Sashe 35
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Uwani ta juyar da kanta gefe har lokacin hawaye take yi, Jafar ya sake zagayowa ta gabanta ya ce. "Ba tambayarki nake ba?"
"Ni ma ai tambayarka na yi me ya sa ka korar mini saurayi?" Riƙe baki Jafar ya yi yana mamaki, yana shirin magana ya ji ta ci gaba da cewa.
"Kai ma fa warewa ka yi a wuri daban kai da budurwarka kuna hira, ni ma ba sai ka bar ni na yi sabgar gabana ba." Ran Jafar a ɓace ya furta, "Da aurena a kanki ba ki isa ki yi mini wannan iskancin ba, sai ki bari ranar da na sauke igiyoyina uku daga kanki sai ki je can ki kula duk wanda za ki kula. Kuma ki tashi ki koma ciki ba na buƙatar ganinki a nan." Uwani yi ta yi kamar ba ta san me Jafar yake faɗa ba, ya sa hannu ta ƙarfi ya fiszo ta har ta kusa faɗawa kansa. A daidai lokacin Safna ta ƙarasa wurin don ta ji Jafar shiru bai koma ba, ganin abin da Jafar ya yi wa Uwani ya sa ƙirjinta ya buga da ƙarfi. A ɗan hargitse Safna ta haɗe fuska tana faɗin, "Baby me kake yi haka? Wace ce wannan?"
Uwani ta wurga mata harara sannan ta ja tsaki, Jafar na shirin magana daga gefe suka ji Maimuna 'yar wurin Baba Mustafa ta ce. "Amaryarsa ce wataƙila sarautar ce ta motsa ya biyo ta yake lallaɓarta, kin san dramar Ya Jafar da Uwani ba ta ƙarewa. Ni ban san ma yadda zamansu yake ƙarewa ba, don wallahi na san watarana sai su cinna wa gidan wuta." Maimuna na gama maganar ta yi gaba tana murmushi, don ita sam ba ta san wace ce Safna ba. Uwani ta fisge hannunta daga jikin Jafar ta dubi Safna ta furta. "Sai ki yi nazari domin ganin buzu a masallaci ya ishi tinkiya ta yi hankali." Daga haka Uwani ta wuce ko waigensu ba ta sake yi ba.
Safna ce ta ƙura wa Jafar ido da kallon tuhuma ta furta, "Wace ce wannan yarinyar? Kuma me ye alaƙarta da maganar da waccen ta faɗa?" Jafar ya ɗan saita nutsuwarsa ganin zancen da Maimuna ta faɗa bai shigi Safna ba, ya sakar mata murmushi ya ce. "Cousin ɗina ce, yarinyar ba ta da kunya and akwai wani yaro ɗan iska ne da iyayenmu suka hana ta kula shi. Ina fitowa nagan su a zaune suna hira, a kan na kore shi take neman ta yi mini rashin kunya. So kar ki damu da maganar Maimuna duk irin wasan abokan wasa ne ita ma cousin ɗina ce." Sai a lokacin Safna ta sauke ajiyar zuciya, ta ɗan saki murmushi ta furta. "Dama maganarta ba ta wani dame ni ba, because i trust you. Na san ko girlfriend ba ka da ita, to ma ta ya har za ka iya rayuwa da wata macen ba ni ba." Jafar ya yi saurin gyaɗa mata kai sannan suka koma ciki.
Jafar tun da ya zauna hankalinsa na wurin Uwani don ya san yarinyar ba ta da hankali tsaf sai ta fita ta je ta kula samari a waje, har sai da Safna ta lura hankalinsa kamar yana wani irin.
Uwani na shiga ta wuce wurin Mami ta ɗan sunkuya wurin kunnenta ta ce, "Mami wani ƙaton mutum mummuna a gate ya ce wai a kirawo ki zai yi miki fatan alheri." Rass! Gaban Mami ya buga, duk AC da ke wurin bai hana gumi ya keto mata ba. Ta yi ƙasa da murya ta ce, "Wane iri ne mutumin? Kuma kin tabbata abin da ya ce miki kenan?" Uwani ta gyaɗa kai ta ce, "Ni fa surarsa tsoro ta ba ni, yatsun hannuwansa bibbiyu ne fa. Ga shi saman tsakiyar kansa na ga har hayaƙi yake yi!" Da sauri Mami ta ce hayaƙi?" Uwani ta gimtse dariyar ta haɗe da gyaɗa mata kai.
Ƙawayen Mami da ke wurin jin abin da Mami ta faɗa ya sa gabaɗaya suka ce, "Hayaƙi kuma? Me ye yake hayaƙi?" Uwani za ta yi magana da sauri Mami ta katse ta da cewar, "Wai bayan fitowarmu daga gida ne aka ga kitchen yana hayaƙi, amma Daddyn yara ya kashe dama gas ne ashe ba a kashe ba abinci ya fara ƙauri." Gabaɗaya suka furta, "Alhamdulillah, Allah Ya kiyaye gaba."
Mami ta riƙe hannun Uwani suka tashi daga wurin sai da suka matsa daga wurin mutane sannan ta furta, "Maza koma ki zauna kuma kada ki faɗa wa kowa wannan maganar." Uwani ta bi Mami da kallo ganin yadda take kwantar mata da murya, Uwani ta koma mazauninta tana ci gaba da 'yan kalle-kallenta tana murmushi ƙasa-ƙasa.
Auta ce ta ƙarasa wurinta ta ce, "Uwani ina kika je ne? Ki zo mu je mu yi rawa." Da kamar Uwani ta noƙe sai kuma ta bi Auta suka shiga cikin fili suka fara takawa a hankali, wani abokin Salim ne ya shiga ya fara yi wa Auta liƙi. Babu jimawa wani ma ya shiga ya fara yi wa Uwani liƙi, ganin irin kuɗin da suke zubarwa a kan Auta da Uwani ya sa Mc ya fara koɗa su yana faɗin.
