Sashe 48
Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Gaskiya ni dai kada ka tafi Ya Jafar wallahi tsoro nake ji." Murmushi Jafar ya saki ya ce. "Tsoron me Uwani?" Shiru ta yi ta kasa magana saboda yadda ƙirjinta ke bugawa.
"Ko tsoro kike ji kada a kashe ni? Ba ke kika ce idan muka rabu za ki auri mai ƙaunarki ba? Ko kin manta?" Idanun Uwani suka sake zubo da ƙwalla, ta kwantar da kanta a ƙirjinsa har cikin jikinsa yana jin bugun zuciyarta.
"Ai wannan ba mutuwa ba ce, kawai dai idan ka sake ni ne zan auri wani tun da kai ma Safna kake so. Amma wallahi ba na son ka tafi, ba na son wani abu ya same ka." Har a ransa ya ji zafin kalaman Uwani, wato har yanzu dai ba ta jin irin abin da yake ji a kanta.
"To wanda ba ka son shi don ya mutu damuwar me za ka yi? Kin ga dai tun da ba kya sona ko na mutu shi kenan Safna ce za ta ji babu daÉ—i." Shiru Uwani ta yi tana jin zuciyarta na zafi, tsam ta tashi daga kusa da shi fuska babu walwala ta ce.
"Tun da haka ka gani shi kenan, dama ka sha faɗa mini Safna ita ce zaɓinka. Ni dama ka ga auren haɗi aka yi mana, tun da haka ne don Allah ka sake ni kafin ka yi tafiyarka. Ka ga shi kenan babu takaba a kaina, idan ya so sai a ɗaura maka aure da Safna kafin ka tafi. Duk tsiya dai na san babu abin da figaggiyar budurwarka za ta nuna mini." Uwani na gama magana ta shige uwar ɗaki, kan gado ta faɗa ta saki wani marayan kuka.
Tun daga farkon kalaman Uwani tsaf Jafar ya fahimce cike suke da zallar kishi, maganarta ta ƙarshe ta ba shi dariya wai figaggiyar budurwarsa. Miƙe wa ya yi ya shiga ɗakin har zai mata magana ya lallashe ta, sai ɗayar zuciyarsa ta gargaɗe shi da faɗin.
"Ya kamata ka rage rawar kai a kan yarinyar nan, kar ka zo raini ya shiga tsakaninku." Toilet ya faÉ—a ya yi wanka har ya fito Uwani na kwance, bayan ya shirya ne ya nufi sashen Mami.
Bayan fitar su Jafar 'yar hira su Dada suka taɓa, baba Mustafa ya ce zai tafi ita ma Dada ta ce su wuce tare. Sai da su Dada suka sauka sannan Mami ta iya motsawa ta koma ɗakinta, Aunty har bakin gate ta raka su sannan ta koma ta shiga kitchen don ranar ita ce da girki.
Lado yana nan zaune yana bin su da kallo jiki a sanyaye, sai da Daddy ya raka su har zai koma Lado ya sha gabansa ya sake ba shi haƙuri a kan abin da suka aikata. Daddy ya yi masa nasiha sosai sannan ya ce masa ya samu Uwani ya nemi yafiyarta, ko ba komai zai sauke nauyi daga kansa.
Jafar na shiga sashen Mami a zaune ya same ta a kan kujera, bayan ya sake gaishe ta ya yi mata kallon tsaf ya ga duk ta rame ta lalace. Yana shirin fara magana Mami ta furta.
"Wato kai yanzu Jafar ina yi maka kallon mai hankali ashe kai shashasha ne ba ka da tunani? Duk huɗubar da nake yi maka a kan yarinyar nan ya tashi a iska? Jafar yanzu a kan Uwani ne har ya kake tayar da jijiyar wuya a kan idona, saboda ƙanwarka da mijinta sun mare ta." Ɗago wa ya yi zuciyar sa na zafi ya kalli Mami, ya sassauta murya ya furta.
"Mami ko ina son Uwani ko ba na son Uwani matata ce kuma a ƙarƙashin ikona take, duk fa wani haƙƙinta yana kaina. Yanzu kina ganin ko mijin Shukra zai zauna wani ƙato ya mari matarsa ba tare da ya ɗauki mataki a kai ba? Mami don Allah ki fahimci ni, amma abin da kike yi fa ya yi yawa. Ki duba ki ga fa saboda Uwani kin kusa jefa rayuwarki a cikin wani halin ina amfanin haka? Yanzu kina ganin Dada ba za ta sanar da sauran 'ya'yanta abin da ya faru ba? Mami ba kya tunanin irin kallon da mutanen Kura da duk wanda ya ji labarin nan zai yi miki?" Jafar ya haɗa hannuwa biyu alamar roƙo sannan ya ci gaba da cewa.
"Na haɗa ki da girman Allah Mami ki fita a harkar Uwani, aure ne dai na faɗa miki zan auri Safna ƙarshen magana ma ga shi har iyaye sun shiga ciki. Na sha faɗa miki Safna ita ce zaɓina ita nake so to me zai dame ki? Wallahi Mami ina tsoron lokacin da Uwani za ta dinga mayar miki da martani domin yau da gobe ta fi ƙarfin wasa." Tun da Jafar ya fara magana Mami take wurga masa harara sai da ta ji ya gama magana sannan ta ce.
"Wallahi har abada ba na jin zan ƙaunaci tsinanniyar yarinyar nan a cikin zuciyata, duk wannan sharhin da kake yi na fuskanci inda ka dosa amma da sannu kai ma zan gyara maka zama. Idan ka gama tashi ka fita ka ba ni wuri." Mami ta ƙarasa maganar tana nuna masa ƙofa.
