Sashe 59
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Mami ce ta ba ni umarnin haka." Nan take ya kwashe yadda suka yi da Mami, Daddy ya jinjina kai rai a ɓace ya ce. "Ka ci gaba da bin ra'ayin mahaifiyarka a kan cikin gidanka, sai ka auna a mizani duk lilon da take ɗora ka akai mai inganci ne ko kuwa a lilon keken ɓera ne? Ban hana ka yi wa mahaifiyarka biyayya ba amma ka san irin umarnin da za ta ba ka ka ɗauka, yanzu kuma dabara ta rage wa mai shiga rijiya. Ruwanka ne ka sanar mata kana da aure, ruwanka ne ku ci gaba da tafiya a haka. Amma ina mai tabbata maka da sannu-sannu ba ta hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba, kuma akwai ranar ƙin dillanci."
Sai a wannan lokacin nadamar hakan ta lulluɓe Jafar, tabbas shawarwarin Mami kaso casa'in da take ba shi ba masu ɓullewa ba ne.
"Daddy maganar Uwani fa?" Jafar ya tambaya gabansa na faÉ—uwa.
"Dada ta hau fa dokin zuciya kuma kai shaida ne ba ta iya fushi ba, sannan ina mai ba ka umarni matuƙar maganar Uwani ce za ta kai ka cikin gidan nan, ban lamunce maka a matsayina na mahaifinka ba. Saboda ni kaina sharaɗi ne da umarnin mahaifiyata ta gindaya mini, kamar yadda na faɗa maka ka je ka ci gaba da addu'a amma yanzu haka matarka ba ta cikin garin nan. Dada ta tabbatar mini da ba ta ma garin gabaɗaya, sai ka je ka ci gaba da shirye-shiryen bikinka." Jafar bai tanka masa ba, ya miƙe yana haɗa hanya. A haka har ya nufi sashensu da yake jin ya zame masa tamkar kuffai.
"Duk da Aunty Saratu ba ta kyauta ba amma hukuncin da Dada ta ɗauka a wannan karon ya yi tsauri. Don Allah idan an kwana biyu ku sake ba ta haƙuri Uwani ta dawo ɗakinta."
Daddy ya jinjina kai cikin damuwa ya ce.
"Zainabu har yanzu ba ki san Dada ba, a soyayyar da Dada ke wa Uwani ba na jin a kwana kusa za ta sauko daga dokin zuciyar da take kai. A sanin da na yi wa Dada idan aka matsanta da maganar wallahi tsaf za ta iya kai Jafar gaban kotu a kan sai ya bada takardarta, addu'ar dai ita ce mafita." Aunty ta furta.
"Allah Ya kawo mana ƙarshen wannan al'amarin." Gabaɗaya suka amsa da amin, don hukunci gabaɗaya bai yi musu ba. Daga na wurin Dada har na wurin Daddy.
Sannu a hankali Jafar ya aura wa kansa zaman cikin ɗaki, haka yake wuni da kwana cikin damuwa ko abinci ba ya ciki. A ɓangare ɗaya kuma Safna ta gagara gane kansa, matsananciyar damuwar da yake ciki ta haifar masa da wata iriyar rama. Sau tari idan Aunty ta aika masa da abinci sai dai a dawo mata da shi, hakan ya sa watarana ta samu Daddy da zancen ya je ya same shi ya taushe shi ko zai rage wata damuwar.
Mami tun da ta koma zaman gidan mahaifinta sam bai mata daɗi ba, duk da ta sa Ibrahim ya saya mata kayan abinci da kayan shayi amma zuciyarta kullun azalzakarta take a kan Daddy na can shi da Aunty suna cikin farinciki. Jafar ma ya kira ta ya tambaye ta abin da take buƙata, ta ce masa Ibrahim ya saya mata komai. Don haka shi kuma ya tura mata kuɗi ya ce ta yi wasu buƙatun da su, da yake a lokacin sun samu albashi. Shukra ma sai daga baya take jin labarin abin da ya faru, hakan ba ƙaramin sosa mata zuciya ya yi ba.
