasa da sallah ko kaɗan. Hakan ba ƙaramin birge shi yake ba, yana nan zaune Mami ta shigo ko shi ba ta yi wa magana ba ta rufe Uwani da duka. Ganin dukan da take wa Uwani ba zai ƙare ba ya sa Jafar ya yi saurin shan gaban ta.

"Lafiya kuwa Mami? Me ta yi miki haka?" Jafar ya furta hankali a tashe.

"Lallai Jafar wannan abar har kake tarewa?" Mami ta faÉ—a tana sauke numfashi.

Ban da kuka babu abin da Uwani take yi, ga gefen bakinta ya fashe jini na ɗiga. Saboda yadda ta galabaita kukan da take yi ko fita ba ya yi, Mami ta sake zuba mata ranƙwashi a ka tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Mami wai me ta yi miki?"

"Wanki na saka ta don iskanci za ta zube mini ta zo ta saka miji a gaba, idan uwarki ce ta saka ki za ki ajiye mata." Mami ta yi maganar tana dungurin Uwani, cikin kuka Uwani ta ce. "Sallah aka kira shi ne na zo na yi..." Da sauri Mami ta sake doke Uwani nan take bakinta ya sake fashewa.

"Haba Mami, ina ce Haladu ne yake yin wanki. Kuma sallah fa ta ce ta zo..." Tas! Mami ta ɗauke Jafar da mari, ba ta tanka masa ba ta figi hijabin Uwani ta fara janta a ƙasa, ba shiri Uwani ta miƙe ta bi Mami. Saboda ɓacin rai tun ba su gama fita ba Jafar ya gegare su ya fice daga gidan zuciyarsa na suya.

"Iyeee Allah Jafar watsa mini ƙasa za ka yi a ido yaushe har ka san zafin mace. Wallahi dole kai ma na ɗauki mataki a kanka." Mami ta yi maganar a ɗan tsorace don ta yi tsammanin ko wuta za ta jefa Uwani sai dai Jafar ya taya ta ba dai ya hana ba.

A cikin duhu ga sauro haka Uwani ta wanke ragowar kayan da ba ta ƙarasa ba, kanta ban da ciwo babu abin da yake yi. Bayan ta gama ne ta nufi sashen Mami har ƙasa ta zube ta furta. "Na gama wankin." A yamutse Mami ta dube ta tana shirin sallamarta Shukra ta shiga ɗakin tana taunar cingam ta ce. "Ke zan saka ki aiki yanzu saura ki yi mini hauka." Uwani ta ɗaga kai a galabaice ta amsa wa Shukra. Auta da ke zaune a gefe duk sai ta ji babu daɗi, tana son ta yi magana amma tana tsoron faɗan Mami.

"Kina ji Shukra na yi miki magana ba za ki iya amsawa ba?" Mami ta yi maganar tana haurin Uwani. Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta rarrafa gaban Shukra ta tsugunna.

"Ga Salim nan ya faka motarsa a cikin gate, za ki je ki wanke masa kuma wallahi idan ba ta wanku ba sai kin sake." Da sauri Auta ta furta. "Aunty Shukra wankin mota fa?"

Shukra ta sake shan kunu ta ce, "Waya na yi da shi zai kai wankin mota ya ce ba zai samu zuwa yau ba, so don haka na ce ya zo gida za a wanke masa saboda ina son magana da shi." Cikin tausaya Auta ta ce, "To shi kenan zan ta ya ki Uwani..."

"Waye ya gayyace ki? Uwar iyayi da kankanba?" Mami ta katse Auta.

Shukra ce ta yi gaba Uwani ta bi bayanta a lokacin zazzaɓi har ya fara rufe ta, lokacin da suka ƙarasa Salim na cikin mota. Da ya hango su ne ya fito yana sakarwa Shukra murmushi.

"You are welcome dear." Shukra ta furta tana fari da ido.
Chapter 24 · 0% Book details