← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 71

Sashe 37

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun ranar da Daddy ya yi wa Mami maganar auren ta É—auki fushi da shi, ko gaisuwa ba ta shiga tsakaninsu. Don ma Jidda da Auta na kwantar mata da hankali, lokacin da Mami ta kira Shukra ta faÉ—a mata haka ta yi ta zuga ta tamkar ita ce uwarta. Shi kuwa Jafar da ta sanar da shi addu'a kawai ya ce ta yi a kan Allah Ya sa ta gari za a kawo mata. Don shi a ganinsa bai ga abin tashin hankali ba, jin Jafar bai ba ta wani goyon baya ba ya sa Mami ta katse wayarta ko da ya kira ta ba ta É—auka ba.

A ranar Juma'ar ne aka ɗaura auren Daddy da Abuwa, sai kuma na na Madina da Goggon su Sabi'u. Da yake ba wani taro aka yi ba ya sa ko Uwani ba ta je gidan ba, don Daddy cewa ya yi ba za ta dinga katse makaranta tana wayo ba. A farkon tafiyar Jafar Auta ke zuwa tana taya Uwani kwana, Daddy da kansa ne ya ce ta dinga taya ta kwana, amma tun ranar da ya faɗa wa Mami zai yi aure ta dakatar da ita. Da yake Mami ba ta bada fuska a game da auren Daddy ba ya sa ko wacce ya aura ɗin ma ba ta sani ba, sai a washegarin ranar da Abuwa ta tare. Saboda ko da aka kawo Abuwa Daddy ya yi juyin duniya Mami ta fito ya yi musu nasiha ta ƙi.
Mami na fitowa falo a lokacin ita ma Abuwa ta fito cikin doguwar rigar atamfa sai zuba ƙamshi take, ganin Mami ya sa ta saki fuska tana faɗin.

"Aunty Saratu ina kwana!"

Sai da Mami ta ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa sannan ta taɓe ta ce, "Riƙe gaisuwarki Abuwa kike ko wa? Dangin mijin sarakan munafurci wato har an samu wurin zama a wurin kishiyata, za ki ɗebo guntum munafurcinki ki ce wani ina kwana? Da ban tashi lafiya ba za ki gan ni haka? Sannu a hankali da ita amaryar da ku zan haɗa su in ci abu ta kazar ubanku." Abuwa na tsaye tana jin duk abin da Mami take faɗa, Daddy ya ƙarasa wurin ya furta. "Kafin dai ki haɗa dangin nawa da matar da na aura ya kamata ki san matsayi wacce ke gabanki, Saratu me ya sa kike haka ne?" Mami ta yi ƙuri tana kallonsa, Daddy ya nuna musu doguwar kujera yana faɗin.

"Saratu zo ki zauna, ke ma Zainab ki zauna." Sheƙeƙe Mami ta kalle shi ta watsar ta yi gaba har ta kusa fita a tsawace Daddy ya ce. "Wallahi Saratu idan kika saka ƙafa kika fita sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Ganin yanayin ɓacin ran da ke kwance a saman fuskar Daddy ya sa Mami ta koma ta zauna, jiki a sanyaye Abuwa ita ma ta zauna.

"Dalilin da ya sa na tara ku a nan don na tunasar da ku matsayin kowacce a cikinku..." Da sauri Mami ta katse shi.
"Ban gane me kake nufi ba Daddyn yara." Daddy bai kula ta ba ya ci gaba.
"Zan fara da ke Saratu ke ce babba, ke ce uwar 'ya'yana kuma ban yi auren nan domin na wulaƙanta ki ko don kin gaza ba. Kuma ba don ba na sonki ko ba na ƙaunarki ba, sai don ra'ayin kaina. Ki riƙe girmanki a matsayinki na babba, ba na son jin wani tashin hankali daga gare ki." Daddy ya waiga wurin Abuwa ya ce.
"Ke kuma Zainab ke ce ƙarama, ban auro ki domin ba na ƙaunar matata ba ko don ta gaza mini ba..." A zabure Mami ta miƙe tsaye tana nuna Abuwa ta furta.
"Wannan ita ce kishiyar tawa? Wato kace auren cin amana aka yi, ai shi kenan dama ni na jima da sanin Dada ba ƙaunata take yi ba. Shi kenan burinta ya cika tun da ta haɗa ka da 'yarta, don haka ka riƙe kalamanka babu wani amfani da za su yi mini." Mami na gama faɗar haka fuuuu ta shige ɗakinta, Abuwa ta sunkuyar da kai ƙasa idanunta suka ciko da ƙwallah ta furta.
"Daddyn Jafar abin da na jima ina tsoro kenan shi ya sa tun farko na ƙi amincewa da maganar auren nan, ba na son na zama silar tarwatsewar gidanka. Don Allah..." Daddy ya yi saurin katse ta, "Ba na son ƙara jin wata makamanciyar magana irin wannan, tashi ki shiga ɗaki zan sa a kawo breakfast." Babu musu Abuwa ta shiga ɗakinta, Daddy ya miƙe ya nufi ɗakin Mami.

