← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 71

Sashe 15

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wuni ɗaya da Uwani ta yi a gidan ta fahimci irin zaman ƙuncin da mahaifiyarta da kishiyarta suke yi a cikin gidan, a kan idonta ta ga Aramma ya yo cefane har da nama ya ce a yi masa jar miya da shi. A yadda ta lura hatta abinci ma daban ake yi masa, su kuma duk kwamacalar da ya ga dama sai su dafa. Don abincin dare sai da ƙyar Uwani ta iya cin miyar kukar da aka kaɗa, saboda haka ta ci alwashin gyara masa zama kafin ta bar gidan.

Tun da doshin magriba Uwani ta hangi wani ludayin silba a kwandon wanke-wanken mahaifiyarta, a fakaice ta ɗauke shi ta ɓoye sai da dare ya tsala kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki a hankali. Har za ta fita ta hangi wani zumbulelen farin hijabin Inna Suwaiba, wani tunani ne ya faɗo mata da sauri ta saki murmushi. Ta figi hijabin a hankali ɗayan hannunta ɗauke da ludayin sulba, can hanyar soro ta nufa da yake a baki-bakin ƙofa turakar Aramma take, daga ɗakinsa kuma sai ɗakin da suke ajiye kayan abinci. Toka ta ɗiba ta bursune fuskarta da ita sannan ta saka zumbulelen farin hijabin, ta leƙa ɗakin ta hango Aramma a kwance ya sharɓe sai sakin munshari yake yi daga shi sai gajeren wando. Da yake irin mutanen nan gajeru masu ƙiba ga uban tumbi. Tana shiga ɗakin ta tsaya a kansa, sai da ta gimtse dariyarta sannan ta daidaici gefen goshinsa ta ba shi raaaal da ludayin hannunta. A firgice Aramma ya miƙe yana dafe da goshi, "Wane ɗan iskan ne a tsohon daren."

"Tawagar fatalwar 'yan iskan lahira ne!" Uwani ta faɗa da wata irin murya, ta sa hannu ta cikin hijabin ta buɗa shi, sai ta ƙara faɗi ta cikinsa. A razane Aramma ya ja da baya ganin hallitar da ke tunkaro shi.

"Mu sababbin ƙawayen 'yarka da ta baƙunci lahira ne. A cikin fatale ma mu tawagar shaiɗanu ne domin fatattaka ɗan adam muke yi da kulkin lahira. Ita da bakinta ta gaya mana irin zalincin da kake yi wa iyalinka, don haka muka zo domin mu tsintsinka hanjin cikinka, ko kuma mu gayyato 'yan uwanmu mu yi daga-daga da kai." Uwani ta yi magana tana wani miƙa wuya gaba.

Jin kalaman Uwani ya sa Aramma ya fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, cikin tashin hankali ya ce.
"Ku dubi Allah ku yi haƙuri wallahi zan daina duk abin da nake yi..." Da sauri Uwani ta katse shi.

"Zo nan maza-maza, matso nan."

"Don Allah ku yi mini rai." Aramma ya faÉ—a fuska haÉ—e da hawaye da majina.

"Za fa ka taka ɗan tsiti a bayanka, wallahi tawagarsa ta fi ta mu bala'i ka matso na ce maka." Da sauri Aramma ya matsa tiɓi-tiɓi sai haɗa gumi yake. Yana zuwa ya tsugunna a ƙasa, hannun Uwani mai ɗauke da ludayin da ke cikin hijabi ta ɗaga da sauri ta sake ba shi raaal a ƙeyarsa. A zabure Aramma ya miƙe sai da ya yi tsalle uku ya faɗi a can gefe cikin azaba.

"Fatalwar 'yarka ta gaya mana duk abin da matanka suke samu karɓe musu kake yi, a jiya ma ka karɓe wa uwar marigayya kuɗaɗenta to ko ka mayar mata da abin ta ko kuma mu mayar da kai kuɗi. Domin muna cikin irin fatalwar da ke yi wa 'yan ƙungiyar asiri aiki, za ka zama kuɗi wayyo kuɗi, kuɗi masu daɗi." Uwani ta yi maganar tana wani tsalle tana ɗaga hannu ta cikin hijabi kamar mai shirin tashi sama.

