← Book details Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 71

Sashe 36

Uwani Yar Kashin Gwuiwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*BOJUWA HERBAL'S & SCENTS*
*Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.*
*Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah*
*Saiwowin tsumi*
*Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru*
*Saiwowin matsi gangariya*
*Original gadalin mata*
*Ƴaƴan gadali na asali*
*Original gumba*
*Tsumin Saiwowi*
*Tsumin kwakwa da Dabino*
*Igiyar alkairi*
*Zumar goran tula*
*Hakkin daka na musamman na asali*
*Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*.
*Akwai bridal package*
*Mai jego package*
*Ƴar gata package*.
*Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.*
*A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne*
*Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi*
*08032773332*
*Iyah Basiru na gaisuwa*😅

Tamkar korarru ko waɗanda suka dawo daga wurin da wata tarzomar yaƙi ta tashi haka 'yan biki suka koma gida, wasu babu ɗankwali wasu babu takalma. Daddy na daga saman barandarsa yana karanta jarida ya fara jin bugun gate da ƙarfi kamar za a ɓalle ƙofar, yana kallo Lado ya buɗe musu ƙofa a yanayin yadda suka shiga ne ya sa ya fahimci wannan taron shi ma ba a wanye lafiya ba. Bayan da suka shiga suka ba wa Dada labari ban da dariya babu abin da take sheƙawa, Mami kuwa takaici da baƙincikin da ta shiga har ya fi na ranar kamu. Domin ba ƙaramin muzanta ta yi a cikin ƙawayenta ba, uwa-uba kuma yadda ƙananun maganganu suka dinga tashi. Jafar shi da Safna babu wanda ya nemi wani a lokacin da ƙurar ta lafa sai a washegari suka haɗu. Ita ma Uwani a wannan ranar a ɗakin Dada ta kwana don ta gaji tuɓus jikinta sai ciwo yake yi, zuciyarta fes take ji don ta san ko babu komai yadda Mami da Shukra suka tozartata suka wulaƙantata suka laƙa mata sata ita ma ta fanshe abin da suka yi mata. Don haka a ranta ta furta, 'Ai ko yanzu kasuwa ta tashi, Ɗankoli ya ci riba.' Tun da ta san babu wani taro da za a kuma yi sai kuma na ɗaurin aure.

Washegari ne ya kasance ranar ɗaurin aure, kuma wurin ƙarfe goma sha biyun rana aka ɗaura auren Shukra da Salim. Ango ya zo da abokansa sai hotuna ake yi, Mami sai shiga ake ana fita cikin shigar alfarma.
Wurin ƙarfe huɗu ne kuma Salim ya aiko da motoci aka ɗauki amarya da 'yan kai amarya, sai dai ko da wasa Uwani ba ta yi gigin bin 'yan kai amarya ba. Hajiyan Safna kuma da Safna suka fito da jakunkuna domin jirginsu ƙarfe shida na yamma zai tashi. Kafin su fito sai da Daddy ya yi mata godiya sosai, sannan ya nuna mata bayan kwana biyu zai nemi mahaifin Safna su yi maganar auren su Jafar, bayan ya warware tun mahaifin Safna yana fama da matsalar ciwon suga. Saboda a nazarin da ya yi duk abin da Mami ta yi babu laifin Jafar a ciki hasali ma ya yi masa biyayya ya auri zaɓinsu, kuma suna zaman lafiya don haka shi ma zai yarje masa ya auri zaɓin ransa.

Sannu a hankali baƙi suka dinga watsewa kowa ya kama gabansa, Dada ma bayan bikin da kwana uku ta ce za ta tafi har da Uwani. Jin kalaman Dada ba ƙaramin farinciki ya dasa a zuciyar Jafar ba, da yake gabaɗaya suna zaune Dada take maganar Jafar da bai san da tonuwar asirin su Mami ba ya furta.

"Ni fa tun da Allah Ya ga ina zaune da yarinyar nan da zuciya ɗaya kuma Dada duk wannan bai yi miki ba, kawai ki ɗauke ta ki tafi da ita. Ƙiri-ƙiri fa Daddy kana gani ta kwashe kuɗin wurinka..." Shewar da Dada ta saki ce ta katse Jafar, sai da ta bi Jafar da kallon harara sannan Dada ta zayyane masa duk abin da ya faru. Daddy na gama sauraron Dada ya ɗora da cewa.

"Duk fa mahaifiyarka ta yi haka ne saboda waccen yarinyar Safna, dalilin da ya sa rannan na ce maka ba za ka aure ta. Amma na yi nazari na ga ba laifinka ba ne, sai dai a sannu zan É—auki matakin da ya dace a kan ki Saratu." Mami ta yi tsilli-tsilli da ido ta gagara yin magana, takaici ya mamaye Jafar yana mamakin abin da Mami ta aikata.

Bayan bikin Shukra da sati guda Jafar ya koma Lagos da aiki, a daidai kuma wannan lokacin ne aka nemawa Uwani makarantar da Auta take zuwa.
An yi wa Uwani Interview wasu ta ci wasu kuma ta faÉ—i, hakan ya sa hukumar makaranta ta nemi da ta saka Uwani a JSS 2 Amma Daddy ya ce a saka ta a SS 1, Zai nema mata mai lesson a gida a dinga koya mata abin da ba ta gane ba.
Da yake makarantar haɗe take Islamiya da boko ya sa Uwani ta samu sauƙin horon Mami, Asabar da Lahadi ne kawai babu makaranta.
Ranar Asabar Teacher Nuhu ne yake koya mata ɓangaren boko, ranar Lahadi kuma Mu'allim Abubakar yake koya mata abin da ya shafi ɓangaren addini.

