← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 87

Sashe 28

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Tafin hannunsa a saman forehead ɗinta ya fara murzawa tare da ɗan bubbugawa,a hankali kuma yakai bakinsa saitin kunanta ya fara hura mata iska,cikin natsuwa kuma ya fara yi mata karatun yana jin yadda take fizga yaƙi sakinta saima ƙara matseta da yyi a jikinsa, sama da 30minutes yana abu ɗaya amma ko tari taƙiyi balle ya saka ran zatai magana,hannunsa dake saman goshinta ya ƙara murzawa tare da dukan goshinta wata ƴar ƙara sukai kana tayi atishawa,lufff tayi a saman ƙirjinsa tana sauke numfashi, shuru yyi shima yana jin yadda jikinta ya ɗauki zafi,tambayar da yake wa kansa dama tana dasu ne,ko kuma yanzu ta samu,idan yanzu ta samu a ina?wanan shi ne tarin tambayoyin da suke zcyarsa amma babu wanda zai tambaya.

Ajjiyar zcy Aryan ya sauke yace "Abbou tunda kaji nace ina sonta ai aurenta nake da niya,wlh ban taɓa ganin macen da tayimin irinta ba, tun lokacin da yaya yazo da ita na fara sonta, Abbou idan kaƙi bani ita wazan nema ya ban ita,kace naje wajan bobo kana ganin ko kulani bai yi ba bare na saka ran zan samu abinda nake so a wajansa" Abbou ne yace "shikenan kaje ka samu soyyarta tukunna" sai lokacin Mummy tace "kada ka damu son zanwa bobo mgn,nasan bazai ƙi ba" miƙewa yyi tare da yin waje yabar gidan gaba ɗaya.

"Amma ya dace a sama mata magani domin naga da ƙarfi suka kamata" Mameey ta faɗa cikin tausaya wa, Lamir ne ya ƙarasa cin abincin dake bakinsa yace "ahhh to ai nayi mgnar hakan babu wanda ya tanka" Mummy tace "ba haka bane yaya, lokacin hankalinmu ne gaba ɗaya baya jikinmu" da sauri Lamir yyi baya tare faɗin suwaye a bayan sofa kuma?" Kafin ai magana Mama fito tana rarraba idanu, kallonta Mameey tayi tace "Mama mene a jikinki kamar ruwa?" Daga bakin ƙofa akace "mene kowa banda fitsari" Abbou ne yace "gidanku Irfan Mama kake gayawa haka" ita dai Mama babu wanda ta kula tayi part ɗinta ruwan fitsari na bin jikinta,daman Nihila tunda aka ɗauke Jalilerh daka wajan tayi nata part ɗin da gudu.

Da sauri Jalilerh ta ƙwace jikinta daga na Jalal wanda bacci ya fara ɗauke sa, miƙewa shima tare dasa hannu ya kamota ganin kamar bata cikin nutsuwarta cikin wata murya tace "Uncle ka fita dani,banson gidan nan, Uncle zasu kamani ga sunan wlh,wayyo Uncle zasu kasheni"saurin rungome ta yyi a jikinta yana bubbuga bayanta tare shafa sumar kanta,
Ƙanƙamesa tayi tare da ƙara faɗin "Uncle ka gudu dani zasu kamani ina tsoransu Please Uncle" bakinsa ya sanya cikin nata sbd bai ƙaunar jin abinda take faɗa,gaba ɗaya idanunsa ya sauya kala zuwa jaaa,jijiyar kansa ta mimmiƙe,a hankali shima jikinsa ya ɗauki rawa sbd sarawar da kansa yyi masa, ƙara rungome ta yyi sbd jin yadda jikinta ya ɗauki rawa gaba ɗaya,bakinsa ya cire daga nata tare dasa hannunsa ya ɗauke ta cak yyi cikin bedroom da ita,yana zuwa ya ƙwantar da ita,shima ya ƙwanta remote ya ɗauka ya ƙaro gudun a.c,gaba ɗaya a tsorace take hakan yasa ta shige cikin jikinsa tana sauke numfashi, lumshe idanu yyi a dai-dai kunanta yace "sleep, nothing happen am with you, Uncle ɗinki na tare dake" ya faɗa yana bata peak a goshinta,kanta ta ɗura saman ƙirjinsa ta ƙanƙamesa,shima rungome ta yayi babu jimawa bacci yayi gaba dasu a tare.

