← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 87

Sashe 35

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da wani kallo Aryan ya bisa yana jin yadda zcyarsa keyi masa zafi da ƙunci a cikinta,lokaci guda kuma wani abu ya ɗarsu a ransa miƙewa yayi jiki a saɓule ya miƙe ya nufi part ɗinsa zcyarsa na ai yana masa abubuwa marasa daɗi.
Jalal yana shiga ya zarce cikin bathroom ɗinsa ya watsa ruwa tare da yin brush ya ɗaura alwala,wasu fararan kayan bacci ya saka masu ƙyau kana ya fesa turare,yana cikin fesawa yaji ana taɓa ƙofar sa,kafin ace "Salumualak" tunda yaji ya nayin gaisuwar yasan cewa itace,wata kujera dake kusa da bed ɗinsa ya Zauna tare da cewa "come in" shigowa tayi hannunta riƙe da wani jug da kuma ludayi, wajansa ta ƙara sa ta zauna gefen bed tace "Uncle gashi inji Mameey" kallonta yayi ba tare da yace komai, wajan ta nufa tana zuwa ta zauna saman cinyarsa yana jinta ba kulata yaci gaba da latsa wayarsa can yaji ta taɓa beard ɗinsa tace "Uncle" ba tare daya kalleta ba yace "uhm" tace "Uncle kai baka aske wannan gashin ne?" Kallonta yayi yace "tashi a kaina"turo baki tayi tace "Uncle to kada ka aske mana" ajjiye wayar yayi tare dasa hannunsa a shoulder ɗinta yace "the you like it?" Ya tambaya yana zare ribbon ɗin kanta tace "Uncle naka yafi na yaya Aryan ƙyau ina so,kaima kana kitso dashi"Kallonta yayi tare da ajjiye ribbon ɗin gefe yace "wane ya gyara sumar?" Tana jan gemunsa tace "Mameey ce"yace "eyeee" yana faɗin hakan ya zame ta daga jikinta yace "ohh" yana faɗin haka ya fara shan damammiyar furar da akai masa,shuru tayi tana kallon sa ganin zai shanye furar yasa tayi saurin faɗin "Uncle nima" ludayin ya ajiye tare dasa hannu ya rangwashi kanta yace "ba ƙyau roƙo"baki ta turo gaba zatai kuka yayi saurin riƙe lips ɗin nata kafin ya ɗauki ludayin ya ɗebo furar cikin sanyin murya yace "haaa"kaita girgiza masa hawaye na fita ta fuskarta,ajjiye jug ɗin furar yayi kafin yasa hannu ya ɗauke ta cak zuwa kan cinyarsa,hannu yasa ya ɗago haɓarta yace "meye?"kuka ta fashe dashi tare da lafewa a jikinsa lumshe idanunsa yyi kafin ya hankali ya sanya hannayen sa zuwa faffaɗan waist ɗinta cikin wata murya mai amoo ya ɗura lips ɗinsa a dai-dai kunanta yace...

"Kamar yadda na gaya maku idan najee ending na book 1 zan ɗauki ƙwana biyar ko baƙwai kafin mu fara book 2 to allahamdulillah yau nazo ƙarshen book 1 kuyi afuwa zuwa ranar da nace maku🌚🌚ina maku sahihiyar ƙauna

_Uncle ne na kuɗi ne akan barshi mai sauƙi 300 ga masu son vip 600 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616_
6/16/21, 8:16 PM - Buhainat: _UNCLE NE_

