← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 87

Sashe 81

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*_Ohhh Habibaties thank you so much for reading my book without paying me, but kusan aƙwai haƙƙina akan ku bana Allah ya isa bana tsinuwa,but kun fi son kubani a sanda komai ya ƙare maku ne? Idan kunfi son haka You can continue ur reading no WAHALA,Duk wanda yay niyyar biyana wahalarta just contact me 08119237616_*

A nutse Jalal yay parking motarsa a harabar gidan,cikin nutsuwa kuma ya sanyo ƙafafuwansa waje yana sanye da wani tissue ɗin yadi Brown mai wando da kuma comper sai babbar rigar,ya sanya wani Black covert shoe mai ƙyau, hannunsa sanye da agogon warist ga wata hula mai gashi-gashi da sanya saman sumar kansa,yay wani irin sihirtaccen ƙyau fuskarsa sai wani haske da annuri take fitarwa, kallo guda zakai masa kasan zuciyarsa babu daɗi, tunda yake a rayuwa damuwarsa bata taɓa bai yana ƙarara irin wannan ba,kenan hakan na nufin soyayyar JALILERH itace rauninsa? A haka yaci gaba da tafiya yana kwallon yadda securities suke dai-dai ta bindiga gudun kada wani ya kawo masa hari,yana gaf da sanya kansa cikin gidan yaji ƙarar notification tsayawa yay yana dubawa still message ne ta email ɗinsa inda ake rubuta *_ Congratulations ur excellence ka fitar da sabuwar ƙwangila,kuma kayi sa hannu a file ɗin da ake buƙatar kuɗi ki manin 10.7m thank you_*
Gabansa yaji ya faɗi tunani ya fara zuwar masa,tayaya kuɗi suke fita ba tare dasa hannunsa ba? Sannan idan ance yay sa hannu a yaushe yay,duk duniya babu wanda ya iya sa hannunsa sai Aryan,yana kuma da tabbacin Aryan bazai taɓa yi masa haka ba,tattara bayanin komai yay ya ajjiye gefe domin abubuwan da suke cikin zuciyarsa sunyi masa yawa,kai tsaye ya fara shiga cikin gidan tunda ya nufi babban parlour ya kejin gabansa na faɗuwa a haka ya daure ya shiga lokacin tuni anyi Asr magrib na shirin gabatuwa,yana shiga idanunsa ya sauka akan Zulfa wacce take ƙwance jikin Abbou sai rusar kuka take tana faɗin "where is he? I want to see my son" kasa shiga yay sai da Papa yace "wlcm my grandson" gaba ɗaya suka ɗaga idanunsu suka kallonsa,wani murmushi Abbou yay kafin ya miƙar da Zulfa yace "look Hubby"ya faɗa yana nuna mata inda ƙyaƙƙyawan yaronta mai kama da ita sak yake tsaye, maƙale kafaɗa tayi taƙi buɗe ido,ganin hakan yasa Abbou cewa "ur son is here"da sauri ta Miƙe tsaye tare da kallon inda Jalal yake tsaye,kallon juna suka farayi tana kallon photocopy ɗinta komai nata ya kwashe shi tatasss babu abinda ya bari,shima kallonta yay yana mamakin a ransa musamman kamar da yaga sunayi,a hankali kuma Jabir yace "My son she's your mother,yeah! She's your real mother" da sauri ya ƙara kallon Zulfa tayaya wannan matashiyar matar zata haifesa gaba ɗaya babu alamun girma a gare ta,bai aune ba yaji ta faɗa jikinsa tare da ƙanƙamesa ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciya...

