← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 87

Sashe 33

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsayawa yyi yana kallon gawar Hibba wacce aka gama sakawa cikin kabarinta za'a rufe ta a hankali yace
" بسم الله وعلى سنه رسول الله"
_Bisimillah wa'ala sunnati Rasulullah_
(Da sunan Allah,kuma akan sunnar Manzon Allah)
Ana gama rufeta da ƙasar wajan ya kuma cewa.
"اللهم اغفر لله اللهم ثبته"
_Annabi (S.A.W) ya kasance idan aka gama binne mamaci sai ya ce: *Ku nema wa ɗan uwanku gafara,kuma ku roƙa masa tabbatuwa,domin yanzu ne ake yi masa tambayar kabari* Ya Allah ka gafatar masa,Ya Allah ka ba shi tabbata_
Ana gama rufe ya miƙe tsaye akai addu'a dashi gaba ɗaya mutane sai ɗaukan photonan suke, kafin su bar wajan tuni an watsa labarai "Muhammad Jalal Kabeer bobo mai neman takardar kujerar Gwamna a garin ibadan a jam'iyyar D.R.P ya ziyarci jana'izar ƴar gidan Governor Mubarak Yahya cibo gwamna mai ci a yanzu a jam'iyyar D.P.P aka sanya photo nan su.
Kai tsaye gidan aka koma hadda Jalal yana shiga ya nufi inda Mubarak Yahya cibo yake .

"ان الله ما أخذ،واله ما أعطى،وكل شيء عنده بأجل مسكر فلتصبر ولتحتسب."
_haƙiƙa abin da Allah ya ɗauka nasa ne,kuma abinda ya bayar shi ma nasa ne,kuma kowa ne abu a wurinsa yana da ajali abin ambato..,sai ta yi haƙuri ta nemi lada *(na haƙurin rashinsa da ta yi)*_
ya faɗi haka kuma yana ƙarawa da "Allah ya jiƙanta yayi mata rahama" gaba ɗaya jama'ar wajan suka amsa da Ameen hadda shi Mubarak Yahya cibo da Lamir,haka akai masa jagora zuwa cikin gida yaywa Hajja Ayushert ta'aziyya,gaba ɗaya matan parlour'n kallonsa suke suna jinjina ƙyansa da kuma karamcinsa,yana fitowa securities ɗinsa suka mara masa baya har zuwa motar Lamir ne ya ƙarasu wajan yace "ko zaka rage min mota ta samu matsala kallonsa Jalal kawai yyi kafin ya sauke numfashi yace...

_you can pay only 300 naira to read a wonderful story that give you so much enjoying, you can continue Reading but you must pay me the day of judgement🌚_

_300 for nrml grp 600 for vip 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616_
6/10/21, 1:21 PM - Buhainat: 48-49

_Rayuwa abace mai wahalar gaske,haka zaman takewa yana da wahala sha'ani,wanda kake tunanin zai zama kariya gareka sai kaga shike neman kaika ƙasa ba tare daka sani ba,duk yadda kake da mutum kayi ƙoƙarin riga wani muhimmin abu ɗaya shafe ka ba komai ake faɗa ba,kamar yadda babu wanda yasan mene zai faru dashi gobe...haka babu wanda yasan mene zai faru a cikin littafi hatta ga marubuciya kawai a duk yadda salon labari yazo maku a haka za kuyi ƙoƙarin amsar sa,muna tafe ne miƙa buɗe shafin rayuwa a cikin labarinmu,bazan iya cewa naje tsakiyar labari ba a'a,haka kuma bazan iya cewa banje tsakiya ba, aduk sanda ku kaga marubuci yayi jin kiri wajan sakin labarinsa Tabbas aƙwai wani dalili daya sanya yayi hakan...zan iya cewa a ko wanne lokacin kuma a ko wanne irin yanayi zaku iya jin salon labarin ya sauya daga yadda kuke tunani,dan haka dukkan abinda zaka ɗauka ka bawa marubuci baza ku biya sa abinda yake ba,kun sani sai dai wasu suyi watsi da sanin su,in Sha Allah ina zuwa ƙarshe book 1 sai nayi ƙwana biyar ciff banyi posting dan haka You guys get ready🌚🌚_

