← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 71

Sashe 60

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baby!" Ta furta tana girgiza ƙafarsa. Murmushi ya sakar mata sannan ya kai mata baki, karɓa ta yi ita ma ta ɗauka ta fara ba shi. Sai da suka ci suka yi ƙat sannan Jafar ya umarce ta da ta ɗauro alwala, duk da zuciyarta na ɗar-ɗar amma wani irin farinciki take ji yana ratsa ta. Bayan sun idar da sallah ya jima yana yi musu addu'a sannan suka shafa. Abubuwa da dama idan Jafar ya aiwatar wa Safna rayuwarsa da Uwani ce take faɗo masa, hakan ne ya sa ko a lokacin da yake tarawa da Safna cikin suɓutar ba ki yake ambatar sunan Uwani. Ba ƙaramin kaɗuwa Safna ta yi ba jin Jafar na ambatar sunan wata mace ba ita ba.

"Jafar ko yana neman mata ne ban sani ba? Kai ko kaÉ—an mu'amalarsa ba ta yi kama da ta masu neman mata ba." Safna ta raya a ranta.
"Ko kuma dai na yi masa magana?" Ta sake tambayar kanta. Tana cikin wannan nazarin Jafar ya riƙo hannunta ya taimaka mata ta gyara jikinta. Tana son tambayarsa amma a zuciyarta na wasu-wasi, don haka ta rabu da shi ta fara narkewa tana shagwaɓe masa.
Bakin ƙoƙarinsa Jafar ya ba wa Safna kulawa sai dai sam ba haka ta yi tsammani daga gare shi ba, a yadda suka zuba soyayya ta yi tsammanin zai nuna mata kulawa fiye da haka. Ko da Jafar bai faɗa mata ba ta san tabbas yana cikin damuwa, domin wani lokacin tsakar dare za ta farka ta ga ya zuba uban tagumi. Amma idan ta tambaye shi wani lokacin sai dai ya ce mata aiki ne ya yi masa yawa, ko ya ce mata wani case ne yake caza masa kai.

Auta ta yi zaryar wurin Dada babu adadi a kan ta sanar mata wurin da Uwani take amma fir ta ƙi, babu yadda Auta ta iya haka ta haƙura amma kullin tunaninta bai wuce ina Uwani take ba.
Gabaɗaya gidan suke jin sa wani iri daga ita har Aunty don idan suka zauna ba su da aiki sai na jajen Uwani, wani lokacin Auta ta sako maganar Mami don ta kan yi kewar mahaifiyarta. Hakan ya sa wani lokacin Aunty ke samun Daddy da maganar don Auta da Madina ba ƙaramin tausayi suke ba ta ba, a kullin Aunty ta je masa da maganar ba ya taɓa ba ta haɗin kai.

Ganin zuru ɗin da Jafar ya yi ba zai kai shi ba ya sa ya fara bibiyar 'yan uwan mahaifinsa, sai dai duk wurin da ya je a kan maganar Uwani amsa ɗaya yake samu, kuma ya yi zaryar gidan mahaifiyarta nan ma an ce masa ba ta nan. Don haka abin duniya ya sake haɗe masa, tun Safna na fushi ta shiga damuwa har ta haƙura ta watsar da komai, tun da ta yi bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta gano abin da yake damunsa ta gagara.

Kamar yadda Dada ta faɗa kusan duk sati sai ta kai wa Uwani ziyara, ganin zirga-zirgar ta yi yawa ya sa Maryama ta ce Dada ta dinga haƙura har sai bayan sati bibbiyu, da ƙyar Dada ta amince da haka. Uwani ta murje ta yi wani irin haske da yake a yanzu laulayin ya yi mata sauƙi. A kullin ta zauna ba ta da aiki sai kallon hotuna da videos ɗin su ita da Jafar, wani lokacin da ta ci kuka wani lokacin kuma idan ta ga wani video ta yi ta sakin murmushi. Gajiya ta yi da zama babu waya don haka ta sa aka sayo mata wani sabon layi, ta kunna wayarta, tsohon layinta ta ɗora ta lalubo lambar Jafar ta ƙura mata ido. Hawaye ke bin idonta kamar almara sai gani ta yi kiransa ya shigo wayarta, sai da ta yanke aka sake kira hannunta na rawa ta ɗaga wayar ta kara a kunne. Ajiyar zuciyarsa ta ji a fili baki na rawa ya ce.

"Bakin tsiwata!" Shiru ta yi tana jin yadda ƙirjinta ke dakan lugude, wani abu ta ji na zagaye ta hawaye ya ci gaba da bin kumatunta.
"Don Allah ki yi mini magana ko zan ji sanyi a raina, so da ƙaunarki za su zautar da ni..." Ƙit ya ji ta katse wayar, jikinta har karkarwa yake ta zare layin ta ɗora sabon layinta a kai. Ta jima tana hawaye sannan ta kwanta ta lula duniyar tunani.

Abin duniya goma da ashirin ne ya mamaye Mami, don a yanzu babu damar ta ajiye kuɗi ko wani abin da ta zagaya banɗaki ko ta matsa daga wurin za ta neme shi ta rasa, ga shi zaman gidan gabaɗaya ya gundure ta. Duk taurin zuciya da kafiya irin ta Mami ƙuncin zaman da take yi ya sa ta yanke shawar kiran Daddy ta ba shi haƙuri. Sai da ta yi wa Daddy kira ya fi hamsin amma babu ɗaya da ya ɗauka, wayar matar babanta ta ara ta kira shi babu jimawa ta ji ya ɗauka.

