Sashe 4
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Kai ni fa ban ma yarda da kai ba wallahi, an ya ma kai ba ɗan sandan bogi ba ne? Dubi yadda kake raba idanu kamar shege a rabon gado. Wai ma uban wa ya ce ka jiye mota a ƙofar gidanmu..." Uwani ta haɗiye ragowar kalamanta sakamakon ganin Jafar ya buɗe mota ya fito, ba Uwani ba hatta Salele sai da ya tsorata da yanayin da ya ga Jafar. Uwani a dole don kar ta kunyata kanta ya sa ta cigaba da tsaiwa ta ce. "Ka ga malam tun kashinka bai bushe a hannuna ba ka..."
Ta sake haɗiye ragowar kalamanta sakamakon jin Jafar ya damƙi hannunta da ƙarfin gaske.
"Yeeeh Uwani ta shiga hannun ɗan sanda." Salele ya faɗa da ƙarfi cikin murna yana tsalle, tuni cikin Uwani ya kaɗa. Salele ya ja baki ya rufe sakamakon ganin bindiga saƙale a gefen aljihun Jafar.
Da ƙarfin gaske Jafar ya fisgi hannun Uwani kai tsaye ya wuce cikin gida da ita. Tamkar raƙumi da akala haka Uwani take bin Jafar ƙirjinta na bugawa, zuciyarta na shelar neman agajin gaggawa. Don duk iskancin Uwani tana tsoron bindiga ɗari bisa ɗari.
Lokacin da Jafar ya shiga É—akin Dada babu kowa a ciki, don haka ya wurgar da Uwani gefe fuska a haÉ—e ya ce.
"Maza tashi ki fara tsallen kwaɗo." Uwani jiki na rawa ta fara tsallen kwaɗo sai dai ba ta kai ko ina ba, ta fara hawaye shaɓe-shaɓe. Belt ɗinsa ya ciro yake lafta mata idan ta tsaya, don haka lokaci ɗaya Uwani ta fara fita a hayyacinta. Bayan ta gama tsallen kwaɗo ya saka ta tuƙin babur, da kansa ya gwada mata yadda za ta yi, tana daga tsaye ban da numfarfashin kukan Uwani babu abin da yake ta shi.
"Allah mai yau da gobe, wato yau kukan Uwani nake ji a gidan nan? Tabbas gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, Uwani yau wa kika taɓo wanda ya fi ƙarfinki haka..." Kalaman Dada suka maƙale sakamakon ganin Uwani a ƙobare da ƙafafuwa tana tuƙin mashin. Baki a sake Dada ta ce.
"Ke Uwani wane sabon iskanci ne kuma haka? 'Ya mace da ke ki hau wani ƙobare ƙafafu kuma kina kuka." Uwani jin abin da Dada ta faɗa ya sa ta faɗi ƙasa ta sake fashe wa da kuka.
"Wallahi idan na ƙirga uku ba ki tashi ba sai kin maimaita har da tsallen kwaɗo." Jafar da ke zaune a gadon ƙarfen Dada ya furta fuska a haɗe. A yatsine Dada take kallon wurin ta ce.
"Waye haka kuma da baƙaƙen kaya? Na san dai na ba wa Mamman tarbiyya ba zai yi wannan rashin imanin ba, domin ni musulma ce kuma ina sallah a ɗakina amma dubi garsameman ƙato ya shigo mini da waɗannan takalman kalar na arnan Lagas har cikin ɗakina. Wai Jafaru za ka fito ka cire mini takalmi a waje ko sai na kira ubanka mamman ya fitar da kai?"
"Dada kada ki sake ɓata mini rai!" Jafar ya furta a takaice.
"Ran naka ya fi na ran ƙuda ɓaci, ke Uwani ta shi ki tafi wannan zalinci ba za a yi shi a ɗakina ba. Ni kam wallahi Sa'idu ya gama cutata da ya haɗa mini zuri'a da aikin kaki." Dada ta furta ƙwalla na zuba.
Bindigar aljihunsa ya zaro yana juya ta, ganin bindigar ya sa daga Uwani har Dada suka zabura. Hawaye bibbiyu na bin fuskar Dada ta ce, "Yanzu harbe mu za ka yi Jafaru? Ni kam ko ana sauya muku zuciya daga ta musulmai zuwa ta kafirai a wurin tirenin ne?" Jafar ya sake haÉ—e fuska ya ce.
"Ta kanki zan fara ma, Dada sai yau kika san ana sauya mana zuciya?"
Ganin yadda ya sha kunu ya sa jikin Dada ya fara karkarwa, Jafar ya fara takowa a hankali kafin ya ƙarasa sai gani ya yi Dada ta zube ƙasa a sume. Murmushin gefen baki ya saki, Uwani na ganin haka ta wage baki ta ƙwalla ihu, a daidai lokacin Malam na madina ya kawo kai yana faɗin.
"Wallahi Uwani sai Allah ya yi mana hisabin wannan ihun da kike yi mana babu ji babu gani." Jafar ya hango a tsaye ya mayar da bindigarsa aljihu, yana shirin magana ya hango Dada a yashe a ƙasa.
"Na Madina wallahi Jafaru ne ya sa bindiga zai harbe mu shi ne Dada ta faɗi." Uwani ta faɗa fuska da hawaye shaɓe-shaɓe don ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Ganin haka ya sa Malam na Madina ya yi wani irin ihun da jaruman indiya suke yi, cikin kukan kura ya yi wata irin sufa ya cukumi wuya Jafar haɗe da maƙale shi yana faɗin.