Washegari tun da safe ya fita sbd a ranar za'a gabatar da zaɓen primary election wato zaɓan cikin gida,wanda yake neman ƴan majalissu su mara masa baya kuma yaji Sa'a a kaso 10 7 zuwa 8 suna bayansa, parking Lamir yyi a compound na gidan yana gama parking ya fito daga cikin motar ya nufi parlour, Mama ya samu sai Jalilerh kallonsu yayi yace "Mama ya naji gidan shuru?" Taɓe baki tayi tace "Salamutu da Jamal sunje kasuwa,Nibala ko niwad ohuuu mata,ta leƙa nan maƙota daga Ni sai wannan mai aljanun" ta faɗa tana nuna masa Jalilerh, murmushi yyi yace "daman nazo ɗauka ta ne zuwa wajan malam"washe baki Mama tayi tace "yawwa irin albarka maza kuje a cire su,nake gaya maka ƙwana nake babu bacci sbd far gaba" ledar hannunsa ya miƙa wa Mama yace "banson mutum gidan susan nine nai mata magani,dan haka kada ki gayawa kowa nazo na tafi da ita,idan zan dawo zan ƙaro maki wani naman" cikin farin ciki Mama ta yagi cinyar kazar takai bakinta tace "jeka abinka daman wake faɗar aikin lada, nina san me zance" murmushi yyi yace "my dear zo muje ita dai Jalilerh kallonsu kawai take dan bata da ikon cewa ba zata bane,kwaɓe fuska tayi tace "Mama ban sanshi ba ai" tsaki Mama taja tace "kamar yadda buba bazai cutar dake ba shima haka,to na taƙaice maki zance ni nayi naƙudarsa na shayar dashi da wannan nonon dake jikina,maza tashi kuje keda za'a taimaka ina ke ina iya yi" jiki na rawa Jalilerh ta miƙe hannunta ya kama yace "muje beauty" har mota ya sata sannan yaja motar ya fice da sauri, Jalal na can amma san hankalinsa yaƙi ɗaya haka nan ya samu kansa da tunanin gida,ganin ba'a fara zaɓan ba ya ɗauki ƙaramar wayarsa wacce amsa kira masu muhimmanci yyi dailing number Abbou, Abbou yana tsaka da driving yaji wayarsa na ƙara ɗauka yyi tare faɗin "fatan lfy dai bobo?" Daga can Jalal ya saki ajjiyar zcy yace "Abbou kada a bar yarinyar nan ta fita koda ita da wani ne" murmushi Abbou yayi yace "yanzu dai na kusa gida,in sha Allah hakan bazai faro ba, Allah ya taimaka" Jalal najin hakan ya kashe wayar yaci gaba da sauran abinda wasu ƴa Majalissu suke faɗa masa.
Lamir na fita Abbou na shigowa Mama ce zaune a parlour ta tisa ƙatuwar kaza tana ci, kallonta yayi yace "mutan gidan basu dawo bane" taɓe baki tayi tace "sa dawo tunda sunbar baiwa a gida"kallon ta yayi yace "Jalilerh fa" tace "tana can tayi bacci yanzu tabar nan ai" jinjina kai yyi yace "bari na dubata" da sauri Mama ta miƙe tsaye tare faɗin"ohhhh ƙarya zan maka kenan ko Kabeeru?" Yace "a'a ba haka nake nufi ba kiyi hqr"yana faɗin hakan ya shige part ɗinsa.
6/10/21, 1:11 PM - Buhainat: Yana driving yana murmushi jifa-jifa kafin a hankali ya juya kan motar zuwa wani waje na daban,a gaban wani kango yyi parking tare da kashe motar ya fito,tana zaune cikin motar idanunta a kansa ga hawayen da yyi ƙwance a cikin idanunta,murfin side ɗinta ya buɗe t fuska babu yabo babu fallasa ya kama hannunta zuwa cikin kangon,yana shiga tayi saurin yin bayansa sbd mutanan data gani wajan mutum goma,daga can ɓangaren aka fara tafi kafin Hon Faisal Lawan ya fito daga cikin wani ƙaramin ɗaki hannunsa riƙe da wata Camera yace "aiki da kai huce takaici,kayi ƙoƙari kayi komai cikin sauƙin"
Chapter 28 · 0% Book details