"Na rantse da Allah ko wasu aka ce na ƙara mata yanzu zan ƙara mata su." Uwani ba ta bi ta kansa ba ta ce.

"Da ma ga hantarka da zuciyarka nan muna gani manya ne, ko su kaɗai muka tsaface za ta kawo mana miliyoyi." Da sauri Aramma ya dafe cikinsa da hannuwansa biyu, ya sake ɓarkewa da kuka.

"Idan ka sake ka tona mana asiri wallahi a yanzu za mu hallaka ka." Jin haka ya sa Aramma ya haɗiye kukansa, ya sa hannu biyu ya toshe bakinsa. Uwani ta sake jingina da bango ta furta. "Ganin yadda muka ga ka yi nadama za mu ɗaga maka ƙafa na kwana biyu mu ga idan za ka sauya halinka, kuma ka gaggauta mayarwa da mahaifiyar 'yar uwarmu kuɗinta. Sannan ita da kishiyarta dole ne ka ƙara musu dubu hamsin-hamsin. Kuma ya zama wajibi duk sati ka dinga ba su dubu uku-uku na kashewa."

"Duka na ji kuma na yi alƙawari zan yi yadda kuka ce, na gode muku Allah Ya biya ku." Aramma ya yi maganar yana rissinawa.
"Ba ma buƙatar godiya, yanzu dai za mu tafi da kai ka je ka ga makwancin 'yarka, sai mu baro ka a can bayan sadakar uku sai mu dawo..."
Tun Uwani ba ta gama magana ba ya katse ta cikin kuka.

"Wallahi na haƙura da ganin ta, Allah ba sai na ga halin da take ciki ba. Na san mai sunan Iya tana da halin na gari."

"To kuwa ya zama wajibi ka zaɓi ɗaya, ko mu ɗauke ka ta ƙarfin tsiya mu tafi da kai. Ko kuma ka zo ka ku yi sallama da shugabar tawagar 'yan iskan fatale." Jin haka ya sa jiki na rawa ya matsa gaban Uwani ya ce.

"Zan gaisa da ita..." Maganar bakinsa ta katse sakamakon jin saukar ludayin da ya yi a gaban kansa. Wannan karon kasa motsi ya yi ganin haka ya sa Uwani ta sake sauke masa na biyu aka sannan ta É—ora da cewa.

"Yanzu haka za mu fita mu ba ka wuri, sauran tawagarmu na tsakar gidan nan. Kuma duk abin da ka ji ko kuma duk hukuncin da ka ji muna aikatawa matuƙar ka leƙo to zai dawo kanka. Sannan saura idan gari ya waye ka ce ga abin da ya faru da kai." Daga haka Uwani ta fice tana wani shagiɗewa gefe tana tura wuya gaba.

Kusan duk abin da ya faru tsakanin Uwani da Aramma, Yaya ƙarama da su Rahane 'yan uwan Aramma sun ji, sakamakon ɗakin da suke kwance a jikin na Aramma yake. Da yake dama idan wani abin taro ya kama a gidan to duka danginsa a wannan ɗakin suke sauka. Kowannensu na daga kwance cikinsa ya ɗuri ruwa ko motsin kirki babu mai yi, babban abin da ya ɗaga hankalinsu yadda suka dinga jiyo kukan Aramma ƙasa-ƙasa, da ita kanta saƙon fatalwar da take faɗa. Suna nan kwance suka ji motsin Uwani a ƙofar ɗakinsu tana ɗan wani gurnani, take fitsari ya jiƙe zanin Yaya ƙarama. Uwani na ɗaga labulen ɗakin ta hango yadda aka jere yara a ƙasa, ɗaya bayan ɗaya haka ta dinga jidar yaran tana kai wa tsakar gida. Yaya ƙarama na daga kwance ta ji Uwani ta dafa ƙafarta, jiki na rawa ta ce.