"Daddyn yara yanzu wayata ce ba za ka ɗauka..." Ba ta gama magana ba ta ji Daddy ya kashe wayar gabaɗaya. A ranar saboda takaici Mami har da ƙwallarta.
Kamar Auta na da masaniya haka kawai watarana da ta wayi gari ta ce za je wurin Mami, wuni guda ta yi a wurinta amma a mafi yawan hirar tasu Mami ce ke kawo mata ƙorafe-ƙorafen zaman gidan da take yi. Ko kaɗan Auta ba ta ji daɗi ba, hakan ya sa ta fara nusar da ita illar abin da ta dinga aikatawa a baya. An yin sallar la'asar Auta ta yi mata sallama, haka kawai zuciya ta raya mata ta ƙarasa ta gaida mahaifiyar Uwani. Don tun bayan abin da ya faru ba ta sake ganinta ba. Saɓanin lokacin da Uwani na nan ba sa wata ba su je ba.

Sai da ta saya wa Maryama kilin da omo a wani shago sannan ta shiga cikin gidan baki É—auke da sallama, Uwani na zaune a kan tabarma tana cin wainar fulawa a lokacin cikinta kusan watansa bakwai. Turus Auta ta yi tana kallon Uwani da ta saki baki tana kallon Auta da mamaki.

"Uwani dama kina nan?" Auta ta furta a ruɗe. Da gudu Uwani ta tafi ta maƙale Auta ta ce, "Auta ya aka yi kika san ina nan?" Auta ta wurga mata harara ta ce. "Malama ki bi a sannu kada ki yi mini asarar yaro ko yarinya."
"Ke fa 'yar iska ce, yanzu dai mu shiga ciki." Uwani ta faÉ—a ta kama hannun Auta suka shiga É—akin mahaifiyarta.

Littafin kuÉ—i ne 500 ta acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan no 07062062624 idan littafi ya kammala 800 ne

#Ummou Aslam Bint Adam🌚

Tun kafin su shiga cikin ɗakin Auta take bin Uwani da kallo ganin da ta yi wani irin kyau da wata 'yar ƙiba.
"Zo faÉ—a mini wai me Inna take ba ki kike ci ne? Haka kika haye kika bar mini É—an uwa yana fama da tunaninki?" Uwani ta wurga mata hararar wasa ta ce.
"Ba na son sharri wai mike kika ga na yi?" Auta ta riƙe haɓa da mamaki ta ce, "Yo ai ko makaho ya shafa ki ya san kin yi ƙiba."
Ruwa Maryama ta kawo wa Auta tana tambayarta su Daddy sai da suka gama gaisawa ta fita ta ba su wuri.

"Uwani ni laifin me na yi da ko a waya ba ki neme ni kin faɗa mini wurin da kike ba? Ko laifin Mami ne ya shafe ni? Wallahi duk yadda muka yi da Dada ta ƙi sanar da mu wurin da kike, yanzu ma rabon zan ganki ne na ce bari na biyo na gaida Inna." Nan take Uwani ta kwashe yadda suka yi da Dada ta faɗa wa Auta, sannan ta ɗora da cewa.

"Don Allah kada ki sanar da kowa ga wurin da nake kin san Dada gani za ta yi kamar ni ce na sanar da ku."
"Amma haka zan bar Ya Jafar kullin yana yawo kamar zautacce, Uwani kin san halin da ya shiga kuwa?" Gaban Uwani ya faÉ—i, a sanyaye ta furta.
"Ni dai kin ji abin da na faÉ—a, idan kuma kika janyo mini matsala ai shi kenan." Jim Auta ta yi sannan ta ce.

"Babu damuwa, Allah Ya tabatar mana da abin da ya fi alheri. Amma gaskiya zan sanar da Aunty halin da ake ciki, sai dai ita ma zan kwaɓe ta, ko Daddy kada ta sanarwa. Kin san daga baya idan ta ji na san wurin da kike ba za ta ji daɗi ba."
Auta da Uwani hira suka sha ta yaushe gamo, Auta ta karɓi sabuwar lambar Uwani. Sannan suka shiga hirar bikinta, don a lokacin bikinta saura wata biyu cif.Sai da aka yi sallar magriba sannan Auta ta yi musu sallama ta tafi, don lokacin ma sai da Maryama ta yi mata magana ganin dare ya fara yi saboda yanayin hanya, Auta ji ta yi tamkar ta kwana don dai babu hali ne. Sai da ta tafi tana hanya ta duba wayarta misscall ɗin Aunty ta gani rututu, gabanta ne ya faɗi ta yi saurin kiran wayarta Aunty na ɗauka ta rufe ta da faɗa.

"Auta ina kika shiga ne dare ya fara yi fa, so kike sai Daddynku ya zo ya fara faÉ—a ko?" Da yake a lokacin Auta ta kusa shiga layinsu a gaggauce ta ce. "Aunty gani ina kusa da gida."

Auta na isa gida ta samu Aunty a falo fuska babu walwala.
"Hajiya Aunty sannu da gida!"

"Wallahi da Daddynku da ya dawo ya yi mini faɗa hukuncinki karɓar wayar hannunki, kuma ki wuce ga tuwo can sai ki kwashe ni na gama aikina." Auta ta ƙunshe dariyarta ganin yadda Aunty ta fututtuke tana faɗa.
"To Hajiya Aunty yanzu dai ba na dawo ba, kuma wallahi da wani albishir nake tafe. Amma ni ma sai na ja ajina." Aunty na jin haka ta saki murmushi ta ce.
Chapter 60 · 0% Book details