← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 87

Sashe 27

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a parking space Jafar yyi parking motar domin Jalal bai cika son securities su dinga binsa ba,ana gama parking Jafar ya fito ya buɗe masa motar yana fitowa ya kaiwa Jafar duka yace "ɗan iska kamar na sashi,kada ka sake buɗen mota ina da hannu" cikin tsokana Jafar ya sunkuyar da kansa ƙasa yace "am so sorry ur excellence ban ƙarawa" banza yyi masa ya shige ciki a main parlour ya samu kusan duk ƴan gida harda Nusaibat,tana ganinsa ta sunkuyar da kanta ƙasa kafin tace "ina yini yaya" baiko kalli inda take ba ya huce wajan Mama ganin tana sharar hawaye hadda majina, kallonta yyi da alamar tambaya kafin yyi mgn Nihila tayi saurin faɗin "yaya wai mgnar da kayi ta kema kuka fa" wata majinar ta face a bakin zaninta kafin ta kalli bobo tace "Ashe haka kake da zcyar imani da tausayi buba? Nidai kaya feni dan har zcyta ina maka kallon mara mutunci musamman idan kaƙi siyomin wannan abun na zoƙa,ahhh to bazan munafurceka ba tunda ba ubana bane kai,amma dai angona kayi hqr kada na tafi lahira da zunubinka" dry Jafar yyi yana zama a kujerar dake kallon Nihila yace " Thanks God yau Mama ta yadda zata mutu" waro idanu tayi waje kafin tayi saurin miƙewa tsaye tana karkace ƙwankwaso😂 tace "Tabbas mutuwa sai dai ka gani a kanka,amma wlh ni yanzu na fara zama a duniya"huuu nida nake saka ran yin sabun aure na fice na bar maku gidanku" dry sukai kafin ta ɗura da "ahhh to nidai babu ruwana yuuuu duniyar gaba ɗaya nawa take" tana faɗin hakan ta shige part ɗin ta, Jalal bai tsaya ba yyi hucewarsa part ɗinsa, Jafar zama yyi suka ci gaba da hira dasu mummy da Mameey,yana shiga part ɗin nasa ya fara zare kayan jikinsa bayan ya gama ya saka su a inda yake ajjiye kaya masu datti,kai tsaye bathroom ya nufa ya sakarwa kansa shower sosai yaji daɗin ruwan sbd sanyin dake ratsashi yana sauka akan fresh skin ɗinsa,Lamir ne zaune shida Gwamna Faisal Lawan suna tattaunawa akan yadda zasu lalata zaɓen da za'ai a gobe,gaba ɗaya Jalal ya wargatsa masu plan ɗinsu,tun yana ganin abin wasa har ya gagara fahimtar abinda zai yi, murmushi yyi ya kalli Faisal Lawan yace bani kunanka kaji,da sauri ya miƙa kunna sa wata dryar mugun ta sukai a tare kafin gwamna Faisal Lawan yace "gsky Lamir baka da imani,kuma kasan idan wannan abun yyi yadda muke so kashin Muhammad Jalal ya bushe" tafawa sukai Lamir yace "ahhh niɗin na wasa ne" fitowa yyi cikin shigar sa ta shan iska,daga shi sai wando three gaiter ko singlet babu jikinsa,sai fresh skin ɗinsa wacce take ta sharning,zama yyi kafin ya kunna t.v ya fara kallon labarai har lokacin shirarsa ake watsa,inda akai translation
É—inta da harshe kala-kala, wayarsa ya É—auka yyi dailing number Mummy ringing É—in farko ta É—aga tace "my love ya akai?" numfashi ya sauke yace "Mom yunwa,bawa beb ko wannan yarinyar su kawo min part É—ina" murmushi tayi tace "ok" kallon Jalilerh tayi tace "my dear jeki haÉ—awa Uncle É—inki abinci" kafin ta tashi Abbou yace "dear zauna abinki Nusaibat jeki kai masa..