Never mind,shiga motar Lamir yyi suka nufi gida tare dashi,suna isa gidan drever yayi parking a parking space,tare buɗewa Jalal ƙofa ya fito,kai tsaye cikin gidan ya nufa Jafar kuma ya juya zuwa gida domin ya huta,suna shiga suka samu kowa a parlour zama Jalal yayi kusa da Abbou kafin ya zame hular kansa yace "barka da hutawa Abbou" murmushi Abbou yayi cike da jin daɗin ganin yaron nasa ya ƙwantar da hankalinsa yace "Ma sha Allah, Allah abin gdy naji daɗin yadda ka ƙwantar da hankalinka,daman komai mai hucewa ne dukkan baka da hakkinsa kana zaune za kaga sakayya cikin ruwan sanyi,kuma hausawa sunce maƙurci mawadaci wata rana wannan abin sai dai mu bada labari" jinjina kai Jalal kamar zai shuru sai kuma yace "already na manta komai,sai ƙarin ƙarfin guiwa dana samu" cikin jin daɗi Abbou ya shafa kansa yace "naji daɗin hakan lokaci yayi da zaka nunawa jama'a waye kai, lokaci yayi da zaka nunawa duniya ni Alhaji Kabeer nina haifeka, lokaci yyi da zakai faɗa.., faɗa akan abinda kake so ba wa maƙiyanka ba" lumshe ido Jalal yayi yana mai jin sanyi da kuma wata nutsuwa na ratsa jikinsa,tabbas dukkan wanda ya yarda da Allah kuma ya kaiwa Allah kukansa baya taɓewa,an nufesa da sharri sai Allah ya nuna masu ikonsa abinda sukai domin sa cikin ruwan sanyi ya samesa,ya san daka nan zuwa wani lokaci kaɗai buƙatarsa zata biya farin cikin daya daɗe bai samu ba sai ya samesa a lokacin,rayuwa domin daman taƙi ce yadda ka ɗauke ta haka nan zata zo maka,da sauƙi ko akasin hakan,duk yadda kake tunanin abu sai kaga Allah yyi ikonsa abun ko yazo a yadda kasu ko kuma akasin haka,yana riƙon Allah ya ƙara ɗora sa akan dukkanin maƙiyansa, Allah ya bashi ikon aikata dai-dai da barin wanda yake ba dai-dai ba..
Mummy ce tace "Bobo Jalilerh zazzaɓi ya rufeta nayi nayi tasha ko tea ne amma taƙi sai kuka take,ban san yaya ne zan mata ba" kallonta yayi ya ɗauke kai kafin Abbou ya ɗura da faɗin "yawwa idan ka gama ina son ganinka" miƙewa Jalal yayi kafin yace "ina Mameey ne?" Mummy tace tana part ɗinta itama ba taji daɗi ba,kafin yace wani abu Mama ta saka kuka tare da miƙewa tsaye tana faɗin "nikam gidanku zan bar maku ina dalili yaro ya dinga gaba daɗi kamar bani na haifi uwarsa ba,to uba nane kai da zaka dinga haɗe min rai kamar nina sace maka ƴar,banda abinda wanda ya cuci wani ai shida mahaliccin sa,kuma ina tsoran Allah,huuuuu ni mai yarinyar tayi min da zan aikata mata haka,amma duk kunbi kun tsanani ɗan tsiran da yake siyomin ya daina, ahhh niba muna tare da ita a nan parlour muna shira gwanin sha'awa ba sai kawai naji tayi ihuuuu,to kun sanni da tsoran aljanu na tashi da gudu kai ɗaki har ina tuntu ɓe dake ni ba uwace ta haifan ba shi yasa babu wanda ya kula da ciwon da naji ba, ahhh to babu ruwa na ina zan kai hakkin ƴar yarinyar nan"ta ƙare maganar tana face majina.

Kallonta kawai Jalal yayi tare da juyawa ya nufin upstairs,Mama ta ƙara saka wani kukan tace "wlh ya tsanane ba kaga wani kallo da yake min ba,kawai ka ɗauki huƙa ka yanka ni ya fimin sauƙi akan wannan mugun halin naka" Abbou yace "haba keda ba kiyi masa jaje ba tare da addu'a yaya za kice haka" Mama tace "shikenan idan kayi aikin Allah saika faɗa eyeee kabeeru?wlh yini nayi ina sallah ni wata ma ban san me mace ba,amma yaron nan duk bai gani ba burinsa ya hulaƙanta ni,ai shikenan wlh bashi ma da wani lafi kabeeru kai ne mai laifi tunda baka koya masa yadda zai mutun tani ba,yanzu da wannan yaya za'ai yyimin haka" ta faɗa tana nuna Lamir wanda bai ce komai yana zaune yana kallon kowa ido yace "to Mama komai ba hqr ake dashi ba,kuma ai jikanki ne ƙilan irin wasan nan na jika da kaka yake Maki" Mama tace "yooo ni tunda wannan yaron ya sumu ya taɓa zuwa munyi shirar minti goma ne?...,ai sai kai ɗin dama zameka dolanka" Abbou miƙewa yayi tsaye yace "Mama sai hqr kin san yaran yanzu" yana faɗin hakan ya shige part ɗinsa sbd ganin magrib na shirin yi, miƙewa Lamir yyi bayan ya saki wani murmushi yace "Mama nizan huce" Mummy tace "ka gaida gida yaya" sallama yayi masu a hanya suka ci karo da Imran wanda tun safe daya fita sai yanzu..

A hankali Jalal ya buɗe ƙofar bedroom ɗin tare da tura kansa ya shiga, ƙwance ya sameta rufe da duvet sai rawar sanyi take,tana kallonsa ta shagwaɓe fuska tare da sakin kuka,gaban bed ɗin ya ƙarasa tare da zama a gefe ya kalleta yace "tashi zaune" girgiza kanta tayi tana ƙara jan duvet ɗin jikinta,bai ƙara magana ba ya gyara zamansa tare dasa hannu ya zare duvet ɗin da sauri ta rufe idanunta shi kam ko a jikinsa saima ƙara ture duvet ɗin yayi,sai yanzu gane dalilin ƙin tashin nata,daga ita sai three gaiter da half vest mara hannu gaba ɗaya manyan cinyoyinta suna waje,hannu yasa ya miƙar da ita zaune,kallonta yayi yace "meke maki ciwo" kasa bashi amsa tayi sai jikinsa data shige tana sakin wani kukan,ya lura gaba ɗayan ta a haka take shagwaɓaɓɓiya yace ita,komai na kuka ga son jin laushin mutum kamar mage,hannu yasa ya ɗago haɓarta a tare suka lumshe idanu kafin ya sunkuyar da kansa dai-dai fuskarta yace "Jalilerh..."da sauri ta lumshe idanungai sbd yadda sautin muryarsa ya daki dodokan kunanta idan ba zatai ƙarya ba yau ne kawai ta taɓa jin ya ambaci sunanta duk zaman da sukai tare,hannu yasa ya daki kumatun ta, a hankali ta buɗe idanunta tare da turo ƙaramin bakinta gaba..
Chapter 33 · 0% Book details