← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 71

Sashe 54

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan ya yi wanka ƙaramar riga ya saka da wando 3 quater, a falo ya samu Uwani tana zaune tana ganinsa ta sakar masa murmushi sannan ta fara zuba masa abinci.
A kusa da Uwani ya zauna ya shagwaɓe fuska yana faɗin, "Na yi kewar girkin nan na ki." Murmushi ta sakar masa Jafar ya buɗe baki, a kunyace Uwani ta fara saka masa yana ci har ta ɗan saki jikinta. Sannu a hankali shi ma yake ba wa Uwani suna ci yana ba ta labarin irin gwagwarmayar da suka sha. Wani irin tausayinsa ya kama ta, ta shafo gefen fuskarsa ta ce.

"Amma me ya sa ba ka dawo gida ba Nur?"
"Ai duk wanda kika ga ya tafi babu damar ya dawo matuƙar ba rashin lafiya ce ta kama shi ba, ita ma sai wacce ta ci ƙarfinsa. Yanzu ba ga shi na dawo ba, kuma wani abin farin cikin ma a Kano zan ci gaba da aiki In shaa Allah." Cikin farinciki Uwani ta ce, "Kai amma wallahi na yi farinciki."

A haka suka ci gaba da hira kuma sannu a hankali hirar tasu ta fara sauya salo, haka kawai Uwani ta tsinci kanta cikin faÉ—uwar gaba
"Nur ba za ka leƙa wurin Mami ba ko za ku yi hira." Uwani ta furta a ɗan tsorace. Har cikin jikinsa yake jin faɗuwar gaban Uwani, ya marairaice murya don ya fahimci halin tsoron da take ciki ya ce. "Ko Mami ai za ta yi mini uzuri yau, ta san fa na yi kewar matata, don haka ni yau angoncina na baya zan fanshe." Idanu Uwani ta waro waje, Jafar ya ɗaga mata gira yana kashe mata ido ɗaya. Dukan wasa ta kai masa tana faɗin, "Ni gaskiya ban yarda ba."

Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Idan littafi ya kammala 800 ne🫠

#Ummou Aslam Bint Adam🌚
*DoctorMaryamahGraphics and Data Services.*

MTN
•1gb ₦300
•2gb ₦600
•3gb ₦900
•5gb ₦1500

AIRTEL
1gb ₦350
•2gb ₦700
•3gb ₦1.050
•5gb ₦1.750

Glo
•1gb ₦300
•2gb ₦600
•3gb ₦900
•5gb ₦1500

9mobile
1gb ₦350
•2gb ₦700
•3gb ₦1.050
•5gb ₦1.750

Our Services:-

•Data Bundles
•Airtime purchase
•Cable TV subscriptions
•Recharge card
•Electricity Bills payment
•Converting Airtime to cash
•WAEC, NECO and jamb pins

Make payment into:-

3195402912 Firstbank Maryam Ibrahim
8136402046 Opay Maryam Ibrahim

Send the receipt into:-
+234 701 714 8194

Available 16hours📌 from 6am to 10pm.

And All types of different Logo invitation card and vide, save the Date and more_____

For more info:- 08136402046

Murmushi Jafar ya saki sannan ya miƙe tsaye yana faɗin, "Naki wasa ne yarinya, yanzu dai ɗauko mayafinki za mu fita shopping." Da sauri Uwani ta miƙe tana cewa.

"Bari na kira Auta mu tafi tare." Ba ta jira cewarsa ba ta É—auki mayafinta ta wuce sashen Daddy. Lokacin da su Uwani suka fito Jafar na jikin motar Daddy suna magana da shi, sai a lokacin Auta ta lura da fuskar Uwani ta gimtse dariyarta da hannu ta ce.
"Wai ni duk cikin ƙaunar ce aka goge miki wannan jan bakin ne?" Uwani ta wurga mata harara tana tuna lokacin da Jafar ya shammace ta ya fara sakar mata kisses, har sai da ta kwace kanta da ƙyar. Ta dubi Auta ta ce, "Wallahi Auta ki kiyaye ni kin saka mana ido ni da mijina, wai ma me kike nufi?"

