← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 87

Sashe 47

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

B) Ya tabbatar wannan danshin ba maniyyi ba ne, to wanka bai wajaba a kanshi ba, hukuncinsa hukuncin fitsari ne, sai ya wanke)

C) Ya yi shakka, maniyyi ne ko ba shi ba ne? To a nan wajibi ne a kanshi ya yi kirdado, idan ya tuna abin da zai nuna masa cewa wannan danshin maniyyi ne, to ya bar shi a kan maniyyi ne. in kuma ya tuna abin da zai nuna masa cewa maziyyi ne, to maziyyin ne, in kuma ya kasa tuna komai, to sai ya yi wanka don fita daga savani da ruxu.

7- Idan ya ga maniyyi, amma bai tuna yaushe ya yi mafarkinsa ba, to wanka ya wajaba a kanshi, ya kuma sake dukkan sallar da ya yi bayan tashinsa daga barcinsa na qarshe.

2- Saduwa (Jima’i)
Shi ne haɗuwar gaban namiji da na mace, wato shigar kan gaban namiji zaya sanya cikin farjin mace, ko da kuwa bai zubar da maniyyi ba, saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم )“Idan kaciyar (namiji) ta shige kaciyar (Mace) to wanka ya wajaba� [Tirmizi ne ya rawaito shi].

3- Musuluntar Kafiri
Saboda “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya umarci Qaisu ɗan Asim ya yi wanka lokacin da ya musulunta� [Abu Dawud ne ya rawaito shi]

4- É—ukewar Jinin Haila Da Na Biqi
Saboda hadisin Aisha cewa Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya cewa Faɗimatu ‘yar Abi Hubaish “Idan al’adarki ta zo, ki bar sallah, idan ya wuce ki yi wanka ki yi sallah� [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Hukuncin jinin biqi kamar hukuncin jinin haila ne da ijma’in malamai.

5- Mutuwa
Saboda faɗin Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) a hadisin wanke ‘yarsa Zainab lokacin da ta rasu ya ce,“Ku wanketa sau uku, ko sau biyar, ko fiye da haka, in kun ga akwai buqatar hakan� [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

Yadda Ake Yin Wanka
Abin da yake wajibi a wajen wanka shi ne gama jiki gaba É—ayansa da ruwa, tare da yin niyya, koma yaya ya yi shi.

Sai dai abin da aka fi so ya yi koyi da siffar wankan Annabi ( صلى الله عليه وسلم ), kamar yadda uwar muminai Maimunatu ta siffanta shi, ta ce, “Manzon Allah ( صلى الله عليه وسلم ) ya sanya ruwa don yin wankan janaba, sai ya karkato abin ruwan da hannun damansa a kan hagunsa ya wanke hannayensa sau biyu ko sau uku, sannan ya wanke gabansa, sai ya doki qasa ko bango da hannunsa sau biyu ko sau uku, sannan sai ya yi kurkurar baki ya shaqa ruwa, ya wanke fuskarsa da sangalin hannunsa, sannan ya kwara ruwa a kansa, sai ya wanke jikinsa, sannan ya matsa gefe guda ya wanke qafafunsa. Nana Maimunatu ta ce, “Sai na kawo masa wani qyalle (hankici) amma bai karɓa ba, sai ya riqa share ruwan da hannunsa� [Bukhari ne ya rawaito shi].

- Yadda ake wankan a taqaice shi ne :

1- Zai wanke tafukan hannayensa sau biyu ko sau uku.

2- Zai wanke gabansa

3- zai doki qasa ko bango da hannu sau biyu ko sau uku.

4- Sai ya yi alwala irin ta sallah, ba tare da shafar kai da kunne ba.

5- Zai kwara ruwa a kansa

6- Zai wanke jikinsa gaba xaya.

7- Zai koma gefe ya wanke qafafunsa.

Bayan ya kammala ya sauke wata wahalalliyar ajjiyar zcya tare da jan numfashi yace "kinji wanan" shuru yaji sai kuma yaji saukar numfashinta mai zafi a saman ƙirjinsa, leƙawa yay yaga tuni bacci ya ɗauke ta,waro idanunsa yay da mamaki yana addu'ar Allah yasa dai duk taji me yace bai wahalar banza ba, miƙewa yay da ita a jikinsa tare da ficewa daga ɗakin,kai tsaye parlour ya nufa,a zaune ya samu Mama tana cin soyayyan nama da kuma lemo,kallo guda yay mata,ita kam baki ta saki tare da rafka salati tace "me zan gani yau?wai ɓatan nono a ƙirjin budurwa,zabgegiyar budurwa ka ɗauka kamar yarinyar goye,maza maza sauketa na gani"haɗe rai yay kafin yace mata "hannunki ne?" Cikin ƙufula tace "to sallamamme yimin rashin kunya,da matarka ka ɗauka ma da sauƙi" waro idanunsa yayi waje kafin yace "ok bari na ajjiye ta na ɗauke ki" zama tayi saman kujera tare da fasa kuka tace "wlh ba hali na ka ɗauka ba sai dai na dangin ubanka,amma tirrrr da mummunan hali irin wannan yanzu ni zaka ɗauka Jalalu?" Mummy dake saman upstairs ta danne dryar dake cinta kafin tace "Bobo maza jeka ƙwantar da ita kazo ka shige ka bamu waje" baice komai ba ya haura upstairs ɗin,yana zuwa ya nufi part ɗin su,babu wani haske ɗakin sai wani light blue bed ɗin ta ya nufa ya ƙwantar da ita,kana ya zare nata hijab tare da gyara mata kwanciyar, jikinsa yazo zamewa tayi sauri riƙesa tare da turo baki gaba,kai kawai ya girgiza ya ɗauki ƙaramin pillow ya saka mata da sauri ta rungome pillow,sosai yay mamaki yadda tasan daɗin jiki gashi shi duk lokacin da suka ɓata babu abinda yaji a kanta,tsaki yaja kana ya tofa mata addu'a ya rufeta da duvet,wajan Nihila ya ƙarasa tana jin zuwansa tayi saurin rufe idanunta,ba tare da wani tunani ba,itama yay mata addu'a kana ya bata light kiss a saman goshinta ya gyara mata kwanciya, remote ya ɗauka ya ƙaro masu gudun a.c kafin yaja Ƙofar ya rufe,da idanu ta bisa harya fice daga ɗakin kafin ta juya ta kalli Jalilerh wacce take bacci cikin nutsuwa ta rungume pillow,rufe idanunta tayi a haka bacci itama ya ɗauke ta ta.
Chapter 47 · 0% Book details