A yanzu babban tashin hankalin da Mami take ciki bai wuce idan bikin Jafar da Safna ya zo yadda za ta ji da ƙawayenta ba.
"Yanzu sai na ce Daddyn yara ne ya turo ni gidanmu? Kai ba zai yuwu ba." Mami ta raya a ranta.
"Ko kuma zan gayyato su wannan gidan? Gaskiya ba mutumcina ba ne na gayyato su gidan nan, tun da gidan ƙasa ne." Haka Mami ta dinga saƙa da warwara, a haka har dabara ta faɗo mata wacce ta san za ta fitar da kanta kunyar cikin ƙawaye tun da ta riga da ta gama raba Invitation.
Sosai Daddy ya yi masa faÉ—a da nasiha hakan ne ya sa Jafar yake É—an shan ruwan tea safe da yamma, sai dai abin da yake damunsa a kullin ya kira layin Uwani sai dai ya ji shi a kashe.
Kamar yadda Jafar ya yi wa Safna alƙawarin halartar taron dinner hakan ce ta kasance, kasancewar familyn mahaifi da mahaifiyar Safna duk mutanen Kano ne, hakan ya sa mahaifinta ya yanke shawarar yin bikinta a gidansa da ke Unguwar Sharaɗa. Jafar da Safna sun yi shigar purple kuma ba ƙaramin kyau suka yi ba, katafaren hall ne da ya amsa sunansa wanda duk mahaifin Safna ne ya yi komai. Jafar ya ɗan saki jiki yana 'yar walwala ganin yadda Safna ta damu da damuwarsa, don tun tana tambayarsa har ta haƙura ta watsar tun da amsar a kullin ɗaya ce sai dai ya ce mata babu komai.
Mami ita da ƙawayenta sun yi shiga ta alfarma, kuma da yake tana cike da su Dada babu mutum ɗaya daga ɓangaren Daddy da ta ba wa gate pass. Aunty ma da farko ba ta yi niyyar zuwa ba sai Shukra ce ta ba ta gate pass ta yi ta roƙonta sannan ta amince. An yi taron lafiya an gama lafiya cikin farinciki da ƙayatarwa.
Daga nan hall kuma Mami kai tsaye gidan Daddy ta wuce, tana zuwa kai tsaye ta wuce É—akinsa. A lokacin da ta shiga yana zaune a kan kujerarsa, da mamaki ya bi ta da kallo ko gaisuwar arziki ba ta haÉ—a su ba Mami ta ce.
"Daddyn yara kada ka yi mamakin ganina, na zo ne domin a yi bikin É—ana da ni. Idan aka kawo amarya zan yi tafiyata na bar maka gidanka." Ba ta jira cewarsa ba ta fice fuuu Daddy ya bita da kallo, mamaki ya mamaye shi ganin har lokacin babu nadama a tattare da ita.
Duk wani abin da ya danganci abinci da hidimar mutane Daddy ne ya damƙa wa Aunty, don haka Mami ta sake ƙullatar Aunty hatta su Dada babu wani kallon arziƙi da yake haɗa ta da su, su ma kuma daga ɓangarensu babu wanda ya yi gigin zuwa sashenta.
Washegari ne ya kama ranar Lahadi kuma a ranar ne dubban al'umma suka shaida ɗaurin auren Jafar da Safana a kan sadaki naira dubu ɗari biyu. Bakin Mami saboda farinciki ya ƙi rufuwa, haka daga ɓangaren Safna ji take tamkar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.