"Wiiiiihuuuuuuhuuuu gafara ga maza nan bisa kanka."
07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA UKU
Ilahirin ƙarfinsa Malam na Madina ya ware yana cakumar Jafar, idan ya dunƙule hannu sai dai ka ji dum! Ya kai masa dundu a baya. Shi kansa Jafar ya yi mamakin ƙarfin dattijon duk da ba fin ƙarfinsa ya yi ba. Na Madina da ya ga ya ɗauki lokaci bai kai Jafar ƙasa ba, ya zuba wata uwar kabbara tamkar wanda yake tsakiyar yaƙin musulmai da arna yana faɗin.
"Allahu Akbar."
Da ya yi kabbara sai ya sauke wa Jafar wani dundu a baya. Uwani na ganin haka ta É—ebo ruwa a randa ta fara yayyafawa Dada, babu jimawa Dada ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ta buÉ—e idonta.
Jafar tun yana ganin dukan da Na Madina yake yi masa wasa ne har ya ga ya cukwikwiye masa wuya, har wani zullo yake yana kabbara yana kai masa duka tamkar mai jifan shaiÉ—an. Jafar ya haÉ—a hannuwan dattijon wuri É—aya ya murÉ—e su sannan ya ce.
"Wallahi Na Madina ko ka sauko daga kaina ko na bi yatsun hannunka É—aya bayan É—aya na tsike su kamar yadda ake tsinkar mangwaro." Jin matsar da Jafar ya yi masa da kuma furucinsa ya sa cikin Na Madina ya karta, yana shirin yin magana ya ji Dada na salati daga kwance.
Tamkar ɗan biri sai ga na madina ya yi tsalle ya faɗo ƙasa, Jafar ya gyara wuyar rigarsa ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ya wuce ɗakinsa da Dada ta sa aka gyara masa. Malam na Madina ya tsugunna a daidai kan Dada ya ce.
"Sannu da farkowa Kulu." Dada ta dube shi luuuu da idanu a shanye sai kawai ta É—aga É—an yatsa É—aya ta ce.
"Ashhadu anla'Ila'ha'illahu wa anna Muhammadur Rasulillah."
Malam na Madina ya sake cewa. "Mun auna arziƙi Dada wannan yaron ashe harbe ku ya so yi?" Dada ta sake yin luuuu da idanu fuskar na Madina na yi mata gizo ta ce.
"Ismi Hauwa kulu wa ana musulima." Jin haka ya sa Na madina ya fashe da kuka, kukan da Dada ta ji ne ya sa ta É—an wartsake sai a lokacin komai ya fara dawo mata. Zumbur ta tashi zaune ta fara bin su Uwani da kallo.
"Uwani kina jin maganata ko kuma da gaske Jafaru ya harbe ni na mutu?" Uwani ta saki dariya ta ce.
"Ina jin ki mana Dada ga Na Madina ma a zaune." Dada ta kalli na Madina suna haÉ—a ido kamar haÉ—in baki suka fashe da kuka a tare.
"Uwani maza É—auko mini wayata."Dada ta furta cikin kuka.
Da sauri Uwani ta É—auko mata don ta san ba ya wuce ta ce a kira mata baba Mamman.
"Maza kira mini Mamman."
Uwani ta karɓi wayar ta gama dube-dubenta sannan ta ce, "Lambarsa ce mai hotan zuciya ko?" Da sauri Dada ta gyaɗa kai. Uwani ta kira tana jin an ɗauka ta miƙa wa Dada.
"Assalamu Alaikum. Hajiya Dadata yau ke ce da kira da kanki..."
"Dakata Mamman! Kiranka na yi ka gaya mini waye shugaban 'yan sanda na duk faÉ—in duniya?" Dada ta katse Baba Mamman a zafafe.
"Shugaban 'yan sanda na duniya? Dada me ya faru kuma?" Ya tambaya a sanyaye.
"Me ye ma bai faru ba Mamman? Ka gaya mini shugaban 'yan sanda na duniya da inda zan same shi, domin a yau ba sai gobe ba wallahi zan ce ya tube Jafaru daga wannan aikin kakin. Kai ni dai Sa'idu ya gama cutata, a ce 'ya'ya duka babu mai aiki ƙwaƙƙwara daga Soja, Rosafti sai Ɗan sabda. Wai kamar ni 'yar limamai jikar limamai ace duka 'ya'yana babu limami ko malamin makarantar allo." Sai da Dada ta fyace majina sannan ta cigaba.
"Mamman ko ka sa a tube Jafaru ko kuma wallahi sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba..."
"Don Allah Dada me yake faruwa?" Baba Mamman ya katse ta hankali a tashe.
Nan take Dada ta zayyane masa duk abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Cikin kwantar da murya ya fara lallashinta har ya samu ta daina kukan sannan ta ce.
"To yanzu Mamman yadda aiki yake wahala, idan aka tube Jafaru daga aikin nan wacce sana'a zai fara? Tsorona Allah tsorona kada ya fara ɗauke-ɗauke, ni dai na san Jafaru da tsoron Allah ko mage ba zai iya kashewa ba, to ko dai a Lagas ɗin nan ya fara 'yan zuƙe-zuƙe ne da ya zo zai harbe mu?" Murmushi baba Mamman ya yi ya furta. "Dada da ya kashe mana ke ai gara a tube shin kawai, amma dai ba na jin Jafar yana shaye-shaye ki bar ni da shi zan kira shi yanzu a waya wallahi ransa sai ya ɓaci." Dada ta ɗan yi jim sannan ta ce.