← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 87

Sashe 71

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Nimcyluv* 08119237616 7/22/21, 8:02 AM - Buhainat: UCL NE _100-101_ Kafin ta ƙarasa inda Jalal yake tsaye ta yanke jiki ta faɗi kanta ya bugo da jikin bango,dake bata hayyacinta yasa ta ƙara zabura ta miƙe tsaye suna nan still a gabanta sun kasa koda ƙwaƙƙwaran mutsi,ganin da gaske downstairs take niyyar yi yasa Abbou faɗin "Muhammad do something,kamar bata hayyacinta"bayanta Jalal yabi lokacin harta kai ga sauka dwonstrais tana ƙoƙarin fiyewa daga cikin gidan,da sauri cikin gudu² ya mara mata baya,tana ƙoƙarin ficewa yay saurin saka ƙafa ya taɗeta tayi baya zata faɗi yaya saurin tareta ta faɗa jikinsa, Murmushi kawai yay lokacin da yaga ta zabura zata ƙwace daga jikinsa, kokawa suka shigayi da ita ganin da gaske tana ƙoƙarin fin karfinsa yasa saka hannu ya ɗagata cak, dai-dai lokacin Abbou ya sakko, Aryan da Irfan suka fito daga part ɗinsu,da sauri su Mameey suka fito,gaba ɗaya suka tsaya a parlour'n suna kallon ikon Allah, Abbou ne yace "Muhammad take her into your room"babu musu yay part ɗinsa da ita zuciyarsa babu daɗi,da ido kawai Aryan yabi Jalal dashi yana haɗiye wani abu mai zafi a maƙoshinsa, Mameey ce tace "Abbou Jalal wai abunne ya dawo ko me?"girgiza kai kawai yay kafin yace "haka muka ganta muma"ya faɗi hakan yana miƙawa twins hannu da gudu suka tawo wajansa sbd daman shi suke kallo, ɗaukan Husainerh yay kana ya riƙe hannun Hassanerh, Mameey tace "Allah ya ƙyauta,amma dai aƙwai matsala yarinya ƙarama su sata gaba"bai ce komai ya nufi upstairs ɗauke dasu Husainerh, Aryan ficewa yay daga gidan,shi kuma Irfan ya nufi upstairs, Mameey ce tace "ina zaka?"yace "Mameey ba wani abu zan ba,baby zan duba"haɗe fuskarta tayi tace "to ba zaka ba"kafin yay magana Anty Sajida tace "huce kaje a binka"juyawa yay cikin sauri ya nufi upstairs, Mameey tace "haba Anty yafa huce shiga part ɗin en matan nan,yanzu ai baki san yaya suke ba,idan suna naked fa?"Murmushi Firdausi tayi tace "Allah ya kiyaye"yana shiga part ɗin ya samu Ikram ita ɗaya zaune saman bed, ganinsa yasa tayi saurin ɗaukan hijab ta saka, Murmushi yay mata kafin yace "meye kike ɓoyewa kuma?"ɓata fuska tai tace "why ka shigo without our permission?" Yace "sbd nasan aƙwai ajjiyeta a nan ɗin,ko ba haka bane?"shiru tai masa ƙara sawa yay wajanta yace "mene ya samu wayarki?na kira but u did pick my call" juyawa idanunta tai tace "ohh ya rabb,wlh tana vibration ne" yace "ok zan kira anjima" tace "to"juyawa yay sai kuma ya kalleta yaga shi take kallo yace "i luv u" kanta a ƙasa tace "luv u too" yace "sure?" Tace "yeah" fita yay tabisa da kallo,yana fita baby ta fito daga bathroom tana sauke numfashi,dry Ikram tai tace "kedai badai tsoro ba"dry itama tayi tace "haba sister aljanu fa?" JALAL na shiga part ɗinsa kai tsaye ya nufi bedroom ɗinsa yana shiga ya sauketa akan bed kana shima ya zauna,bayan ya gama kallonta ya sauke numfashi yace "Jalileeee..rhhh"shiru tai masa tai lamo jikinsa tana zazzare ido, ɗan yatsarsa yasa ya taɓa tsakiyar goshinta, ƙara ta saki tare da fashewa da kuka,cikin wata murya tace "wayyo idona"cije lips yay kafin ya fesar da iska daga bakinsa yace "ido a goshi? weldone mene ya dawo ko?" Ɓata fuska tayi