"A gaskiya wannan biki ya yi albarka, ga wasu abokan ango nan suma da alama sun yi kamun matan aure." Wani irin tuƙuƙin ɓacin rai ne ya mamaye Jafar, musamman da ya ji kalaman Mc. Ita kuwa Uwani ko a jikinta sai juyi take tana sakin murmushi. Sai da Uwani ta gaji don kanta sannan ta ja hannun Auta suka fita daga cikin filin, Muhsin ne ya biyo Uwani yana neman lambar wayarta. Nan take Auta ta shaida masa tana da aure, ba don ya so ba haka ya koma ya je ya zauna.
Uwani na daga zaune ta bi ƙaton cake ɗin amarya da ango da kallo, ya ƙwayatu sosai kuma a tsaye ya kusa tsayinta don da gani an narka dukiya a jikinsa. Ta waiga ta hangi yadda Mami ke washe baki cikin farinciki. A fili Uwani ta furta, "Ya zama dole taron nan ya watse yanzun nan." Miƙewa ta yi ta kira Auta ta ce ta raka ta za ta yi fitsari, Humaira da Na'ima ƙawayen Auta suka ce za su raka ta don ita ma Na'ima fitsarin take ji.
A ɗan zagayen hall ɗin banɗakunan suke guda uku a jere, sai dai wurin duhu gare shi ba kamar can wurin da mutane ke zirga-zirga ba. Daga ɗan baki-baki su Auta suka tsaya Uwani da Na'ima suka ƙarasa, Uwani dama babu wani fitsari da take ji kawai don ta tashi wurin da ƙura ne. Tana shiga banɗakin ta ƙwalla ƙara tana faɗin.
"Wayyo kunnuwana! Auta suna fisgar ƙafata, wai kunnuwa za su cire. Sun ce duka sai sun fige kunnuwan mutanen wurin nan." Uwani ta fito daga banɗakin a guje tana doka ƙauren banɗakin da Na'ima take ciki. Tun Uwani ba ta gama ihu ba Auta da Humaira suka zuba a guje, Na'ima na jin haka ta fito a guje wando na saɓulewa don ko fitsarin ba ta gama ba ta ji ihun Uwani da abin da take faɗa. Sai da Uwani ta ga sun shige sannan ta yi tsalle ta sauke fiyus ɗin wutar wurin, ta kuma ƙarasa can bakin ƙofar hall ɗin da gudu a cikin duhu ta laluma ta tura ƙofar shiga hall ɗin ta datse ta.
Lokaci ɗaya hall ɗin ya kacame da ihu masu kuka na yi masu kiran sunan Allah na yi. Mami kuwa dama tun lokacin da wutar wurin ta ɗauke take sakin fitsari ba ji ba gani, Uwani kuma ta fara bi tana gasa wa mutane mintsini wasu kuma sai dai ta sa takalminta ta wanka musu mari da shi. Sai dai ka ji ƙato ya zuba ihu yana cewa, "Wayyo sun mare ni."
A haka ne Uwani ta É—aga takalmi ta tafkawa Salim a fuska, cikin tashin hankali da galabaita ya furta, "Wayyo Allahna Shukra kin cuce ni, sai da na ce ba zan zo ba kika tilasta mini ga shi yanzu suna zo yage naman fuskata."
Securities ɗin wurin ne suka buɗe ƙofar da ƙarfi ganin abin da yake faruwa ya sa suka fara haske-haske, ɗaya daga cikinsu ya zagaya ya ɗaga fiyus ɗin wutar lokaci ɗaya haske ya mamaye cikin hall ɗin.
Kallon kallo kowa ya tsaya yana yi ganin yadda suka hargitse lokaci ɗaya, Jafar na ɗagowa ya gan shi saƙale a jikin Hajiyan Safna ga jakarta rataye a saman kafaɗarsa ta zagayo ta cikin kansa. Da sauri ya ja da baya a kunyace, ita ma Hajiyan Safna ta matsa gefe saboda kunya kamar ta nutse a ƙasa.
Da Mami da Salim sai kallon juna suke ganin yadda suke dame fuskokinsu da zungureren cake ɗin amarya da ango, jin sanyi-sanyi a kan Mami ya sa ta kai hannu sai ji ta yi ta kwaso wani lafcecen cake a saman kanta. Tana waigawa ta hango gwaggwaron kanta ya yi cokoko a saman cake ɗin, Shukra kuma na maƙale da Mc sai da ta dawo hayyacinta ta diro daga bayansa, don shi ma bai san ya saɓa ta a baya ba saboda tashin hankali. Uwani na ankare da su ɗaya bayan ɗaya, ganin har lokacin a firgice suke ya sa ta manna a guje tana faɗi. "Ga su nan, ga su nan sun fara jan ƙafafuwan mutane, wayyo Allah ƙafata!" Ta yi hanyar gate a guje, ai kuwa a guje mutane suka rufa mata baya. Salim yana gudu babbar rigarsa na taɗe shi shi da abokansa, ita kuwa Shukra kafin ta je bakin ƙofa faɗuwar kusan biyar tana tashi. Mami ba ta jira ɗaukar ɗankwalinta a kan cake ba ta fita a guje zanin jikinta na ƙoƙarin kuncewa.
Littafin kuÉ—i ne idan kina buÆ™ata za ki biya 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wanaan layin 07062062624 idan littafi ya kammala cmplt doc 800 neðŸ«
#Ummou Aslam Bint Adam🌚