Ana gobe Uwani za ta fara zuwa makaranta Daddy ya kira ta É—akinsa, bayan ta zauna ya furta.
"Mamana!" Uwani ta É—ago ta amsa sannan ya ci gaba da cewa.
"Kin san dai ke yanzu ba yarinya ba ce ko Mamana? Kin ga yanzu za ki fara zuwa makaranta, kuma mun yi wa malamanku bayanin kina da aure. Ki tsaya ki yi karatu sosai, kin taɓa ce mini aikin tuƙin jirgin sama kike so ko?" Uwani ta ɗan yi farr da ido sannan ta yamutsa fuska ta ce, "Gaskiya Daddy na canza, ni fa ina jin 'yar sanda zan zama don gaskiya na gaji da barazanar da Ya Jafar yake yi mini da bindigi. Ka ga idan na zama 'yar sanda sai mu nuna juna da bakin bindiga idan ya so ko harbe juna sai mu yi, ba shi kenan ba kowa ya huta?" Daddy ya yi murmushi ya ce, "Mamana kenan, aikin ɗan sanda ai ba don a yi wa juna barazana ake yi ba. Domin kare dukiya da rayukan al'umma ne. Ki dai yi nazari Mamana ki zaɓi wani aikin da kike ganin ya fi." Uwani ta gyaɗa kai sannan Daddy ya ce. "Alƙawarin awakinki da na yi miki kuma yau zan sa a fara aikin runfar da za a yi musu, zuwa nan da kwana huɗu na tabbata an gama komai sai na sa a kwaso miki su. Amma fa ba za a kawo kejin nan naki ba, zan sa dai a haɗa miki wani na ga wancen ya tsufa ya ma sunan zakaran nan na ki?" Da sauri Uwani ta ce.

"Wai Lawan mijin fanteka? Allah sarki Lawan wallahi Daddy na yi kewarsu, na san suna can suna saka Dada Magana." Daddy ya yi murmushi sannan suka ci gaba da hira.

A cikin kwanaki ƙalilan aka yi wa Uwani wurin mazaunin awakinta, kuma a cikin waɗannan kwanakin ne Daddy ya sa aka ƙara gyara masa ɗayan ɓangaren da ke kallon na Mami. Mami ta yi mamaki har ta gagara shiru a ranar da ta ga Daddy ya sa an kwaso mata wasu tarkacen da ta zuba a wurin.
"Daddyn yara ni fa ban gane wannan gyaran da kake yi ba, yaushe muka dawo gidan nan da za a ƙara gyara wannan sashen?" Daddy ya ɗan yi murmushi ya furta. "Saratu don zan gyara muhallina sai kin tutsiye ni da tambayoyi? Dama yau nake shirin sanar da ke Juma'a me zuwa ne za a ɗaura mini aure, ya kamata a sama miki ƙanwa tun da sannu a hankali yaran nan tafiya suke yi..."

"Ƙundun uban can! Mamman ni za ka tozarta ka wulaƙanta. Da tun da ƙuruciya ba ka yi mini kishiya ba sai yanzu da girma ya zo? Wallahi ba ka isa ba sai dai ka zaɓa ko ni ko matsiyaciyar da za ka auro." Daddy ya saki murmushi sannan ya nuna mata hanya ya furta, "Saratu ai ƙofa a buɗe take ni ba zan yi miki dolen zama da ni ba. Kuma idan muna da yawanci kwana aurena babu fashi, gara ma ki kwantar da hankalinki don ni ba zan yi auren nan don na wulaƙanta ki ba..." Kukan da Mami ta saki ne ya katse kalaman Daddy, ta miƙe rai a ɓace cikin kuka ta ce. "Wallahi namiji ɗan kunama ne tsakanina da kai ban yafe ba." Mami ta fice tana doko masa ƙofar da ƙarfi. Murmushi Daddy ya yi a fili ya ce, "Saratu ko rigima."

Abuwa 'ya ce a wurin marigayya Fatsime ƙanwar Dada, kuma tun gabannin auren Uwani ta dawo wurin Dada da zama sakamakon ta gama takabar mijinta da ya rasu. Shekararta Talatin da biyar, kuma duk tsawon shekarun da ta shafe da mijinta Allah bai taɓa ba ta haihuwa ba. Tun bayan bikin su Jafar Daddy ya fara gabatar da kansa a wurin Abuwa sai dai nauyinsa ya sa ta gagara amincewa, sai daga baya ne sannan ta ce masa su yi Addu'ar Allah Ya zaɓa abin da ya fi zama alheri. Kuma ko Dada ba ta san abin da yake tsakaninsu ba sai daga baya, a wannan lokacin ne ragowar mutanen cikin gidan suka fara jin raɗe-raɗin abin da yake faruwa. Da yake Mami ba wani fuska take ba wa facalolinta ba shi ya sa ko a tsegumi babu wanda ya taɓa tunkararta da maganar, saboda sanin wulaƙancinta ya sa kowa yake kama mutumcinsa.
Abuwa ta kasance mace mai sanyin hali ba ta hatsaniya ko kaɗan, tana da haƙuri sosai sai dai ba ta ɗaukan raini ko cin zarafi. Ƙaunar da Dada take yi wa 'yar uwarta Fatsime ya sa bayan mutuwarta ta dawo da ita kan Abuwa, saboda duk cikin 'yan uwanta ta fi shaƙuwa da Fatsime tun da a hannunta ta taso.
Chapter 36 · 0% Book details