"Me kuwa nake nufi? Ga abin da nake nufi can a gefen kumatun mijinki!" Auta ta faɗa tana nuna Jafar, zaro ido waje Uwani ta yi ganin janbakinta danɓar a gefen baki zuwa kumatunsa, don ma ta lura kamar Daddy bai gani ba tun da ba ta ɓangare yake ba.

"A toh ki ja shi gefe ki goge ragowar kar mu fita a dinga yi masa dariya." Uwani ta kwaɓe fuska kamar za ta yi kuka, lokacin da suka ƙarasa gaban motar Daddy ya wuce sashensa. Sam Jafar ya manta da Auta, Uwani ta saka hannu ta fara goge masa gefen kumatunsa ta ce. "Nur duk ka ɓata gefen bakinka da janbaki fa." Janyota ya yi jikinsa ya rungume ta, yana jin soyayyarta har cikina jikinsa, a ɗan kunyace Uwani ta raɗa masa.

"Auta fa tana gefenmu!"
Shi ma Jafar ya mayar mata da cewar, "Auta za ta hana ni soyayya da matata ne? Ko a gaban Daddy tsaf zan rungume ki." Uwani ta janye jikinta tana dariya ta ce. "Wallahi da ka kashe ni da kunya."
Zagayawa Jafar ya yi ya shiga mota, Auta ta mintsino Uwani ta ce.

"Idan kun san iskanta ni za ku yi Uwani sai na koma inda na fito, haka kawai ku sa Autar Daddy a gaba kuna falsafar É—iban albarka." Uwani ta saka dariya tana shigewa Mota.
Suna fita daga gidan kai tsaye Jafar ya wuce da su babban kantin Binafa shopping Complex da ke kan titin rijiyar zaki, saye-saye kala-kala ya yi musu dangin kayan ƙwalam da maƙwalashe. Sannan ya biya ya saya musu shawarma, burger da gasassun kaji. Bayan haka ya tambaye su ko akwai abin da suke buƙata, gabaɗaya suka ce babu saboda dama kayan zaƙi ne zaɓinsu kuma ya riga da ya saya musu. Lokacin da suka dawo gida kusan goma saura, a gate ya miƙa wa Auta ledojinsu ya ce ta kaiwa Mami da Aunty kowa da tashi. Uwani ta fakaici idon Auta ta sakar mata gwalo sannan suka wuce sashensu.

A falo Jafar ya baje musu ledojinsu, Uwani kuma ta faÉ—a toilet ta yi wanka. Bayan ta fito ta saka wata doguwar riga mara nauyi, ledar kaza ta fara janyowa ta saka a faranti tana faÉ—in.

"Kasan dai ni a nan fa na fi kauri Nur, da hajiya dajaja zan fara." Murmushi Jafar ya yi ya saka hannu ya dinga bata yana ci, suna hira cikin so da ƙauna. Sai da suka ci suka ƙoshi sannan Jafar ya ce Uwani ta ɗauro alwala za su gabatar da nafila. Jiki a sanyaye Uwani ta ɗauro alwala, bayan ta fito shi ma Jafar ya ɗauro alwala.
Jafar ya jima yana addu'o'i a lokacin da suka idar da sallah, sannan ya dafa kanta ya sake karanto addu'a. Bayan ya gama addu'o'in ya kama Uwani ya fara rage mata hijabin jikin, duk tsiwa da bakin Uwani tuni bakinta ya mutu. Jikinta ban da rawa babu abin da yake yi uffan ta gagara faÉ—a. Jafar ya lura da yanayin Uwani don har a jikinsa yana jin bugun zuciyarta, don haka lokacin da ya janyo ta jikinsa ya ce.

"Tsoron me kike ji?" A kunyace Uwani ta sunkuyar da kai ta ce, "Ba komai Nur."

