Sashe 62
Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
yace "Allahamdulillah"zata Æ™ara magana Mameey tace "leave" komawa tayi da tray É—in lemon tana tafe tana juyawa,bayan yasha ruwan da Mameey ta bashi ya miÆ™e tsaye zai fita Mameey tace "koma ka zauna i want talk to you Muhammad" zama yay yana É—ura idanunsa akan Mameey,itama kallonsa tayi tace "mene ra'ayinka akan baby?" With much surprise ya dinga kallonta kafin ta É—ura da faÉ—in "nasan baka da niyyar aure yanzu,amma yanayin da kake jiki auren shine mafita,kuma kasan idanun jama'a akan ka suke dole ne ka ajjiye iyali ka fara mulkarsu kafin ka mulki jama'ar gari,ban san yaya matsayin baby yake a ranka ba,kana sonta da aure ko akasin haka? duk yadda yake a ranka inma kallon sister kake mata ko baka da feelings a kanta,ya zama dole ka dinga sanya sonta da son kasancewa da ita a cikin zcyarka,nasan bata da wata damuwa komai aka zartai zata amsa,amma ga namiji auren macen da bai so matsala ne,duk da cewa ina da tabbacin ba zaka taÉ“a yin wani abu da zai cuci Nihila ba,amma rayuwar aure da kuma zamantakewarsa daban yake,dole yadda kuke ada ba haka zaku kasance ba,anawa tunanin ya kamata ka fara jin ta bakinta ma'ana ka fara keÉ“ewa da ita"ware idanunsa wanda suke a rufe yay kafin ya cije lips É—insa yace "what about Jafar?" Shiru Mameey itama tayi kafin ta miÆ™e tace "don't worry about him, Abbou Jalal zai masa magana ok" tana faÉ—in hakan ta miÆ™e tsaye tare da É—aukan tray É—in tai gaba da kallo kawai ya bita,kafin ya sauke wasu tagwayen ajjiyar zuciya. Bayan sallar issha'i Jafar yay parking da motarsa kana ya nufi cikin gida,a main parlour ya samu Mameey sai kuma Mama zama yay kansa a Æ™asa ya gaishesu kana ya Æ™ara yi masu ta'aziyya,satar kallon Nihila yay sai kuma ya É—auke kansa, miÆ™ewa Mameey tayi tace "bari nasa Laure ta kawo maka ruwa"bai ce komai ba sai Murmushi da yayi, Nihila ce tace "Yaya Jafar ina yini?" Murmushi yay wanda yake nuna zallar jin daÉ—i yace "bana amsawa" idanunta ta É—auke daga kan littafin da take dubawa tace "why?" Shima ya kwaikwayi muryarta yace "why?" Salati yaji an zabga da sauri ya juya sbd a tunaninsa tuni Mama tabar parlour'n tsaye ya ganta tana tafa hannu tace "huuuu³ yaushe ka zama sallamamme bani da labari,a'a Wlh wannan halin banza ne,ina ruwanka dayin Muryar mace? Banda neman magana, yuuuu ko daudo zaka koma ne bana da labari Jafaru? a'a wlh wannan gantalewa ce yaya ina ya bonka sallah zaka kasa alwala?" Æata fuska yay yace "to ina ruwanki ne?" HaÉ“a ta riÆ™e tace "Mahadurrasulillah zagina zakai? Daga faÉ—in gsky sai cin mutunci ya biyo baya? To Allah ya baka hqr tunda ka zama gantalalle" shi dai baice komai ba harta gama surutanta tai gaba,tana barin parlour'n ya koma kusa da Nihila yace "me kike ne?" Idanunta akan littafi tace "study" jinjina kai yay yace "ok you can continue my wife to be soon in sha Allah" É—ago kai tayi ta kallesa suka haÉ—a ido kasa É—auke idanunta tayi sbd gabanta daya faÉ—i taba rasa mene za tace masa,tarin da sukaji yasa gaba É—aya suka dawo cikin nutsuwarsu,bobo ya fito daga shi sai 3gauter da farar singlet kai tsaye kitchen ya nufa ko inda suke bai kalla ba, duk da cewa shida