Sashe 31
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da komai ya lafa sannan kowa ya fara gane a mahallin da yake, Salim na tsugunne a bayan manyan sifikun Mc sai a lokacin ya farga da ashe akwai mutum a cikin babbar rigarsa. Miƙewa ya fara yunƙurin yi sai a lokacin Mami ta ji yana jan kanta, a tunaninta ƙadangaren ne yake fusgarta. Ihu ta zuba tana jan kanta shi ma Salim ya saki ihu yana jan babbar rigarsa, babu zato sai gani aka yi daga ita har shi sun zube a ƙasa. Da ƙyar Mami ta zaro kanta daga cikin babbar rigar Salim yayin da ɗankwalin gwaggwaronta ta hango shi a saman kan Salim. Cibiri-cibirin gashin Mami duk ya tashi tsaye da bai wuce kamu ɗaiɗai ba, a kunyace Salim ya miƙe yana kaɗe jikinsa sai ji ya yi gwaggwaron Mami ya faɗo.
Shukra na daga ƙarƙashin table ta ɗago a hankali tana goge hawayen baƙin ciki, wata ƙanwar Mami ce ta cire mayafinta ta rufa wa Mami a kanta, sannan ta kama ta ta zaunar da ita a kan kujera. Salim neman duniya ya yi wa hularsa bai ganta ba don haka ko ta kan Shukra bai bi ba shi da Abokansa suka fice daga cikin hall ɗin a guje manyan rigunansu sai tashi sama suke yi.
Saboda tsananin ɓacin rai sai kawai Mami ta rushe da matsanancin kuka, ita tana yi Shukra na taya ta. Ita kanta Auta jikinta duk ya yi sanyin don abin bai yi daɗi ba. Mami ta sake kallon wurin da irin dukiyar da ta kashe, hatta ɓangaren abinci ta zube masa maƙudan kuɗin abinci. Sai ga shi a cikin hall ɗin ko cokali ɗaya ba ta jin wani ya ci na abinci, ga shi kowa ya tarwatse.
Kafin wani lokaci tuni hall ɗin ya ɗaɗe sai tsirarin mutane masu ganin ƙwaƙwaf, lokaci ɗaya ƙananan maganganu suka fara tashi wasu su ce a tsofaffin samarin Shukra ne suka yi mata ture, wasu kuma su ce Salim aka yi wa. A raɗe-raɗin ne maganar auren Mami da ƙandare ta ɓilla, sai da Mami ta ci kukanta ta koshi sannan ta ɗebo takalmanta a hannu sun zo fita sai ga gayyar 'yan jarida sun shigo ɗaukan rahoto.
"Sannu Hajiya, a yadda muka fahimta kamar kema wata jigo ce a cikin shagalin auren ko? Shin ko akwai wani ƙarin haske da bayanin da za ki iya yi mana dangane da abin da ya faru?"
"Kwatsam Hajiya sai kuma aka riski ƙaton ƙadangare a cikin jakar uwar taro, ko za ki yi tsokaci a kan haka? Shin akwai wanda kuke zargi a kan faruwar wannan al'amarin?"
"Hajiya a yadda rahoto ya zo mana an ce sirikin uwar taron ma ya samu tagomashin samun ƙadangare a cikin aljihunsa ko akwai wani abu me alaƙa tsakanin ƙadangaren wurin uwar amaryar da na wurin shi angon?"
'Yan jaridar suka dinga jefa wa Mami tambayoyi, kafe su ta yi da kallo cikin ɓacin rai ta haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ya fara sauke fushin ta a kansu tana faɗin, "Da kai, da kai da sauran ma'aikatan gabaɗaya kun ci ubanku. Munafukai masu jiran kaɗan ku ƙara, duk wanda ya ƙara tunkaro ni da tambaya sai na ci ubansa." Mami na gama magana fuuu ta wuce zuciya na suya.
Dada da a lokacin ita ma ta samu sukunin fitowa wani É—an jarida ya tare ta da tambaye. "Hajiya barka da fitowa! Hajiya shin ko akwai abin da za ki faÉ—a dangane da faruwar wannan abin?"
Dada ta riƙe haɓa cikin sanyin jiki sannan ta ce. "Yaro ba dole na samu abin faɗa ba, ni fa na haifi uban Shukra. Ko ba ka san Mammam Mai shanu ba ɗan sanda?" Ɗan jaridar ya sake riƙe abin naɗar muryar cikin jin daɗin haɗin kan Dada da ya samu ya ce, "Hajiya waye bai san Mai shanu ba ai fitacccen ɗan sanda ne."
"To mu dai muna tsaye mun gama kama amarya da ango sai Saro ta saka hannu a jaka sai fa kawai ƙadangare muka gani, kai na yi mantuwa shi dai ƙadangaren kwanakin baya ya tarfa Saro a bayi tana wanka wai ya aure ta. Ni dai ban san me ya kawo shi yau ba, ina kira ga malaman garin nan su kawo wa Mamman ɗauki kada sabon angon Saro ya halaka mini ɗa." Dada na gama faɗar har ta yi gaba sai kuma ta sake dawowa.