"La'ilaha'illahu Muhammadur Rasulillah."

"Ba za ki mutu yanzu ba sai mu fafe ƙwayar idonki." Uwani ta faɗa da wata irin murya, har ta juya za ta fita ta ce. "Su kuma waɗancan yaran zan ba wa ƙananan fatalenmu umarni su gama da su." Uwani na ƙarasa magana ta wuce wurin yaran da ke kwance a tsakar gida, idan ta ɗauko yaro ɗaya sai ta gasa masa mintsini ta tura shi cikin ɗaki. Ganin yadda yaran ke shigowa a firgice cikin kuka ga magagin bacci ga kuma zafin mintsini, ya sa su Yaya ƙarama suka banka uwar ɗaki a guje. Uwani ta yi wata irin sufa ta rufa musu baya tana faɗin. "Ya Ahalul fataleeee ku zo ga nama mun samu."

07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

SHAFI NA TARA

Sai a lokacin Uwani ta fahimci ashe ba iya su Yaya Ƙarama ce kaɗai idonsu biyu ba, hatta mutanen da ke cikin uwar ɗakin lakur suka yi sai da suka ji Uwani ta yi sufa za ta faɗo uwar ɗakin suka fara ihun neman ceton rai. A daidai bakin ƙofar uwar ɗakin Uwani ta tsaya sai ta hango wata wuƙa a gefen randa, ta janyo ta ta fara wasawa. Naziru ɗan wurin Sa'a da a lokacin ya wartsake ya kafe Uwani da kallo, ganin haka ya sa Uwani ta kalle shi tana zare ido ta ce.

"Ga wani ɗan ƙwage da shi za mu fara." Uwani ta ƙarasa maganar tana fusgar hannun Naziru da bai wuce shekara huɗu ba.

"Wayyo Iyata! Wayyo Iyata." Ya fara ihu hankali a tashe don ƙiri-ƙiri ya ga wuƙar hannun Uwani. Sa'a na ganin haka ta fara jan hannun Naziru Uwani na jan ɗaya, Sa'a ta waiga wurin su Yaya ƙarama ta ce. "Ƙarama don Allah ku kawo mini ɗauki Naziri zai tafi."

Yaya ƙarama da ke ƙuryar uwar ɗaki ta ce. "Sa'a ki haƙura da Naziru tun da ba wuce haihuwa kika yi ba, wallahi a yanzu ko Habibu (Shi kaɗai ne ɗanta) suka ja sai dai na bi shi da addu'a." Sa'a na shirin magana Uwani ranƙwala mata ludayi a ka, a guje ta saki hannun Naziru cikin kuka ta faɗa uwar ɗakin tana faɗin.

"Wayyo Naziru."
Shi ma Naziru sai tirjewa yake yana faɗin. "Iyata wayyo Iyata." Yaya ƙarama ce ta yi sauri ta banka ƙofar ɗakin ta danna sakata tana sauke ajiyar zuciya.
"Idan kun rufe ƙofa za mu ɓullo ta ƙarƙashin ƙasa, mu dama ai daga kabari muke. A wannan lokacin babu buƙatar mu yi muku bayanin mu su waye, domin hukunta ku muka zo yi ɗaya bayan ɗaya, a kan cin zarafin da kuke yi wa mahaifiyar 'yar uwarmu da kishiyarta. Mu tawagar fatale sai mun saɓule fatar jikinku sannan mu tsotse romo da ɓargon jikinku. Amma za mu ɗaga muku ƙafa zuwa nan da ɗan wani lokaci, don mun lura kun fara nadama. Sai dai muna mai tabbatar muku babu wanda zai tafi gidansa sai an yi sadakar uku, idan kuma mutum ya yi kuskuren tafiya gida gobe, to a daren ranar sai dai ya kwana a ƙiyama."
Chapter 15 · 0% Book details