← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 71

Sashe 28

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankali a tashe Dr Nura ya shige can kusurwar É—akin yana faÉ—in.
"Help! Help! Help!" Mami ta sake zungura masa ƙarfen tana faɗin.

"Wato don ubanka har surar Nasara kake rikiɗewa ai wallahi yau ko ni ko kai." Dr Nura ganin neman agajin da yake yi da harshen turanci ba zai kai shi ba, ya sa ya taƙarƙare cikin ihun tashin hankali ya ce. "Wayyo Allah! Jama'a Patient ɗin nan za ta halaka ni."

Su Daddy na daga waje suka jiyo ihun Dr Nura, da gudu suka taho za su buɗe ƙofar, sai dai da yake Mami na jingine da ƙofar tana jin alamun za a buɗe ta sake danna ƙofar da ƙarfi tana zungurin Dr. Ganin Mami na niyyar illata shi ya sa ya faɗa ƙarƙashin gadon asibitin, da ƙyar su Daddy suka turo ƙofar suna ganin ta da ƙarfen suka shiga kallon-kallo suma suna ja da baya. Daddy ne ya murɗe hannun Mami ya karɓe ƙarfen ya ajiye, sororo ta yi ta fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce.

"Daddyn yara da gaske kune? Ina ne nan?"

Kafin Daddy ya ba ta amsa tuni Dr Nura ya yi wata irin sufa irin ta jaruman indiya ya fice daga É—akin, glass da takalmansa kusan lokaci É—aya suka yi tsalle sama suka zube a tsakar É—akin sai dai hakan bai sa ya tsaya ko waige ba ballana ya É—ebi abin sa.

Kan gado Daddy ya zaunar da ita yana yi mata sannu, sai ji suka yi ta fashe da kuka tana faɗin. "Daddyn yara ni dai daga nan ka wuce Kura da ni, har abada ba zan sake kwana a gidan can ba." Kamar ƙaramar yarinya Daddy ya shiga lallashinta sai da ta yi shiru sannan ya tambaye ta ainihin abin da ya faru.

Tiryan-tiryan Mami ta sanar da shi abin da ta ji da kuma shigowar ƙadangaren, don ita ko shigar su Jafar ba ta sani ba saboda ta yi suma ya fi bakwai a cikin banɗakin. A yanzu shi kansa Daddy ya fara yarda da cewar gidan ba su kaɗai ba ne, saboda ya sake kwantar mata da hankali ya ce ya amince za su koma can da zama. Uwani na rakuɓe a gefe ta yi zuru tana ƙarewa fuskar Mami kallo, tana mamakin yadda Mami ta zabge ta zuƙe a wuni guda, suna haɗa ido ta doko mata harara ba shiri Uwani ta janye idonta gefe.

Daddy da kansa ya koma kiran likitan da zai sake duba Mami duk da ya lura ciwon ba na asibiti ba ne, da ƙyar ya samu Dr Samira ta je ta duba Mami ta saka mata ƙarin ruwa da allurai bayan wani lokaci aka sallame ta. Su Shukra ko kaɗan ba su so komawa Kura ba don dai babu yadda suka iya ne, ita kuwa Uwani murna fal ciki. Daddy ne ya kwashe su suka ɗebo kayan sakawarsu. Mami kuwa fir ta ƙi yarda ta shiga gidan sai a mota suka bar ta.

Su Shukra sun ɗauki hanyar Kura babu jimawa Salim ya kira ta a kan zai je ya ɗauki motarsa, bai dai gaya mata ba amma a cikin ransa ya ƙissima ba zai sake zuwa gidansu ba har zuwa lokacin da za a ɗaura musu aure.
Adaidaita sahu ne ya sauke shi a ƙofar gidan Daddy, gaban Salim ne ya fara faɗuwa a hankali ya yi ta maza ya ƙarasa jikin gate ɗin ya fara ƙwanƙwasawa. Daga cikin gidan Lado ya furta.

"Waye nan?"

"Lado ni ne." Zuro kai Lado ya yi yana ganin Salim ya washe baki ya ce, "Allah Ya taimake ka, yau kaine da rana tsaka." Salim ya miƙa masa mukullin motarsa ya ce.

"Shiga ka tuƙo motata ka fito mini da ita." Sororo Lado ya yi ya furta. "Ranka ya daɗe ni da ko mashin ban iya tuƙawa ba, ina ni ina tuƙa mota?"

"Lado amma gidan nan ba ku kaɗai ba ne a ciki, ka na gani dai rannan aka so tafiya da mu a bokiti ban da ƙarfin addu'armu da ta iyaye da tuni wani zancen ake ba wannan ba." Lado ya yi jim sannan ya ce.
"Ranka shi daɗe naka ai mai sauƙi ne." To yau dai in faɗa maka tik da ka sani haka ƙadangare ya tarfa Hajiya tumɓur tana wanka. Kai yanzu haka ma suna can hanyar Kura don gabaɗaya Hajiya ta rikice, ban da sha'anin iska ina ka taɓa jin ƙadangare ya auri mutum? Wai ƙadangare ne fa yake ce mata amarci zai sha da ita, ina ka taɓa ganin ƙadangare na magana?To Kai kuwa ma a shekarun Hajiya ban da neman cika wa da imani me take nema a wurin namiji ballantana ƙadangare? To ɗazun nan sun zo ɗiban kaya za su wuce Kura Uwani ta kwashe komai ta faɗa mini." Take cikin Salim ya sake kaɗawa, ganin ya ɗan fara ja da baya Lado ya ce.