Wani ɗan jaridar ne ya sake tunkararta ta dakatar da shi sannan ta tara duka sauran 'yan jaridar, sai da kowannensu ya gama saita na'urar ɗaukar sautinsa sai kawai Dada ta fashe da kuka. Ganin kukan Dada ba mai ƙarewa ba ne ya sa suka fara kashe na'urar naɗar sautin suka shiga rarrashinta, ta share hawaye da gefen mayafinta sannan ta ce.
"Kaicon wannan lusari da zai tsaya yana bibiyar Saro da zuri'arta domin abin da ya yi Mamman shi ya yi Saratu. Yaro shekararsu sama da talatin da biyar da aure, shin Saro ba ta zama Mamman ba?" Dada ta tambaye su, cikin haÉ—ain baki suka amsa mata ta ci gaba da cewa.
"Ai ni tsohuwa ya kamata wannan ƙadangaren ya tunkara domin mune muke kan hanyar tafiya, ba Saro da ke fama da ɗawainiyar Mamman da iyalansa ba." 'Yan jaridar suka shiga kallon-kallo kowa da abin da yake raya wa a ransa, wasu kuma sai murmushi suke. Dada ta dunƙule hannuwa, sannan ta ɗaga su sama jikinta har karkarwa yake cike da rashin tsoro ta ci gaba.
"Ni na sadaukar musu da kaina amma su ƙyale iyalan Mamman su zauna lafiya..." Atika 'yar wurin Dada ta biyun ƙarshe ta ɗan zunguro Dada tana ƙasa da murya ta ce.
"A'a Dada su fa mutanen nan ba a yi musu haka!" Dada ta doke hannun Atika a É—an fusace ta sake mayar da kallonta wurin 'yan Jaridar ta ce.
"Ina kira da babbar murya, duk wani taƙadirin aljani a shirye nake da ya tunkaro ni. Ni Kulu yadda su Mamman suka faranta mini rai ba zan bari a tarwatse zaman lafiyarsu ba. Ni na bar ku lafiya na gode kowa zai iya tafiya."
Dada na gama magana hayaniya ta kacame a wurin, Uwani da ke gefe ta zuba wa Dada ido a ranta ta furta.
"Za ki yi mini bayani kuwa."
"Hajiya ko akwai abin da kika taka da har kike irin wannan iƙirarin?" Wani ɗan jarida ya tambayi Dada. Ta waiga ta ce. "Kai yaro wannan yaƙin da kake gani na zuri'ata ne zan iya tarar komai da kowa a kansu." Daga haka Dada ta fice.
Duk yadda suka so sake jin ta bakin Dada ba ta kula su ba, a haka kowa ya watse.
Lokacin da kowa ya koma gida haka aka haÉ—u aka dinga jajantawa, abincin da Mami take ta kaffa-kaffa da shi da kajin ciki tana ji tana gani aka baje shi da daddare aka cinye. Shukra kuwa tun da ta shiga É—akinsu ban da kuka babu abin da take yi.
Cikin Dare
Cikin sanɗa Uwani ta fice daga sashenta don lokacin bacci Jafar yake har da munshari, kasancewar a ranar suka dawo daga kaduna shi da Ibrahim a kan wani aike da Daddy ya yi musu don su wakilce shi, ya sa ya gaji tuɓus. Kamar mara gaskiya haka ta dunfari sashen Mami, ta yi sa'a kuma a buɗe yake don haka tana shiga ta leƙa ɗakin da su Dada suke ciki. Shi ma a buɗe ta same shi duk sun baje sai sauke munshari suke yi, kashe glub ɗin falon ta yi ta ciro wata wayar caja ta riƙe.
Da Sajida ta fara cin karo matashiyar budurwa ce 'yar wurin Baba Inusa, sai da Uwani ta ja wata ƙatuwar hular sanyinta ta rufe fuskarta ta fara jan hannun Sajida, sai da kawo ta falo sannan ta ɗaga wayar caja ta zuba mata a baya. A zabure Sajida ta miƙe tana susa ta shige ɗakin a guje, Uwani ta saki murmushi lokacin da ta reƙa hannuwan Dada ta fara ja. Dama saboda yanayin cinkoso da zafi Dada daga ita sai ɗaurin ƙirji. Tun da Uwani ta fara jan Dada zanin jikinta ya faɗi daga ita sai ɗan tofi, cikin bacci Dada ta ji ana janta tana buɗe ido ta ganta a duhu.
"Waye haka yake figa ta cikin dare kamar kaza?" Dada ta faÉ—a a tsorace. Uwani ta kausashe murya ta ce.
"Mune da kika gayyato kika ce za ki yi yaƙi da mu, ga mu mun zo tafiya da ke mu kacalcala namanki."
Uwani na faɗar haka ta saka hannu ta fisgo maman Dada ta ci gaba da cewa. "Da farko dai za mu saka lauje mu yanke waɗannan abubuwan, sai mu feɗe su mu yi banda ranar amarcin sabuwar matar da za mu aura mu ci amarci da su, tun da kina yunƙurin hana mu keɓewa da Saratu."
Littafin kuÉ—i ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wnn lambar 07062062624 idan littafi ya kammala cmplt 800
#Ummou Aslam Bint Adam
*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