_BOOK 2_

50-51

"En matan Uncle"
Shuru tayi masa kafin a hankali ta miƙe daga jikinsa ta nufi fita daga cikin bedroom ɗin, murmushi kawai yayi tare dasa hannu ya shafi sajen fuskarsa zuwa gemunsa,baiko kailli inda take ba har ta fice daga cikin part ɗin nasa baki ɗaya,tana fita taji an riƙe hannunta cikin tsoro ta buɗe baki zatai kuka yayi saurin sanya tafin hannunsa ya rufe mata baki tare dasa hannu ya ɗaga ta cak ya nufi cikin part ɗinsa da ita,gaba ɗaya Jalilerh ta gama tsorata domin har yanzu bata san wanene ba,yana zuwa cikin parlour'nsa ya direta saman sofa tare da zama kusa da ita, ajjiyar zcy ya sauke tare dajan idanunsa ya rufe su ruff hannunsa dake cikin nata ta shiga zare kafin a hankali ta buɗe idanunta,wata wahalalliyar ajjiyar zcy ta sauke sbd ganin Aryan zaune kusa da ita ba wanda take tunani ba, hannunta ta zare kafin ta turo baki gaba cikin Muryar shagwaɓa tace "Yaya me nai maka? idanunsa ya sauke a kanta kafin yace "da akai me?" Ya faɗa yana ƙara kama hannunta, ƙara zare hannunta tayi tana jaa baya kaɗan tace "daga ɗauke ni" jinjina kai yyi yace "ok me kikaje yi part ɗin Yaya Jalal at this time?" Kallonsa kawai tayi ba tare da tace komai ba,zamansa ya gyara sosai da inda zai dinga ganin yadda zata fahimci maganarsa yace "look Jalilerh abinda kike a musulunce is not good,babu ƙyau mace ta dinga rabar jikin wanda ba muharraminta ba,domin hakan babban zunubi ne,ance idan mace dana miji suka haɗu waje guda to na ukunsu sheɗan ne,kinga indai har sheɗan yayi nasarar shiga tsakaninku something bad is gonna happen Allah ya kiyaye ba fata nake ba,amma ki daina raɓar jikinsa kinji darling?" Kallonsa kawai take with so surprised kafin tace "to ai bai ce bai so ba" ware idanunsa yayi yana sauraran zallar wawta irinta ta tayaya mutum kamar Jalal dan mace ta raɓesa zai ce bai so?tayaya mutum mai shekara sama 30 zai ce mai son jin ɗumin mace?and tayaya bobo zai buɗe baki yace ta daina hawa jikinsa? Ai bazai taɓa yiwuwa ba, Aryan yace "eh, ƙilan bai son takuraki ne,ko kuma yana jin daɗin yadda kike masa" da sauri ta kallesa tace "daɗi kuma?" Gira ya ɗaga mata yace "kin san mene?" Kaita girgiza masa alamar "a'a" yace "ita mace ai gubace abu kaɗai zai rabeta ta lalace shima abin ya lalace, naji Mama tace da zarar mace ta fara zama cikakkiyar mace ta fara al'ada to dole rayuwarta zata zama a killace dan idan har ta sake namiji ya taɓa jikinta lokacin da take al'ada to Tabbas zata iya ɗaukan ciki"da sauri Jalilerh ta ƙara kallonsa zcyarta na bugawa da ƙarfin gsken,kallonsa kawai take ta gagara cewa masa komai,a hankali kuma ta miƙe tsaye tare da ficewa daga cikin part ɗinsa ta nufi sashin su.
Wani lalataccen murmushi aryany yayi kafin ya koma jikin sofar ya ƙwanta yana jin kamar hakan da yayi ya shiga matakin farko cimma burinsa...