"Ni ma fa Baffa nake jira ya zo a yi wacce za a yi, idan har ƙadangare zai auri Hajiya ni waye da ƙangaruwa ba za ta aure ni ba. Haka kawai ina zaune ta murƙushe ni cikin dare babu mai ceton rai." Salim ya zaro ido ciki a tsure ya ci gaba da ja baya. Lado ganin haka ya sa ya ce.

"Ranka shi daÉ—e ina za ka je ne? Ka shigo ka É—auki motarka mana." Salim ya zabura a razane ya furta.
"Allah Ya tsare ni wallahi, zan aiko a É—aukar mini ita daga baya don ita kanta motar kafin na fara hawa sai an yi mata sauka biyar." Daga haka Salim ya juya ko sallama bai yi wa Lado ba yana zuba sauri.

Da zuwan su Mami Kura ba a É—auki lokaci ba, labarin abin da ya faru da ita ya watsu cikin gidan gabaÉ—aya. Facalolinta sai zuwa suke duba ta, wanda yawanci zuwan da suke yi da biyu suke yi. Domin masu yi mata dariya a bayan fage sun fi yawa saboda irin habaicin da ta dinga yi musu a lokacin da za su tare. Sai daga baya Dada ta shiga a lokacin yawancin mutane sun watse daga Daddy sai su Jafar, Uwani kuwa dama tun da ta shiga gidan ta yi sashen Dada daga nan ta wuce wurin turken awakinta.

Sannu a hankali jikin Mami yake ƙara samun sauƙi, ganin yadda Mami ta yi laushi ya sa Uwani ta yi tsammanin ko Mami sauya halinta ne. A haka sai da suka shafe kusan kwana goma a cikin gidan, kuma a wannan kwanakin kullin sai Daddy ya sa an yi saukar karatun Alƙur'ani. Wannan saken da Uwani ta samu ya sa hankalinta ya kwanta, ta manta da matsalar Mami gabaɗaya. Don tun da suka koma Kura sau biyu ta shiga duba Mami, kuma ba wata kyakkyawar fuska take samu ba.

Su Mami ba su suka koma gidansu ba sai bai fi saura sati guda bikin Shukra ba, da ƙyar Mami ta yarda ta koma kuma kafin ta koma sai da suka yi musayar ɗaki da Daddy, ita ta koma ɗakin Daddy shi ya koma ɗakinta. A kwalemar fitar da kayan ne aka fitar da Jangwalagwadan da ya shiga ɗakinta, don shi kansa ya galabaita. A lokacin da za su tafi ne Uwani ta saka kuka don cewa ta yi fir ba za ta koma ba, sai da Dada ta lallaɓa ita da Daddy ta amince amma sai cewa ta yi sai dai idan da awakinta za ta koma. Ba musu Daddy ya amince ya ce zai yanki wani wuri a cikin farfajiyar gidan a yi wa awakinta wuri, amma sai bayan bikin su Shukra. Cikin farinciki Uwani ta bi Jafar suka wuce duk da shi ma ba wata fuska take samu a wurinsa ba, amma ba ya zagin ta ko cin zarafin ta.

Shirye-shirye sun fara kankama a wurin su Mami da wurin iyayen Salim, da yake Mami na zirga-zirga sai tsangwama da takurar da take yi wa Uwani ta yi sauƙi. Haka kuma Uwani ta fara gogewa da aikin da suke yi da Inna, don wani lokacin ma idan Inna ta gaya mata yadda za ta sarrafa abu ita take yi.

Tun ana gobe kamun bikin Shukra hankalin Mami yake a tashe sakamakon wayar da suka yi da mahaifiyar Safna, a kan cewar za su zo ranar Juma'a da safe su tafi ranar Lahadi bayan É—aurin aure. Sakamakon biyo jirgin da za su yi daga Lagos zuwa Kano.
Tun da suka gama wayar gumi yake keto wa Mami. Ganin ta rasa mafita ya sa ta kira Shukra É—aki.

"Shukra ina tsoron asirinmu ya tonu, ina gudun duk plan ɗin da na shirya ya wargatse. Kin san dai matuƙar Safna da mahaifiyarta suka zo gidan ko yaya ne za su iya fuskantar Jafar na da aure, alhalin ni kuma ban sanar da kowa ba bayan Hajiya Falmata." Shiru Shukra ta yi sannan ta ce.

"Hanya É—aya ce, mu nemo abin da zai sa Yaya ya sake ta kawai."
"Ta wace hanya kenan?" Shukra ta zuba tagumi tana nazari, da sauri ta dafa Mami ta ce.

"Na samo mafita, kin san me za a yi Mami?" Mami ta girgiza kai da sauri.
"Sata kawai za mu laƙa mata, ba kin ce Daddy ya ba ki ajiyar wasu kuɗi masu yawa ba? To da su za mu yi amfani." Shukra ta yi ƙasa da murya tana tsara wa Mami yadda za su yi, lokaci ɗaya suka saki dariyar samun mafita.
Chapter 28 · 0% Book details