Ganin Mami ta ɗauka da zafi ya sa Jafar ya saki murmushi ya ce. "Tuba nake ranki shi daɗe, yanzu dai Mami mu bar wannan zancen. Cikin wata na gaba nake son fara haɗa lefe, amma kafin nan akwai kuɗaɗen da za a biya mu kafin mu tafi ina son Daddy zai saya mini fuloti a unguwar Mai dile." Jin daɗin maganar Jafar ta haɗa lefen Safna ya wanke laifinsa a ranta, cikin farin ciki Mami ta ce. "To ko kai fa? Allah Ya nuna mana da rai da lafiya. Dama duk wani abin da ka sani irin na 'ya'yan manya za a yi, don kasan dai wane ne mahaifin Safna. Kuma idan ka tashi babban gida za ka gina mata don na fi son harkar girma, Allah dai ya kai ka wannan ƙasar lafiya ya dawo da kai lafiya." Jafar ya yi murmushi sannan ya amsa da Amin. Ya jima a wurin mahaifiyarsa suna hira, sannan ya fice daga ɓangarenta. Yana fita harabar gidan ya ga su Auta sun dawo daga makaranta, da gudu suka ƙarasa wurinsa suna mamakin ganinsa. Sai da suka ɗan taɓa hira sannan suka wuce ciki shi ma ya koma sashensu.
Ko da ya koma Uwani zaune take tana game a wayarta, ko ƙurarsa ba ta kalla ba Jafar ya saki murmushi don ya fahimci fushi take da shi.
Washegari tun da Uwani ta tashi sallar asuba ba ta koma ba, sai da ta haɗa musu breakfast a lokacin Jafar yana kwance. Sai da ta shirya komai ta ajiye shi a mahallinsa, sannan ta faɗa toilet ta yi wanka. A gurguje Uwani ta ci abinci saboda ta kusa makara, ta ɗauki jakar goyonta ta saka har za ta fita ta ji Jafar na faɗin. "Tafiya kuma babu sallama Uwani?" Tura baki gaba ta yi sannan ta ce, "To ba bacci kake yi ba! Ni dai na tafi Ya Jafar kar mu makara ." Tana gama maganar ta ji bugun ƙofa da sauri ta ƙarasa ta buɗe ƙofar, Auta ta gani a tsaye. Sai da Auta ta ɗan leƙa ta gefen Uwani ta yi ƙasa da murya ta ce.
"Ni fa na ɗauka ma yau ba za ki ba, tun da na ji shirun ya yi yawa na ce ƙila kina can kina tsinkar fure." Uwani ta ɗaka wa Auta duka a baya ta ce. "Wallahi Auta ki fita idona, kin raina ni da yawa me kike nufi." Auta ta ƙunshe baki ta ce.
"Abin da kike nufi mana, wai ma me ye sirrin ne yasin na ga yau har wani fresh kika yi. Ni fa ina tsoron wallahi kada mu je ana wa'ec kina fama da tumbi a gaba." Auta ta ƙarasa maganar ta yin gaba don ta san tsaf Uwani za ta sake kai mata duka, Uwani ta riƙe baki tana murmushi ta furta.
"An gaya miki mu haka muke? Ni fa Auta wallahi kin fi ƙarfi bari mu dawo da kaina zan samu Daddy, na gaya masa gaskiya gara Dr kawai ya turo." Da sauri Auta ta marairaice don ta san ba ƙaramin aikin Uwani ba ne ta aiwatar da abin da ta faɗa, ta ƙarasa ta saƙalo Uwani cikin kwantar da murya ta ce. "Haba matar yaya kada mu yi haka da ke." Uwani ta bushe da dariya ta ce. "Ashe dai iskancin na ki na ƙarya ne." Gaba ɗaya suka saka dariya.
Suna nan tsaye Ibrahim ya fito ya shiga mota, su Uwani suka buÉ—e suka shiga ya wuce da su makaranta.
Kamar yadda Malam Harisu ya faɗa ko da Lado ya wayi gari da asuba sai ganinsa ya yi ƙirjinsa ya koma daidai, ya jima yana hamdala ga Ubangiji. Kuma da asubar bayan Daddy ya dawo daga sallar asuba Lado ke sanar da shi yadda ya wayi gari.
Takardunsa masu muimmamci Jafar ya ɗauka bayan ya yi wanka ya ci abinci ya shirya, kai tsaye Bompai ya nufa domin cike duk waɗansu muhimman abubuwan da suka kamata. Sai yamma liƙis ya dawo a lokacin su Uwani suma sun dawo daga makaranta, Aunty ce ta sa Uwani ta girka wa Jafar tuwon semovita miyar kuɓewa ɗanya. Ya ji daɗin abincin don haka ya zage ya ci tuwon sosai, yana ci yana santi Uwani sai murmushi take bayan ya gama suka wuce sashen Daddy. Jafar ya wuce ɓangaren Mami Uwani kuma ta wuce ɓangaren Aunty, tana shiga ta samu Auta suna hira. Cikin zuga da shaida Auta ta ce.
"Aunty kin ga Uwani a tsohon daren nan ko ina ta bar Ya Jafar?" Aunty ta yi murmushi don ta fahimci da biyu Auta ta faɗi haka. Uwani ta kai wa Auta ranƙwashi a ka ta ce. "To munafunfun ai tare muke, shi ma ya shiga sashen Mami." Daga haka suka ci gaba da hira, ita kuwa dama Madina 'yar ɗakin Mami ce, saboda tun da Aunty ta zo gidan ba ta shiga sashenta ya kai sau biyar ba.