Sashe 44
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Baby zan mare ki ne ba don ina so ba. Kin san soyayyar da nake yi miki ba zan iya marinki ba sai da dalili..." Maganar Salim ta katse sakamakon wani gigitaccan mari da Uwani ta zabga musu daga shi har Shukra da hannuwanta. A gigice kusan lokaci ɗaya suka ƙwalla ƙara, Shukra ta faɗa ɗaki a guje Salim ya bi ta yana buga ƙofar amma ba ta bi ta kansa ba ta banka sakata. Salim yana kuka yana buga ƙofa har Uwani ta ƙarasa wurinsa, a lokacin hannunta ɗauke yake ta ludayin sulba. Da yake Salim ya gama tsorata hannu ɗaya Uwani ta saka ta fisgo rigar shaddarsa, sai ji kake ƙuuuum ta yi wurgi da shi. A zabure Salim ya miƙe yana ihu ya faɗa ɗakin da Uwani ta kwana shi ma ya banke ƙofar da sakata.
Littafin kuÉ—i ne a kan 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala cmplt 800 neðŸ«
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
Uwani na ganin Salim ya shige ɗakin ta je ƙofar ɗakin da Shukra ta shiga ta fara bugawa, ta kausashe murya ta fara faɗin.
"Wallahi sai mun yi maganinku, ke da mijinki kun tsokano bala'i mara yankewa. Idan ma ba ku buɗe ƙofar ba za mu ɗaga gidan gabaɗaya mu kifar da shi." Jin abin da Uwani ta faɗa ya sa Salim da Shukra suka sake shiga tashin hankali, Shukra ban da kuka babu abin da take yi. Ga shi babban tashin hankalinta wayarta na falo ballantana ta kira Mami ta sanar da ita abin da yake faruwa. Salim na cikin ɗakinsa ya laluba wayarsa ya ciro daga aljihu, lambar Saminu abokinsa ya kira cikin ƙasa da murya ya ce.
"Saminu muna cikin tashin hankali." Saminu jin muryar Salim ƙasa-ƙasa ya sa ya ce. "Me ya faru abokina ka ɗaga murya ba na jin ka." Uwani na daga falo ta jiyo maganar Salim ƙasa-ƙasa don haka ta fahimci waya yake yi, da ƙarfi ta doka ƙofar ta ce. "Da kai da wanda kuke wayar sai mun haɗa ku mun murɗe muku wuya."
Jin haka ya sa Salim ya fashe da kuka jiki na karkarwa ya sanarwa Saminu abin da yake faruwa, Saminu ya yi murmushin takaici ya ce.
"Amma wallahi abokina ka ji kunya, yanzu aljanun yarinya ƙarama ne za su sa gotai-gotai da kai ka dinga kuka har ka rufe kanka a ɗaki, bari dama ta hanyarku zan wuce gani nan zan biyo." Duk maganar da suka yi Uwani na daga falo tana jin Salim har ya gama waya, shiru ta yi tana nazari a ɓangare ɗaya gabanta na ɗan faɗuwa don tana tsoron kada asirinta ya tonu a gane ba aljanun gaske ba ne.
Uwani na daga tsaye ta hangi Shukra ta fara buɗe ƙofa tana zuro kai, da gudu Uwani ta nufi ƙofar tana faɗin. "Za mu ƙwaƙwale ƙwayar idonta." A guje Shukra ta sake danno ƙofar sai ta sake fashewa da kuka.
Uwani tana nan a zaune babu jimawa ta ji Gali mai gadi ya wangale gate, wanda hakan ne ya ba ta tabbacin Saminu abokin Salim ne ya ƙaraso. Cikin kitchen ta shiga ta turo ƙofa ta yi luf, ba a daɗe ba ta ji sallamarsa cikin falon. Shiru Uwani ta yi ba ta tanka masa ba, a can ƙasa-ƙasa ta ji muryar Salim ya amsa.
"Kai dallah matsoraci ka fito, wannan ma ai babban abin kunya ne ace yarinya ƙarama tana raina muku hankali. Ni akwai aljanin da zai ɗaga mini lissafi, ai ko ifiritu ne a kanta take masa wuya zan yi." Jin irin kurantawar da Saminu yake wa kansa ya sa Salim ya yi ta maza ya leƙo kai, ya yi ƙasa da murya yana faɗin.
"Saminu ka yi ƙasa-ƙasa wallahi aljanun jikin yarinyar nan ƙarfi gare su." Saminu ya saki tsaki, ya ce.
"Ubansu! Kai matsa gefe wai ina Shukran take ne ko ita ma ta shige É—akin?" Sai a lokacin Shukra ta fito fuska a kumbure ta yi jawur, gefen kumatunta na hagu har da shatin hannun Uwani.
"Salim tun da na samu Saminu ya fito wallahi gidanmu zan tafi." Shukra ta yi maganar tana ƙoƙarin fita. Daga cikin kitchen suka ji Uwani ta tuntsire da dariya, sai kuma ta fara wani irin gurnani. Salim da Shukra a zabure suka miƙe suna kallon juna, Saminu ya miƙe tsaye yana ƙwambare kafaɗu sai da ya zuba hannu a aljihu sannan ya ce. "Wannan fa kada ya dame ku, ku dai ku bar mini komai a hannuna. Ke wane ɗan iskan ne a kanki?" Saminu ya tambaya yana kallon ƙofar kitchen.