Kamar ƙaramar yarinya haka ya same ta a kan gado tana gursheƙen kuka, zama ya yi a gefenta ya janyo ta da ƙarfi ta fara kiciniyar fisgewa. Riƙe ta ya yi sosai suna fuskantar juna, Daddy ya ciro wani handkee ya ba ta sannan ya furta. "Goge fuskarki!" Shiru Mami ta yi ganin ba ta da niyyar goge fuskarsa ya sa ya ɗauka ya goge mata sannan ya furta.

"Me ya sa kike son saka wa kanki damuwa a kan abin da bai taka kara ya karya ba? Saratu!" Daddy ya kira ta da wata irin murya.
"Ke ce matata ta farko wacce muka yi aure tun ƙuruciya, ke ce kuma uwar 'ya'yana wacce duniya ta san ni da ita. Na san wace ce ke kin san waye ni, ba na jin ko mahaifiyata ta san waɗansu ɗabi'un nawa kamar yadda kika san ni. Ta yaya kike tunanin zan auri wata mace domin na tozarta ki ko na wulaƙanta ki? Saratu da zan wulaƙanta ki yau shekara sama da talatin da aurenmu, ban wulaƙanta ki ba sai yanzu? Ina ƙaunarki kin sani..."
"Amma me ya sa Daddyn yara?" Mami ta katse shi.

"Me ya sa tun tuni ba ka yi auren ba sai yanzu? Me ya sa ba ka fita duniya ka auri bare ba sai a danginka? Allah Ya sani ba zan iya jure ganin ka tare da wata ba, idan na furta hakan na yaudari kaina. Don Allah ka rubuta mini takardata na haƙura da kai Daddyn yara." Murmushi Daddy ya saki ya furta. "Saratu kenan! Ke a gajeren hankalinki kina ganin zan iya sakinki a yanzu? Ki yi nazari da kyau don kin fi kowa sanin wane ne ni idan har zan rabu da ke da tuni na jima da sakinki. Ki yi tunani da kyau kin san dai zan yi adalci a tsakaninku." Daddy na kai wa nan ya fice daga ɗakin.

Haka zaman Mami da Abuwa ya ci gaba da tafiya, Mami ba ta kula ta koda ita ta yi mata magana. Hatta shi kansa Daddy ta zame al'amuranta daga gare shi, daga gaisuwa babu abin da yake haÉ—a su koda ranar girkinta ne, Auta tana ba wa Abuwa girma daidai gwargwado Jidda ce dai take ta ya Mami kishi sai kuma Shukra idan ta zo gidan, amma hatta Ibrahim idan suka haÉ—u yana ba ta girmanta.
Zaman Abuwa a gidan sai ya kawo wa Uwani samun rangwame da sauƙi sosai, sai ɗan abin da ba a rasa ba domin da gayya Mami take saka Uwani wani aikin don tana taƙamar ita mahaifiyar Jafar ce. Kuma ta ci alwashin yadda Dada ya dasa mata baƙin cikin zama da kishiya, ko da malamai sai ta sa Jafar ya ƙara aure ko da kuwa Safna ba ce. Ballanta ta tabbata Safna ita ce birnin zuciyar Jafar.

Tun da Jafar ya sa ƙafa ya tafi Lagos sai da ya shafe sama da wata takwas ba tare da ya zo Kano ba, kullin Daddy ya yi masa maganar zuwa gida sai ya ce masa aiki ne ya yi masa yawa, ko ya ce an tura shi wani garin aiki. Har sai da ran Daddy ya ɓaci ya ce masa tun da ba zai dawo ba zai nemawar Uwani transfer makaranta ta bi shi Lagos ta ci gaba da karatunta a can. Abin da Daddy bai sani ba kuma, Mami ce ta hana Jafar zuwa har sai da ya sanar mata da saƙon Daddy sannan ta amince masa, don ta san idan ta bari Uwani ta bi shi Lagos komai zai iya faruwa, kuma ta samu 'yancin cin gashin kanta a ɓangare ɗaya kuma ta wargaza maganar auren Jafar da Safna. Tun da ta san ko hauka ne a kan Hajiyan Safna ba za ta bari Safna ta auri Jafar ba, matuƙar ta san yana da aure.

A ranar wata laraba ne Jafar ya ce zai zo, amma da yake kwana suke yi a hanya sai alhamis zai iso Kano. Daddy ne ya sanar da Aunty wato Abuwa da su Uwani suke saka mata. A ranar alhamis kuwa cewa ta yi Uwani ba za ta makaranta ba saboda ta yi É—an gyare-gyaren da ba a rasa ba tun da mijinta zai dawo. Daddy bai yi faÉ—a ba, sai ma daÉ—i da ya ji ganin yadda Abuwa ke haÉ—a Uwani da Auta take yi musu abu tare kamar 'ya'yan cikinta.

Abuwa da kanta ta kai Uwani wurin wankin kai da yake me kufan gashi ce tuni kanta ya haɗe, daga nan ta kai ta gidan lalle ita ma aka zane mata ƙafa da hannunta. Uwani ta fito shar ta yi kyau, bayan sun dawo gida ta sa Uwani ta sake gyara gidanta aka saka turaren wuta, ta ko ina ƙamshi sai tashi yake.

Kimanin ƙarfe bakwai na dare Jafar ya ƙaraso gida, sashen Mami ya fara shiga ya gaishe ta sannan ya fito falo suka haɗu da Aunty suka gaisa. Jafar har zai sauka Mami ta furta.
Chapter 37 · 0% Book details