Sashe 50
Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
ne ya sauka akan Jalilerh wacce yaga tai masa ƙyau sosai,ta saka light blue ɗin lace mai Maroon touchs sai siririn mayafinta shima Maroon da kuma flat shoe shima Maroon,hannunta riƙe da hisilin muslum,babu komai fuskarta sai lipstick tayi fresh kamar amarya,sai ya kasance ita dashi kamar sunyi anko,kallo guda yaywa ahalin nasa yaji wani farin ciki ya rufe sa gefe guda kuma na zcyarsa yana buga tare da faɗuwar gaba,haka dai ya wanzu yana azkar a ransa, Abbou ne yace "muje lokaci naja"Mummy tace "Mama mun tafi" kallon Mummy Mama tayi tace "to Allah ya kiyaye" gaba ɗaya suka fita Mummy still tana cikin parlour'n kamar wacce tayi mantuwar wani abun, Jalal ne ya dawo baya yaja hannunta yana amsa addu'ar da Mama keyi masa,Babbar motarsa Jalal ya shiga,ya zauna mazaunin drever, Jalilerh na gefensa baya kuma Mummy ce, ɗaya motar kuma Mameey ce a gaba Abbou mazaunin drever sai Nihila a baya,sai kuma motocin securities wajan guda uku suna mara masu baya,a haka suka fice daga cikin gidan Baba habu nayi masu fatan nasara. A haka suka ƙarasa mazaɓarsu, kasancewar duk a mazaɓa guda za suyi zaɓen,nan waje ya hargitse kowa yana murna yaga Jalal bobo,da ƙyar securities ɗinsa suka nema masu waje saida kowa yay zaɓen sanna yayi, Nihila na zuwa aka rufeta mutane suna karɓar rabonsu haka dai ta dinga raba masu kuɗin jakarta,wani ne ya hangi Jalilerh yace "laaa ga matarsa can ai kuzo muje wajanta"tana tsaye sai raba idanu take domin bata saba ganin haka ba taji ance "Hajia muna maku fatan nasara Allah ya taimaki mijinki in sha Allah saiya haye" rasa gane maganarsu tayi,sai tunanin waye mijinta take kafin tai magana yaja hannunta zuwa cikin mota yace "baki iya amsa addu'a bane?" Turo baki tayi bata ce komai ba,a haka suka shiga mota suka nufi hanyar gida,cikin nutsuwa yake driving yana kallon Mummy ta madubin motar data zabga tagumi,ana haka wayarsa ta fara ƙara ganin sunan Jafar na yawo yasa ya danna picking kana yace "uhm" Jafar daga can ɓangaren ya share zufar data karyo masa yace "kana ina yanzu haka?" Da rashin fahimta Jalal yace "hanya" Jafar ya ƙara kallon jama'ar gabansa na wajan zaɓe yace "maza kuyi gida,sannan ku baza securities a layin"Jalal na ƙara giyar motar yace "lafiya?" Jafar kamar zai kuka yace "Jalal bazan iya faɗa maka da bakina ba,amma ka kunna redio nima ina wajan zaɓe ake sanar dani wannan tashin hankalin" Jalal baice komai ya katse kiran kai tsaye ya kunna redio'n dake motar lokacin 12:30 an fara labarai,yana kaiwa yaji ana faɗin _Kudin labaran kenan yanzu zaku saurari cigaban labaran..,A yanzu ne muka samu cikakken labari daga bakin wani mutum wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa,inda yake faɗin, Munata murna zamu samu shugaba adali kuma mai asali,ashe shima tumun dare ne domin bincike ya tabbatar mana uban Governor Muhammad Jalal Kabeer bobo bashi da asali kawai yayi dirar mikiya a garin namu na Ibadan,abu mara daɗi an ƙara tabbatar mana shi kansa Muhammad Jalal Kabeer bobo ba'a san inda mahaifiyar sa take ba,a taƙaice ma ance mahaukaciya ce ta haifesa..._ Bai ƙarasa jin labaran ba ya kashe redio'n lokacin guda kuma jikinsa ya fara rawa a zafafe ya juya ya kalli Mummy wacce take baya,a zaune ya ganta idanunta sun firfito waje gumi sai yanko mata yake,kana ya juya ya kalli madubin motarsa nan ya hangi motar Abbou tana biye da tasa, Jalal ƙasa magana yay gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya brain ɗin sa ta daina aiki,a hankali kuma lakar jikinsa ta zare ya fara ganin duhu a cikin idanunsa,yadda tunaninsa ya tsaya haka hannunsa ya zare daga kan motar,motar tafiya kawai take Jalilerh tsoro da firgici ya hanata koda mutsawa musamman da taga kan motar yana sauka daga tsari,ganin inda motar tayi tasa ta fasa uwar ƙara tare dayin jikin Jalal wanda ya kifa kasa ƙasa a kuma dai-dai nan motar ta daki jakin baban gida cikin rashin Sa'a motar ta tuntsira tare da mirgina wa sau biyu a tsakiyar titi......