tace "ina ruwanka?" Girgiza kai Jalal yay kafin yace "babu fa,matsala ta ɗaya daku da kuka rasa jikinwa zaku shiga sai nata"dry tai sosai kafin suce "meye haɗin ka da ita?" Shima yay Murmushi yace "niwai?" Sukace "eh fa"zama ya gyara yace "ita ɗin rayuwar Muhammad Jalal Kabeer bobo ce" shiru sukai kafin suce "sonta kake kenan?" Ɓata fuska yay kana yace "yeah? what's your problem?" Girgiza kai Jalilerh tai tamkar ita take magana tace "a'a!baka sonta tunda har zaka iya zuba ido wani ya AURETA bakai ba,bayan kuma kana da iko da ita,ita ɗin mallakinka ce"shiru yay masu bai ce komai,chan kuma yaga ta zabura tace "gida zani ka rabu dani,ka sakeni wajan Ammina zani bana son zama daku na gaji,gida zani" with soo much surprised Jalal yace "alright,zaki gida soon kuma at this week,amma ku fara sakinta" sukace "to kayi mana al'ƙawarin zaka kawota cikin satin nan?" Yace "Nima kuyi min alkawarin kun bar jikinta har abada?" Shiru sukai chan kuma sukace "a ranar daka mai data a ranar zamu rabu da ita" yace "sure?" Suka ce yace "yeah" idanunsa a lumshe yaji tai hamma tare dayin miƙa sai kuma jikinta ya saiki tai luff jikinsa tana sauke numfashi a hankali, gajiyayyun idanunsa ya sauke a kanta lokaci ɗaya yaji wani mugun tausayinta ya kamashi,kasa tashi yay kamar yadda ya kasa janyeta daga jikinsa,yana nan zaune harta farka daga baccin wahalar daya ɗauke ta,hamma tayi tare da buɗe baki ta shiga karanto addu'ar tashi daga bacci,jin laushi ga kuma wani sihirtaccen ƙamshi da yake ratsa cikin hancinta yasa ta ƙara tura fuskarta cikin ƙirjinsa ha tare da tasan ko mene ba, still idanunsa a kanta while hannunsa na cikin sumar kanta Murya can ƙasa yace "Takwaraaaa" ware idanunta tayi tare da juyasu kafin ta ɗaga ƙwayar idanunta a hankali ta sauke ganinta a kan bobo,da sauri ta miƙe daga jikinsa sai kallonsa take,a zuciyarta tana mmkin yadda akai tazo ɗakinsa, bakinta na rawa jikinta ma vibration tace "Uncle"gira ya ɗaga mata kafin yace "meye kikazo yi ɗaki na da har kike min bacci?"kwaɓe fuska tai kamar zatai kuka tace "ayya!wlh nifa ban san yaya akai ba" bai kulata ba ya miƙe tsaye kana ya mai alama data miƙe tsaye,tashi tayi yazo dai-dai kusa da ita, fuskarsa a haɗe ya jawota jikinsa tare da rungome ta, ajjiyar zuciya duka suka saki,kafin ya ɗura bakinsa saman kunanta ya shiga karanta Ayatullah KURSIYO,luff tayi jikinsa tana sauke numfashi tana jin yadda karatun nasa ke ratsa ta,a hankali kuma ya zura hannunsa ta bayanta, ƙara shigewa jikinsa tayi sbd saukar hannunsa da taji a saman fresh skin ɗinta,a hankali kuma yay sama da hannunsa harya sauke a jikin brezia ta data buɗe,kama duka side ɗin yay ya shiga haɗe maɓalllan,jin booms ɗinta sun matse yasa ta fahimci ta brezia a buɗe take,sai lokacin ta tuna tana fitowa daga bathroom bayan ta shirya sai ta manta bata rufe brezia bar,wajan Ikram ta nufi ganin baby ba wani amsa mata take yanzu ba,taje daniyyar a gyara mata daga nan bata ƙara fahimtar komai ba,sai yanzu data farka da ganta da a ɗakinsa, hannunsa ya zame bayan ya gyara mata kana ya cire a jikinsa ya fara kallonta, idanunsa ya ɗauke daga gare ta kafin ya ce "wait a moment" yana faɗin hakan ya fita, a main parlour ya samu Mama da Asabe sai kuma Firdausi da twins,ya na zuwa baby na sakkowa daga upstairs,zama yay idanunsa