"A duk duniyar nan bayan ni ba na jin akwai wacce za ta so ki sama da Dada, Uwani kada ki yi wa Dada mummunar fahimta domin soyayyar da take yi miki ce ta sa ta ɗauki wannan matakin a kanki. Kada ki sake ki ba ta kunya Uwani matuƙar kika bi abin da Dada ta nusar da ke wallahi ba Jafar ba hatta mahaifiyarsa muna zaune sai ta nemi bikonki. Ke dai ki kwantar da hankalinki kada ki saka wa kanki damuwa kin san dai ba ke kaɗai ba ce, ki kula da kanki har zuwa lokacin da Allah zai sauke ki lafiya." Maryama ta yi wa Uwani nasiha, gyaɗa kai Uwani ta yi idanunta na ciko da ƙwallah.
Sau tari mahaifiyarta na zama ta yi ta ɗebe mata kewa, haka daga ɓangaren mutanen gidan babu wani bambamci ko ƙyama da take fuskanta. Da yake Uwani ba ta da wuyar sabo har ta saba da 'ya'yan gidan.
Uwani tana yawan tashi sallar dare ta kai wa Allah kukanta. Sai dai a kullin ji take soyayya da kishin Jafar na sake nuƙurƙusarta, musamman da ta kasance ranar Lahadi kuma a ranar ne take da tabbacin an ɗaura wa Jafar aure da Safna. Wani abu mai nauyi ta ji ya danne mata zuciya, ta miƙe ta shiga ɓanɗaki sai da ci kuka ta ƙoshi sannan ta yi wanka ta dawo ɗaki ta kwanta.
Tun da gari ya waye mahaifiyarta ta lura da yanayinta, tambayar duniya ta yi mata Uwani ta ƙi gaya mata sai ce mata ta yi cikinta ne yake ɗan yi mata ciwo.
Yamma liÆ™is Jafar ya tura mota aka É—auko Safna, sai da aka fara kawo ta nan gidan Daddy aka kai ta kowanne É“angare ta gaida su sannan aka sake fita da ita aka wuce da ita gidanta. Ƙawayen Safna kusan su huÉ—u ne suka zauna zaman jiran sayan baki, da mamaki sai gani suka yi shi kaÉ—ai ya shiga hannuwansa É—auke da ledoji. Sam Jafar ba shi da ra'ayin zaman wani sayane baki, don haka ganin babu wata fuska ya sa Safna ta yi musu raÉ—a a kunne. Sallama suka yi masa kowacce ta É—auki jakarta ta fita, har sun kusa gate Jafar ya bi su ya ce akwai abokinsa Muhammad zai mayar da su gida. Suna fita ya saka sakata ya dawo ciki. Æangaren Safna ba Æ™aramin tsaruwa ya yi ba, kuma an narka dukiya daidai gwargwado. Da yake Hajiyan Safna ta san Jafar na da Æ™ani Ibrahim, ko da 'yan jere suka kai mata rahoton sashe biyu ne a gidan daga ita har Safna sai suka yi tsammanin na Ibrahim ne. Don ba a jima ba da Mami ta taÉ“a yi mata maganar, shi ma Ibrahim ana shirin kai masa kuÉ—in aure.
Shigar Jafar ɗakin babu jimawa Safna ta yaye mayafin jikinta, ba ƙaramin kyau ta yi masa ba. Ya zauna a bakin gado ya sakar mata murmushi.
"Cutie kin yi kyau!" Cike da kissa Safna ta sunkuyar da kai ƙasa tana murmushi. Hira Jafar ya ɗan ja ta da shi sannan ya shiga toilet ya watsa ruwa, bayan ya fito ya yi musu masauki a ƙasan carpet.
Da kansa ya riƙo hannun Safna ya zaunar da ita, lokaci ɗaya zamansa da Uwani ya faɗo masa a ranar da ya dawo daga Sudan. Wani abu ya ji ya tsaye masa a rai, ya haɗiyi yawu mai ɗaci. Safna ta yi mamakin ganin yadda Jafar ya ɗauki tsokar nama amma ya lula duniyar tunani.