Washe gari da yamma Jalal bobo ne Zaune a main parlour watching TV yana yi yana kallon agogon hannunsa,wajan 10minutes bayan an kammala labaran ya miƙe tsaye yana gyara zaman babbar rigar jikinsa, Mummy ce ta sakko hannunta riƙe da wani cup ta kallesa tace "badai fita zakai ba?" Jinjina mata kai kawai yayi yana mai ƙara kallonta yace "ina baby ne?" Mummy tace "kasan yau Monday tana school,kuma exam zasu fara so tun 7 tabar gida" yana fita waje yana "ok I think zan biya ta makarantar so kada a tura wani drever" da murmushi a fuskar Mummy tace "to, Allah ya kiyaye hanya sharri mutum dana ƙarfe ya tsare ka dashi" da "Ameen" ya amsa ya fita drever na zuwa da sauri ya buɗe masa sabuwar motarsa mai ƙirar marsandi,back seat ya shiga ya zauna yana zama ya ɗauki jaridar daily trust ya fara dubawa,kai tsaye gidan gwamnati suka nufa,a parking lot drever yayi parking,ka san cewar shi ɗaya ne ko securities ya hana su biyo sa yasa drever yayi saurin fitowa ya buɗe masa murfin motar,fararan ƙafafuwansa ya fara fito dasu kafin a hankali ya fito gaba ɗaya, kallon drever'n yayi yace "thank you" drever'n yace "ur wlcm sir" da haka ya nufi cikin gidan gwamnatin domin zuwa wajan meeting ɗin da aka haɗa na gaggawa wanda zallar governor's zasu hallarta da sabbi da kuma wanda suke shirin zama governor ɗin nan da wasu watanni,cikin nutsuwa da kamala ya shiga cikin hall,kusan kowa yazo shine ya rage kujera aka ja masa ya zauna yana zama shugaban meeting ya fara addu'a tare da faɗin"Ma sha Allah munawa dukkan ƴan tarkarinmu Barka da shigowa wannan wajan,sannan muna miƙa gaisuwar ban girma ga shugabaninmu wanda suka kasan sune suke jagorantar mu a yanku kafin lokacin zaɓe yazo,abu na gaba shine,muna mai sanar ku cewa nan da wasu watanni za'a gabatar da zaɓe wanda a nanne za'a ga wanda yake da rabon samun wannan kujera,zuwa yanzu idanun mutane suna kan waɗan nan mutanan guda biyu wato Governor Mubarak Yahya cibo da Muhammad Jalal Kabeer bobo sabun ɗan takara kenan a jam'iyyar D.R.P,dukkan wata matsalar mu kune sbd rashin jituwa da baƙwai yi,sannan daga gobe mun bawa ko wannan ko damar fara campaign,wannan shine abinda ya sanya na kiraku domin bana son a samu wata matsala daga ɓangaren ko wannan ku" governor Mubarak Yahya cibo yace "Ni nayi alƙawarin babu wata damuwa da zata faru ta ɓangare na Allah ya bawa mai rabo Sa'a,ya kuma taimake mu baki ɗaya" mutanen wajan suka amsa da "Ameen" shugaban wajan ya kalli Jalal da idanunsa yake a lumshe sai ka rantse bai san mene akai magana akai ba,sbd gaba ɗaya hankalinsa ba akansu yake ba yace "what about your side Muhammad Jalal Kabeer bobo?" Numfashi ya fesar tare da ware manyan idanunsa ya kalli kowa kana ya ɗauke kansa yace "basai nace komai ba,sbd abunda zan nema a yanzu yana da sauran lokaci" kallonsa governor Mubarak Yahya cibo yayi yace "ai gwara ka faɗa yanzu aji ko" ba tare daya kallesa ba yace "uhm da sauran time" yana faɗin hakan yayi masu sallama ya fice daga cikin hall ɗin,gaba ɗaya suka bisa da idanu da haka kowa ya miƙe yay waje Jalal na ƙoƙarin shiga cikin motar yaji ance "hey mr arrogant" tsayawa yayi sbd yasan ko waye,matsawa kusan sa Mubarak Yahya cibo yayi yace "kabi a sannu domin kana son shiga gonar da bana ka ba,bana ragawa kowa duk yadda nake da mutum indai a kan muƙamina ne zan nuna ban san wanene shi ba,ko zan tabbatar maka da soon tunda kai ka nunawa duniya kana son zama lfy,great ni hakan yyimin daɗi zan fi jin daɗi buga game ɗin yadda nakeso,da yau zuwa ko wannne lokaci ka sanya ranka cewa idanun Mubarak Yahya cibo yana kanka,all the best"
Chapter 35 · 0% Book details