a kan Mama wacce take ta raba idanu tana jiran taga daga ina Jalilerh zata fito,bayan ya zauna ya ce "ina yininku" Murmushi Firdausi tayi tace "yamai jiki?" Idanunsa akan baby yace "she's fine" kana ya cewa baby "jeki kawo min hijab ɗin ta" tsaye tayi kamar ba taji mene yace ba sai kuma ta juya ta nufi upstairs, Mama tai salati tare da tafa hannu ta ce "kai dai Jalalu ka banu,yanzo kana ganin ƙawar tawa kaƙi gaisheta sbd mugun abu ko me? a'a mugun abu mana,banda haka gaisuwa ta fatar baki ta gagara?nidai wannan muƙamin mugun abu kawai ya ƙara maka da kuma nuƙufarci,wlh nidai babu ruwana dole na faɗa maka gsky"yana jinta baiko kulata ba, idanunsa a rufe har baby ta dawo karɓar hijab ɗin yay tare da miƙewa,gaba yay baby ta bisa a baya,kai tsaye bedroom ɗinsa ya shiga yana tsaye inda ya barta yana zuwa ya zura mata hijab ɗin, kallon yadda take lumshe idanunta da kuma yadda numfashinta yake fita da zafi yasa ya dafa saman kanta da sauri ya cire sbd a zababban zafin da yaji, hannunta ya kama har zuwa parlour a zaune suka samu Nihila itama idanunta a kansu musamman ganin yadda bobo ya riƙe mata hannu, ɗauke idanunta tayi,da sauri Jalilerh ta ƙwace hannunta tana kwallon bobo kamar zatai kuka, gyara tsaiwarsa yay yace "jira nai maki allura" da sauri hadda gudu tai waje jikinta yana tsuma,waje ya nema ya zauna tare da ɗaukan remote ya kunna cenema, ganin baiko kalli inda take ba bare ta saka ran zai kulata yasa ta fashe da kuka tana jin wani irin a ranta,jiyowa yay ya zuba mata idanu shi har ransa mmkin yadda kuka baiwa mata wahala yake,yanzu suke lfy yanzu zaka gansu suna kuka, ɗauke idanunsa yana ci gaba da kallon series ɗin Begusarai wanda zee world suke haskawa lokacin,sai da tayi mai isar ta sannan ta shiru miƙewa tai zata fita muryarsa yana faɗin "Zo nan" tsayawa tai sai kuma ta ƙarasa inda yake zauy,zama tayi a saman kujerar da yake, idanunsa akan kallon yace "mene?" Turo baki tai kafin tace "bakai ka daina kulani ba" taɓe baki yay kafin yace "haba?"sosai mgnarsa ta bata haushi amma ta daure tace "ehmn,gashi yanzu ma ko inda nake baka kalla,ka nunawa Jalilerh ta fini a wajanku, bayan kuma kasan ni zaka au...,"kasa ƙarasawa tai sbd kallon da yake mata, Murmushi yay yace "nasan ni zan aureki right?"kasa bashi amsa tayi,shi kuma ya juyawa gaba ɗaya yana kallonta kafin ya sanya hannunsa ya ɗago haɓarta yace "look at me"kallonsa tai kamar yadda yace shi kuma ya ɗura da faɗin "da ke da ita kuna da bambanci,tunda nake da ita bata taɓa shigowa part ɗina ba tare dana bata izini ba,bata taɓa zama kujerar da nake zaune akai ba, anytime a ƙasan ƙafafuwana take zama,bata taɓa yimin complain a kanki ba,sai gashi ke kinyi yanzu abinda nakeso dake bana son irin wannan shirmen,idan ma kishi kike da ita is better for you ki daina,ita babu komai a ranta tana min kallon wani jigo nata ko damuwa ce da ita idan bani da faɗawa ba zata iya gaya wa kowa ba,dake da ita duk ɗaya kuke a wajena ke jini nace ita kuma rayuwata ce kinga babu bambanci ko?" Tunda ya fara magana dake kallonsa kamar wacce bata gane me yake faɗa ba,kasa cewa komai tayi sai saukar muryrsa da taji yana faɗin "tashi kije" miƙewa tai tare da fashewa da kuka yana jin zuciyarta kamar zata fito,ita dai bata san mene hakan ba,amma
Chapter 71 · 0% Book details