Suna nan a tsaye carko-carko suka ga Uwani ta fito zuwa ƙofar kitchen ɗin ta tsaya, kanta ɗauke da ƙaton kwandon wanke-wanke. Gwalo ido waje ta fara tana wani harare-harare, sannan ta fara ɗaukan kwanukan ciki ta jifansu tamkar yadda ake jifan shaiɗan. Sai da Uwani ta ƙarar da kwanunka sannan ta tunkari Saminu da ke tsaye, ganin haka ya sa gaban Saminu ya faɗi amma sai ya dake don kada Uwani ta fahimci ya fara tsorata da lamarinta. Su Salim na ganin haka suka fara ja da baya, Uwani na zuwa ta kifa kwandon wanke-wanken a kan Saminu. Ta sa hannu ta fisgo shi sai ga Saminu a cikin kwando ana jan kansa kamar wani rago.
"Ga wani ƙarin naman mun samu, yau kam sai dai mahaifiyarsa ta haifo wani ba shi ba. Kunzuzuuuu ka zo ga irin jinin wanda kake so." Uwani ta ƙarasa zancen ta kai wa Saminu duka da farantin da ke ɗayan hannunta. Saminu na jin haka ya fara kiciniyar ƙwacewa, da ƙyar ya samu ya cire kwandon daga kansa. Shukra da Salim dama tuni suka shige ɗaki, daɗin da Shukra ta ji da ta ɗauki wayarta ta shiga da ita.
Saminu na shirin fita a guje Uwani ta yi sufa ta datse ƙofar, sai da ta rufe sannan ta zare key ta ɗaga kanta ta wurga shi cikin bakinta. Da sauru ta kawar da kai gefe ta fito da shi ta soke mukullin, shi kuma da yake Saminu bai lura ba tuni cikinsa ya kaɗa. Uwani ta wage baki tana tauna da haɗiya kamar mai cin abu sannan ta ce.
"Kamar yadda muka taune wannan mukullin haka za mu haɗiye ku ɗaya bayan ɗaya." Uwani na gama maganar ta ga fitsari na bin wandon Saminu, ta ɗauko robar yajin da Salim ya sha ya rage ta miƙa wa Saminu cikin wata irin murya ta ce. "Riƙe ka shanye shi tass, domin idan mun zo cin namanka mu ci shi da yaji-yaji. Idan ka shanye zan ɗauko maka mai galan guda ka shanye domin man jikinka ya yi mana kaɗan."
"Don Allah ku yi haƙuri, ni dai tsautsayi ne ya kawo ni gidan nan." Saminu ya furta cikin zubar hawaye.
Uwani ta suri wani ludayi ta ranƙwala wa Saminu, tun ba ta yi magana ba Saminu ya ɗauki robar yajin ya fara zazzagawa a baki. Yana sha yana hawaye ga wani azabar zafin yaji na ratsa shi. Numfashinsa ne ya fara yin sama, don haka ya ɓarke da kuka. A guje Uwani ta nufi ƙofar ɗakin da Shukra da salim suka shiga ta fara dukanta iya ƙarfinta. Hakan ya sa Saminu ya samu sukunin tashi a guje ya faɗa cikin kitchen ya rufe.
Jin irin bugun da Uwani take yi ya sa Shukra cikin kuka ta kira Mami, Mami na ɗauka Shukra ta fashe da kuka sannan ta ce. "Mami na shiga uku, wallahi Uwani kashe mu za ta yi don Allah ku kawo mini ɗauki." Mami na shirin magana da mamaki ta ji Salim ya ɓarke da kuka, garjejiyar muryarsa ta ciki mata kunne.
"Ke Shukra me kike faɗa ne? Kukan waye nake ji haka?" Bam! Bam! Bam! Mami ta ji ƙara ta cikin waya. Salim ya yi sauri ya fisgi wayar a hannun Shukra cikin garjejiyar muryarsa yana kuka ya ce.
"Mami don Allah ki kawo mana ɗauki, wallahi aljanun Uwani hallaka mu za su yi." Jin da gaske Uwani na shirin karye ƙofar ya sa Shukra ta sake fashewa da kuka .
"Ku saurare ni da kyau ku ji, wallahi ni nan da kuka gan ni na fi ku shiga tashin hankali. Uwani dai ga dukkan alamu tana da alaƙa da aljanu..." Mami ta kwashe duk abin da ya faru da tsakaninta da bunsuru, sannan ta ɗora da cewar. "Don haka ni yanzu babu wani taimako da zan iya yi muku, ni dai wallahi har abada na bar muku Uwani ta zauna a wurinku. " Daga haka Mami ta kashe wayar. A daidai lokacin Uwani ta samu nasarar karye ƙofar ɗakin, ƙofar na faɗuwa sai ita ma ta faɗi a ƙasa yaraf. Daga Shukra har Salim aka rasa mai motsi saboda tashin hankali. Suna son fita daga ɗakin suna jin tsoro saboda Uwani da ta yi kwance a bakin ƙofar,sai bayan wani lokaci ta ɗan fara motsawa a hankali. Tashi zaune Uwani ta yi tana jera atishawa tana murtsuka idanu, ta fara kallon su Salim da yanayin mamaki sannan ta miƙe tsaye ta ce.
"Aunty Shukra lafiya na ga kina kuka ko jikin ne?" Gaban Shukra ya faɗi, amma sai ta ƙaƙalo murmushin yaƙe ta ce. "Cikina ne yake ciwo wallahi."
Uwani na kai kallonta wurin ƙofar da ta karya ta dafe ƙirji a tsorace ta ce. "Na shiga uku, wannan ƙofar fa." Salim ya ƙarasa yana goge ƙwalla cike da yaƙe ya ce. "Ɗazu me gyara ya zo duba ta dama can matsala take ba mu, ai mai gyaran yana gidan ma bai tafi ba." Uwani a zuciyarta ta ce.