Miƙewa Nusaibat tayi zcyarta fal farin ciki, kitchen ta shiga ta ɗauki tray ta haɗa masa dukkan abinda ya dace dashi, bayan ta gama ta nufi part ɗinsa,da idanu kawai Jalilerh da Nihila suka bita, Abbou murmushi kawai yyi kafin ya miƙe ya nufi part ɗinsa,yana zaune yana operating system ɗinsa yaji anyi sallama,jin baƙuwar murya yasa ko ɗaguwa baiyi ba,yace "Wasallam" yana faɗin hakan yaja bakinsa yyi shuru,ƙarasa shiga tayi tare tajan table ta ajjiye masa tray ɗin abincin akai,durƙusawa tayi kafin tace "ina yini yaya?" banza yyi mata kamar baiji me tace ba,kanta a ƙasa ta ƙara cewa "yaya" da sauri ya juya ya kalleta kafin cikin ɗaga murya yace "out!!...
6/10/21, 1:10 PM - Buhainat: _Duk yadda kaso kayi rubutu perfect ba tare da wani matsala ba hakan ba faruwa,nayi mamakin yadda na kasa gane kuskuren, sannan nai mmkin yadda marubutan da suke karantawa suma suka kasa ganewa,sai wata daban ta gane, a Nigeria muna da state 36 muna da OYO wacce ta kasance state,sannan muna da IBADAN wacce ta kasance Capital a garin OYO, nace *Muhammad Jalal Kabeer bobo* na neman takarar shugaban ƙasa president kenan,bayan idan president ke nema sai dai nace na Nigeria baki ɗaya😂,a nan kuskuren yake *Muhammad Jalal bobo* ta karar governor yake nema a IBADAN ba president ba,so Please gusy babu baya kuskure aimin afuwa, shi RUBUTU kamar rayuwa ce,kamar yadda babu wanda yasan mene zai faru da mutum gobe ko jibi,haka babu wanda yasan mene zai faru next a cikin littafi abinda muka sani labarin daga farko zuwa ƙarshe an riga da an gama tsara shi,rubutune kawai ya rage✍🏻kuma shima in sha Allah babu tsayawa sai lokacin da Al'ƙalamina yaje ƙarshen labarin_

Uncle ne is not free is 300 0116886423 sulaiman Naima s union bank, evidence of payment 08119226716

_36-37_

Da sauri taja baya sbd tsawar da taji yyi mata, kafin ta kallesa tace "Abbou ne yace na gaisheka fa,me nai maka ne da baka son kulani yaya"ci gaba yyi da latsa system ɗinsa,ganin bashi da niyar kulara yasa taja jikinta zuwa parlour,tana fita ta samu Jalilerh zaune ita kaɗai ta rufe idanunta,zama tayi tace "Jalilerh ke ɗaya ce?" buɗe idanunta tai kafin ta ɗauke kai tace "eh" murmushi tayi tace "kinga na daɗe ko,yaya ya tsaidani wai muyi Shira"kallonta kawai Jalilerh tayi dan a halin bobo yanzu babu abinda bata sani ba tace "yana da kyau ai" Nihila ce ta sakko tana faɗin "har kin fito?,naje ɗaki ɗauko laptop ɗina zan nunawa Jalilerh wani abune"miƙewa tayi tace "Nima zan huce ne,ashe haka bobo yake da kirki yau kam munsha Shira"waro idanu waje Nihila tayi kafin tace "Allah sarki" sallama tayi masu tabar gidan zcyarta cike da takaicin da kuma haushin abinda bobo yyi mata,tana fita ya ajjiye system ɗin tare da miƙewa tsaye ya nufi bedroom kai tsaye bathroom ya shiga ya ƙarasa gaban sink ya wanke hannunsa,yana fitowa ya zauna gaban table ɗin tare da buɗe wermers ɗin,dambun shinkafa ya gani wanda yaji albasa da zugala da gyaɗa,sai tashin ƙamshi yake yaji kifi,yana gama zubawa a plat Jalilerh na turo ƙofar parlour'nsa tana shigowa,zama tayi kusa dashi tare da yin shuru ta sunkuyar da kanta ƙasa,spoon ya ɗauka ya ɗibi dambun tare da kaiwa bakinsa, daɗi da kuma garɗin gyaɗar daya ratsa kunansa yasa yyi saurin lumshe idanunsa,tunda ta shigo bai kalleta ba a hankali yaci gaba tacin dambun har yaci rabi, ɗaya wermer ɗin ya buɗe yaga zallar kayan cikin rago wanda akai farfesun yaji daddawa da kayan ƙamshi, spoon yasa sau uku yaci ya rufe wermer ɗin, miƙewa yyi ya nufi ƙaramin fridge ɗinsa ya ɗauki bottle water mai sanyi ya ɓalle murfinta sai da ya shanye tass sannan ya ajjiye emty bottle ɗin a side ɗin fridge,sai a lokacin idanunsa suka sauka akan ta yanzu tana durƙoshe ta cure waje guda jikinta duk rawa yake gargasar dake jikin ta duk sun mimmike,idanunsa ya ɗauke tare ɗaukan remote ya sauya channel zuwa sunna t.v yaci Sa'a ana karatun Kur'ani,yana kaiwa yaje kujerar da yake ya zauna.