Murmushi ya sakar mata a hankali hannuwansa suka fara yawo a jikinta, dalilin da ya sake birkita shi cikin yanayi marar misaltuwa. Jin yana aika mata baƙin saƙwannin da bai taba ratsa inuwarsu ba ya sa jikin Uwani ya ci gaba da karkawa. Cikin sanyin murya ta ce, "Don Allah ka yi haƙuri Nur."

Idon Jafar a lumshe cikin wata irin murya ya furta, "Da aka yi me?" Shiru Uwani ta yi don ba ta da amsa, Jafar ya ci gaba da aika mata zafafan sakwanni tun Uwani na ɗari-ɗari tuna huɗubar Aunty ya sa ta ɗan fara sakin jiki tana mayar masa da martani. Hakan ba ƙaramin hautsina shi ya yi ba, ta saki jiki tana ba shi duk kulawar da ta dace.
A lokacin da Uwani ta sakankance suna faranta ran juna, ta tsinkayi Jafar na addu'ar da Annabin rahama ya koyar ga magidanta ya yin tarawa da iyali.
Allahumma janibnashshaiɗan, wa janibnashshaiɗanu marazaƙtana.
Babu zato ta ji baƙon al'amarin da ba ta taɓa ji ba, duk yadda Uwani ta yi yunƙurin dakatar da Jafar abin ya gagara. Hakan ya sa ta saki kuka cikin jin raɗaɗi da azaba, Jafar bai fahimci halin da take ciki ba har sai ya samu nutusuwa ya dawo hayyacinsa. Ganin yadda Uwani ta yi tuɓus ya sa ya taimaka mata suka gyara kansu, a jikinsa ya kwantar da ita cikin so da ƙauna ya furta.

"Allah Ya yi miki albarka!" Fuskar Uwani kumbure idonta cike da ƙwallah ta ce, "Ni dai ba zan sake kwana a nan ba sashen Aunty zan koma." Maganar Uwani ta so ba shi dariya, ya saki murmushi ya ce. "To idan kin je ta ce me ya kawo ki kwana wurinta ki ce mata me?" Shiru Uwani ta yi hawaye na zuba, wuyanta ya ji ya ɗauki ɗumi. Ya ɗauko magani ya ɓallo mata ya ba ta tasha, sannan ya sake rungumo ta jikinsa yana sake ji wani abu na fisgarsa a kanta. Tana nan kwance sai saukar numfashinta ya ji bacci ya yi awon gaba da ita, gyara mata kwanciya ya yi ya ci gaba da yawo da hannunsa a cikin jikinta.

Cikin bacci Uwani ta ji Jafar na shirin sake biya mata karatun da ya biya mata da farko, ɗumin hawayenta ya ji na sauka a fuskarsa. Ta saka hannu tana yunƙurin ture shi, cikin wata irin murya ya furta.
"Don Allah kada ki dakatar ni." Jafar ya ci gaba da aika mata saƙonnin faratan zuƙatan ma'aurata, tuna nasihar Aunty ya sa ta sake daurewa ta ba wa Jafar haɗin kai har ya sake biyan buƙatarsa.

Washegari Uwani da zazzaɓi ta tashi, ga rashin ƙwarin jiki. Don haka Jafar da kansa ya haɗa musu breakfast, Uwani kuwa sai sake shagwaɓe masa take yi kamar yadda Aunty ta koya mata. Shagwaɓarta ba ƙaramin susuta Jafar ta yi ba hakan ya sa wuni guda ya gagara sukuni, sai dai Uwani sai ta yi kamar ta dakatar da shi sai ta tuna nasihar da Aunty ta dinga jera mata.

Wuni guda Jafar a tare da Uwani ya ƙare shi, wani abin da Jafar yake yi Uwani har mamaki take yi don ko kaɗan ba ya jin kunyarta. Sosai take mamaki da kunyarsa, don wani abin sai dai shi ya ce ta aiwatar masa da abin da yake muradi game da ita. Rashin gilmawar Jafar ya sa ran mami ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Don haka ta aika Auta kiransa a lokacin an idar da sallar la'asar. Bugun ƙofar da suka ji ne ya sa Jafar ya nufi ƙofar yana faɗin.

"Waye?"
Chapter 54 · 0% Book details