*Nimcyluv*
8/1/21, 5:09 PM - Buhainat: UCL NE
_112-113_
Lumshe idanunsa Jalal yana jin yadda Zulfa ta rirriƙesa tana faman rusar kuka,kasa koda mutsi yay haka kuma ya kasa fahimtar maganganun so Abbou, kallonsu kawai yake,amma cikin zuciyarsa yana jin wani sanyin da bai taɓa jin irinsa ba yana rasa ko ina na jikinsa,gaba ɗaya ya nemi ɓacin rai dake damunsa ya rasa,ganin yadda yaƙi taɓa ta yasa ta juyo ta kalli Abbou tare da ɗan kwaɓe fuskarta kamar yarinya tace "ka gansa ko?" Gaba dariya sukai mata sbd yadda ta marai-raice fuska kamar ƙaramar yarinya, Jabir ne ya miƙe tsaye tare da kallon Jalal yace "talk to her she's your mother Son"waro idanunsa waje yay domin sai yanzu yaga zallar kamarsa da ita,da sauri yay ƙasa da kansa tare da janye jikinsa daga nata haka nan yaji wata kunyar mahaifiyarta sa ya kamasa,wajan Abbou ya ƙarasa yana zuwa ya kifa kansa a saman jiyarsa ya shiga sauke ajjiyar zuciya da sauri²,kansa Abbou ya shafa a hankali kuma yace "Muhammad mahaifiyarka kake gudu?"girgiza kai Jalal yay yana ƙara rufe idanunsa, Abbou yace "nayi tunanin zakafi kowa farin ciki da ganin mahaifiyarka?ko sbd abinda akai maka kwanaki?" A hankali Jalal yace "Abbou ni kunyarta na keji fa" ɓata fuska Abbou yay yace "matar tawa kake jin kunya ko?" Ƙara suwa wajansu Zulfa tayi tare da zama kusa da Abbou sosai kamar zata shige jikinsa ta leƙa fuskar Jalal da sauri ya rufe idanunsa tace "wai me yake cewa?" Kallonta Abbou yay yace "wai kunyarki yake" bakin Abbou ta kala kamar bata fahimci abinda yake cewa ba sai kuma tace "mene sunansa?" Nuna mata Papa Abbou yay yace "kinga sunan wanda yaci" Murmushin jin daɗi Papa yay sosai yake farin ciki da ganin full family nasa, lumshe idanunta tayi sai kuma tace "to meye sunan?" Kafin Abbou yay magana Jabir yace "matar yaya sunan ɗan naki Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo,kuma Governor na garin Ibadan" waro idanunta tayi sosai kafin tasa hannunta cikin sumar kansa ta shafa,ajjiyar zuciya ya sauke,a Kuma tace "Ma sha Allah! Allah! Raya mana Muhammad kuma my boo" lumshe idanunsa yay har cikin ransa yaji daɗin sunan data sanya masa, idanunsa a rufe ya miƙe daga jikin Abbou kamar zai tashi sai kuma yay saurin shigewa jikin mahaifiyarsa ya rungome ta,da sauri itama ta rungomesa cikin rawar murya yace "Ammi"sai kuma ya fashe da kuka yana tura kansa cikin jikinta,kuka itama ta saka tana faɗin "am sorry my boo am sorry double sorry boo" murmushi kawai Abbou yake shima idanunsa ya cika da hawaye su yake kawai ya keɓe da matarsa yaji ɗumin jikinta ko saiji sanyi a ransa, luff Jalal yay jikin mahaifiyarsa wanda ya rabonsa dajin ɗumin jikinta tun yana cikinta, kansa kawai take shafawa tare da bubbuga bayansa, cikin ƙasa da muryarsa tace "ina jikoki na?" Da sauri ya kalleta sai kuma ya ɗauke idanunsa yana kwaɓe fuska tamkar wanda zai ƙara fashewa da wani kukan, Mama ce tai saurin faɗin "kaji sallama wanne jikoki kuma? Banda auren yanzu masa a bazata wannan yana da niyyar aure ne? Ai sai dai kiyi fatan Allah ya kawo masu albarka,tunda naga fara a fuskarsa nasan yau ya cika namiji" ya ilahi wata kunyace ta kama Jalal wacce bai taɓa jin irinta ba, Wannan tsohuwar ta fiya magana da karan bani,kowa ya tambaye ta ohhhu!?" Cikin farin ciki Zulfa ta miƙar da Jalal daga jikinta idanunta a kansa tace "is that true my boo? Da gaske ka zama ango? Tell me please ina Daughter ɗin?" Ƙasa kawai yay da kansa domin bashi da amsa gaba ɗaya Amminta sa ta ɗaure sa da jijiyoyin ka jikinsa, ƙara rungome sa tayi tace "ma sha Allah, Allah ya baku zuri'a ta gari mai albarka, I'm going to be grandmother soon,sannu my boo" Abbou dry kawai yakewa matar tasa domin gaba ɗaya ta gigice da ganin yaron nata,shi kam baiyi mamaki ba domin yafi kowa sanin matarsa ƴar boko ce sosai babu ruwanta da idanun jama'a,banda haka har uban miji da mahaifiyarta na wajan take faɗin haka,peak taiwa Jalal a kumatu tana ƙara rungomesa,shima kwanciyarsa yay jikinta sbd sanyi da kuma daɗin daya keji,wata nutsuwa na saukar masa yana jin nada ban da sauran kwanaki,sai lokacin idanun Zulfa ya sauka akan Irfan haɗa ido sukai yay mata Murmushi itama tai masa ba tare data ɗauke idanunta ba, kwallon Abbou tayi tace "Hubby waye Wannan?ina Anty Salmerh?" Ta jera tambayar ga Abbou lokaci ɗaya,zama ya gyara yace "wannan Irfan kenan,kuma su ukune dashi da Imran sai Aryan su uku ta haifesu lokaci ɗaya,gaba ɗaya yaran Salmerh ne"da sauri Zulfa ta kalli Irfan cikin farin ciki tace "come closer my dear" miƙewa yay yazu wajanta yana zuwa ta haɗa su shida Jalal ta rungomesu, gyara zama Abbou yay yace "zan baku labarin yadda nabar wannan Birnin da kuma yadda na samu mata har biyu na aura" gaba ɗaya suka gyara Jalal yana ɗan zare jikinsa daga na Zulfa,hararan wasa tai masa da sauri kuma ta maidashi jikinta sbd gani take kamar zata ƙara rabuwa dashi, Abbou ya fara da faɗin.
Chapter 81 · 0% Book details