← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 71

Sashe 53

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Maryama ki daina yi mini godiya domin duk abin da na yi wa Uwani kaina na yi wa. Allah Ya jiƙan Umaru na tabbata yau ko ni na mutu na bar masa iyalina ba za su yi kukan rashina ba, Allah Ya gafarta masa halinsa na gari ya bi shi." Wani abu ta ji ya tsarga mata, musamman da ta tuna kyawawan halaye da ɗabi'unsa. Idanunta suka ciko da ƙwalla jiki a sanyaye ta ce, "Amin Ya Rabbi Yaya, Allah Ya ƙara girma Ya shirya zuri'a." Daddy ya amsa da Amin.

Lokacin da su Uwani suka yi candy cikin Aunty kusan watansa takwas, a wannan lokacin kuma Jafar saura wata É—aya ya dawo gida Najeriya. Bayan kwana biyu da candy É—in su ne kuma Dr Bilal ya turo manyansa aka saka ranar aurensa da Auta shekara É—aya, ita kuma Madina an kawo kuÉ—i amma ba a tsayar da rana ba, saboda saurayinta gini yake yi sai ya kammala za a tsayar da lokacin biki.
Tun da Jafar ya faɗi lokacin dawowarsa Uwani take lissafi zuciyarta fes, don idan ta ce ba ta yi kewarsa ba ta yi ƙarya. Haka kawai idan ta zauna ta tuno irin faɗan da suke da cin zalin da yake yi mata sai ta saki murmushi. A ɓangaren Safna ma zuciyarta fes don ta san Jafar yana dawowa za a ɗebi kwanaki a sha bikinsu, ita kanta Mami burin da take ci kenan. Sai dai Uwani da ta tuna maganar auren Jafar sai ta ji duk jikinta ya yi sanyi, musamman da ta tuna kalamansa na baya da yake faɗa mata cewar Safna ita ce zaɓinsa.

Tun satin da Jafar zai dawo Aunty ta fara yi wa Uwani dafe-dafe da tsimi kala-kala waÉ—anda ta saya a wurin BOJUWA HERBAL'S&SCENTS 08032773332, saboda yadda ta yarda da ingancinsu domin a wurinta take sayan kayan gyara da magungunan sanyi kala-kala.
A ranar da Aunty ta saka Uwani ta a ɗaki ta ba ta wani dafaffan tsimi kurɓa ɗaya ta yi ta ce.

"Aunty ni fa wannan abubuwan wallahi ba wani amfani da za su yi mini, kawai dama ba ki kashe kuɗinki ba." Riƙe da baki Aunty ke kallon Uwani don ta san a wannan lokacin dai Uwani ta gama mallakar hankalin kanta.
"Me ya sa kika ce haka? Ko sakarcin naki za ki yi mini?" Aunty ta tambaye ta tana haÉ—e fuska.

"To Aunty ni fa babu wani abu da ya taɓa haɗa mu..." Da sauri Aunty ta zaro ido waje, ta ɗora kofin a kan mudubi tana salati.
"Uwani ki gaya mini gaskiya ba na son shashancin banza." A kunyace Uwani ta ce. "Allah ni fa da gaske nake." Jinjina kai Aunty ta yi sannan ta miƙa mata kofin da wata gumba ta ce.

"Maza ki shanye shi ki ba ni kofin an jima za mu zauna da ke. Don na lura Uwani sai na cire fuskar Auntyn na ajiye a gefe na yi miki lecture mai zaman kanta sannan za ki dawo daidai." Uwani ta fara shan tsumin tana yatsina fuska don ko kaÉ—an ba ta ji daÉ—insa ba.
Kusan kullin da dabarun da Aunty ke koyawa Uwani na sace zuciyar miji, tun Uwani na jin nauyin Aunty har ta ware wani abin ma take yi mata tambaya idan ba ta gane ba. Ana saura kwana uku Jafar zai dawo aka yi wa Uwani gyaran jikin dilka da halawa, washe gari aka yi mata lalle da gyaran gashi. Auta ban da tsokanarta babu abin da take yi, Mami kuwa zuciyarta a cunkushe take ganin yadda Uwani ta sauya ta yi wani shar tamkar sabuwar amarya.

A ranar da Jafar zai dawo hatta Aunty sai da ta taya Uwani tsara masa abinci, bayan soye-soye har da abin da ya danganci gashi a oven. Wani tsalalelen leshi Uwani ta saka doguwar riga, ta naÉ—a É—aurin É—aukwali sai ga ta fito tamkar a sace ta.

"Malama wannan wankan a rage shi don wallahi kada ki sumar mini da ɗan uwa, na rantse da Allah idan ya ga wannan wankan sai kin susutar da shi!" Auta ta raɗa mata a kunne. Uwani ta yi farr da ido ta ce, "Yarinya ai yau sai dai ki runtse idonki don kada su ƙone ƙurmus, kin san dai shekara guda har da rabi ba banza ba..." Kalaman Uwani suka maƙale sakamakon jin horn ɗin motar Daddy.

"Bari mu ja gefe mu ga kallon masoya, inyeeee yau ango ya dawo." Auta ta faɗa cikin sigar tsokana. Uwani sai murmushi take a ɓangare ɗaya wata irin kunyar Jafar take ji ta lulluɓe, tana daga barandar ɗakin Aunty ta hango fitowarsa daga cikin mota.

Wani irin kwarjini ya yi mata, ya ƙara haske sosai da 'yar ƙiba kaɗan. Ga wani saje da ya tara ba ƙaramin birge ta ya yi ba. Tana yawan mamaki idan ya turo mata hotuna ko idan suna video call, na yadda ya sauya sai a fili ta sake tabbatar da haka.