Miƙewa tayi da sauri zata fice daga ɗaki shima da sauri ya miƙe ya nufi inda tayi tako ɗaya yyi zuwa biyu ya zafkota,dukkan ƙarfin ta tasa ta hankaɗesa baya yyi yana mai dafe kujerar dake kusa dashi,hakan ya tabbatar masa ba ƙarfin ta bane, ƙara suwa yayi wajan ta da sauri ya samu harta isa parlour,tsaye yyi sbd kokawar da yaga sunayi ita da Aryan gaba ɗaya ta wajigasa,jingine jikinsa yyi da jikin bangon tare na daɗe hannunsa a ƙirjinsa ya zoba masu idanu.

Mama dake rakuɓe a gefen kujerar jikinta duk rawa yake ta kalli Nihila itama da take a tsorace cikin ƙasa da murya tace "wlh kada ki yadda ta ganki,gaba ɗaya aljanun zasu dawo kanki,Nima ina budurwa haka wata tayimin wannan muguntar,sai gani da yada zani,kee abindai babu kyau,ba kiga yanzu na ɓuya ba"

Kallon Nihila tayi kafin tai magana taji an ƙwala ihu tare da zubewa ƙasa,ihu Mama tayi itama tare faɗin "wa'innahu sulaimanu wa'innahu bisimillahir rahim" shuru itama Nihila tayi tare toshe bakinta hawaye na zuba ta cikin idanunta, Abbou dake tsaye shima ya kalli Jalal yace "Bobo kana ganin abinda take,tana shan wahala fa,kuma Aryan ya kasa da ita" tagumi Mummy tayi abin na mata mmki Ita dai tunda take ba'a taɓa aljanu a gabanta sai yanzu dan duk ta tsorata tausayin Jalilerh ya cika mata zcy, Aryan ne ya kalli Abbou yace.

"Abbou zan iya kula da ita kabar yaya ya huta"kallon sa Mameey tayi tace "rufen baki kalli yadda kake haɗa zufa tun ɗazo sai kokawa kuke kace Zaka iya" Mummy tace "no kibarsa mana,ai kinsan ƙarfin aljanu dana mutum ba ɗaya bane" Shidai Jalal na tsaye yana kallon kowa da ido,ana haka Lamir yyi sallama ya shigo, kallon su yyi tare faɗin "lfyanku kowa?" Abbou ne yace "inafa mutanan ɓoye suka fara damun dear a ƙwana biyun nan" kayan hannunsa ya ajjiye saman sofa kafin ya ƙarasa inda take ƙwance yace "ai ba'a barta haka ba, aƙwai wani malami dana sani sai a kaita can" sai a lokacin Jalal ya ɗaga kai ya kalli Lamir kallonsa yyi shima kafin yace "sannu bobo" jinjina kai kawai yyi kafin yasa hannu ya shafi sumar sajensa a hankali kuma ya fara takawa zuwa inda take ƙwancen yana zuwa yasa duk hannayensa ya ɗauke ta cak,kai tsaye part ɗinsa ya nufa,wani numfashi Aryan ya fesar tare dabin Jalal da kallo shi kaɗai yasan abinda ya keji a ransa,yana zuwa parlour'nsa ya shimfiɗeta a saman duguwar sofa kafin ya zauna gefen ta tare ɗagota zuwa jikinsa.
Chapter 27 · 0% Book details