"Idan kin gama leƙen malama ki fito habibinki yana babban falo." Aunty ta faɗa tana dafa kafaɗar Uwani, kunya ce ta kama Uwani a ɗan kunyace ta ce.

"Wallahi Aunty kunya nake ji." Sakin baki Aunty ta yi ta ce, "Sai ka ce wacce za a kai ɗakin miji yau? Uwani wallahi kika sake kika zubar da huɗubar da na yi miki sai ranki ya ɓaci." Uwani ta yi murmushi Aunty na gaba Uwani na biye da ita a baya.

Shigarta falo ya yi daidai da ɗagowar idabuwansa da suke a yunwace da son ganin ƙwayar idonta, sakamakon jin wani yalwataccen ƙamshin turarenta da ya doki hancinsa. Ya yi matuƙar kewar bakin tsiwarta. Uwa-uba gabaɗaya kyakkyawar fuskarta.
Uwani ta sunkuyar da kai ƙasa, a kunyace ta zauna su Daddy sai jan jafar da hira suke yi ana hirar yaushe gamo. Amsa yake ba su amma hankalinsa yana kan Uwani da take jin ta gabaɗaya a takure. Mami kuwa da gayya ta dubi Jafar ta ce.

"To Jafar wai-wai dai ta ƙare, yanzu sai a zo a saka rana tun da kayan lefe sun kammala kai ma kuma ka dawo gida." Ƙirjin Uwani ya buga dam! Jafar ya ɗan sosa kai a duburburce ya ce. "Ammm... eh dama... na ce dai sai... an kwana..."

"Ai kuwa rannan Uwani take ce mini tana son fitar da ankon wuni, ni leshi ne ko atamfa Uwani?" Aunty ta tsinci kanta da furta haka, don ba ta son Mami ta gane lagon Uwani a ɓangaren kishi. Sai da Uwani ta haɗiyi yawu mai ɗaci ta saki murmushin yaƙe ta ce. "Leshi ne Aunty amma ni ya yi mini arha ina jin mu sauya wani." Uwani ta yi ƙarfin halin faɗar haka. Sam Mami ba haka ta so ba, Jafar ya kafe Uwani da kallo ƙirjinsa na bugawa.

"Yarinyar nan kenan ko kishina ba ta yi da har za ta fitar da anko? An ya ba ni kaÉ—ai nake kiÉ—a da rawata a kanta ba?" Jafar ya ayyana a ransa.

"Jafar ya kamata ku ƙarasa sashenku ka yi wanka ka huta ko?" Daddy ya katse shirun. Yana gama magana, Mami ta shige ɗaki fuuuu Daddy ya saki murmushi don ya fahimci salon Mami tun farkon maganarta, da yadda Aunty ta sauya akalar maganar.

Hanyar fita ya nufa Aunty da Daddy kowanne ya shiga sashensa, Uwani ta yi saurin bin Aunty idanunta sun ciko da ƙwalla.

"Au abin da take son aiwatarwa a kanku kina nufin za ki ba ta dama ta yi nasara a kanki ne? Bari ki ji, sirikarki da biyu ta tsiro maganar auren Jafar saboda ta lalata farincikin da kuke ciki. Maza ki goge hawayenki ki wuce ki tarairayi mijinki don na san ya yi kewarki, kuma saura anjima na ga ƙafarki a nan don ko Auta na ce ita da shiga sashenku sai bayan kwana uku. Na san kafin lokacin an gama cin amarcin..." Uwani ba ta gama jin maganar Aunty ba ta fita da gudu saboda kunya, lokacin da ta sauka tuni har ya shiga sashensu. Tana shiga falon ganin baya ciki ta fara waige alamar nemansa, ta baya ta ji ya rungumota kusan lokaci ɗaya suka sauke ajiyar zuciya. Jafar ya cusa kansa cikin wuyanta ya fara sakar mata kisses, cikin tsantsar soyayya da kewarta.

"Ya Jafar!"
Uwani ta furta cikin wata irin murya. Bai amsa mata ba sai ma ƙira tura kansa da ya yi cikin wuyanta yana shaƙar ƙamshin turarenta, a hankali ya juyo da ita suna kallon juna ta yi saurin sunkuyar da kai ƙasa.

"Laifin me na yi da ba a yi mini sannu da zuwa ba?" Uwani ta yi murmushi ta ce, "Ni fa kunyar su Daddy na ji." Bin ta yake da kallo yana mamakin sauyinta, komai na Uwani ya sauya tamkar ba ita.

"Bakin tsiwa kin ƙara girma!" Da sauri ta cusa kanta a ƙirjinsa ta ce. "Ni fa ba na so wai ƙare mini kallo ka yi dama." Jafar Ya shafo fuskarta ya ce.

"Da gaske komai na ki ya sauya, sai dai ban sani ba ko halinki na ƙiriniya da tsiwa yana nan?" Uwani ta saki murmushi a ranta ta ce. "To dama mai hali yana fasa halinsa ne?" A fili kuma ta ce.

"Ya Jafar ga ruwan wanka fa ya kamata ka yi wanka ka huta."
"Mu je ki taya ni..."
Ganin yadda Uwani ta zaro ido waje haÉ—e da ja baya ya katse maganarsa yana dariya.

"Na ga alamar kunyar nan za ta hana ni rawar gaban hantsi dai, amma zan yi maganinta." Uwani tana ji ba ta tanka masa ba, Jafar ya shiga ɗaki ya rage kayan jikinsa. Lumshe ido ya yi yana shaƙar ƙamshin turaren don ba ɗaramin daɗi ya yi masa ba. Kiran Safna ne ya shigo wayarsa, da sauri ya saka wayar a silent sannan ya tura mata sakon yana zuwa daga ƙarshe ya kashe wayar gabaɗaya.
Chapter 53 · 0% Book details