Jalal abokai ne amma hakan bai hana yaji wata kunyarsa ta kama sa ba,dalilin haka yasa ya miÆ™e da sauri ya É—auki key É—in motarsa yace da Nihila "goodnight wify,luv u Soo much" yana faÉ—in hakan ya fice daga cikin gidan ya nufi waje,bobo na shiga kitchen yaga da aÆ™wai ruwan zafi a flast tea ya haÉ—a a mug ya zuba milk da bonvita da obalti,sai suger guda uku, spoon yasa ya juya tea É—in, yana kitchen É—in zaune saman stool kasan cewar ta kashe wutar kitchen É—in yasa ba kowa zai san yana ciki ba, tun daga bakin Æ™ofa ya hango ta tana tafiya a hankali kamar wacce Æ™wai ya fashewa a ciki,tana tafe hannunta a mararta wacce tun safe take mata ciwo, idanu ta fara rarraba wa sbd duhun data gani a kitchen É—in, Æ™arasa shiga ciki tayi ta nufi inda makunnin Æ™wan yake,tsayawa tai cak a tsakiyar kitchen É—in sbd wani murÉ—awa da marta tai har sai da ta saki Æ™ara ta durÆ™oshe a wajan ta fara kuka,sbd Allah yana gani ciwon ya fara cin Æ™arfinta,ga wani amai dake taso mata haÉ—e da ciwon kai zazzaÉ“i duk lokaci guda,duk abinda take a kan idanunsa yana zaune yana shan tea hankali Æ™wance time to time yana lumshe idanunsa,amma idanunsa ko mutsawa basayi a kanta, lokaci É—aya kuma ya fahimci abinda ke damunta,ganin bata da niyyar miÆ™ewa ga kukan dake cin Æ™arfinta,yasa ya sakko daga saman stool tare da ajjiye cup É—in wajan sink,kai tsaye wajanta ya nufa yana tafe a hankali sbd bai son taka wani abu ko taka hannunta sbd ba sosai yake ganin komai na kitchen É—in ba,a haka harya Æ™arasa zuwa inda take,fesar da numfashi yay tare da sunkuyawa yasa duk hannayensa biyun ya É—agota sosai ta tsorata zata saki ihu yay saurin saka hannu ya toshe mata baki, tura ta ya dingayi har zuwa jikin bango kafin ya haÉ—ata da jikin bangon ya É—an ranÆ™wafo dai-dai fuskarta yana leÆ™awa, bakinta kawai yake iya gani suma dalilin jan da sukai ga kuma hawaye da yawon da suka jiÆ™asa,ita dai Jalilerh sai leÆ™a fuskarsa take amma ta kasa ganin ko waye sbd duhu ga kuma wani a zaÉ“aɓɓen ciwo dake cinta hakan yasa ta Æ™ara sakin wani kukan tana zabewa zata faÉ—i yay saurin haÉ—ata da jikinsa a tare suka sauke ajjiyar zcya mai Æ™arfi,da sauri Nihila wacce take bakin kitchen É—in ta juya idanunta cike da hawaye,shiru gaba É—aya sukai sai Jalilerh dake sauke ajjiyar zcy,a hankali kuma ya dinga bubbuga bayanta yana shafa Æ™wantaccen gashin kanta,a hankali kuma ta dingani ciwon na sauka sai wani gumi daya dinga sakko mata, idanunsa ya sauke a red lips É—insa kafin a hankali kuma ya Æ™arasa kusanta bakinsa da nata ya É—an lumshe idanunsa cikin É—aukewar numfashi ya sauke lips É—insa saman nata kafin ya bata wani special hurt kiss a gefen lips É—inta,kana ya juya da sauri yabar kitchen É—in,yana fita ya samu Aryan a parlour ko kallansa bai ba ya Æ™arasa shigewa part É—inta, Aryan kuma kitchen É—in ya shiga yana shiga yaji bugi abu da sauri kuma yasa hannu ya kunna hasken kitchen É—in,tsaye ya ganta kanta a Æ™asa, Æ™arasawa yay inda take tsayen tare da leÆ™a fuskarta ganin hawaye Æ™wance saman fuskarta yasa shi faÉ—in "Hubby...!!"saurin É—ago kai tayi yayinda zcyarta ta buga da Æ™arfi,zallar tsoro ya bai yana a Zcyarta tunaninta shine badai Aryan shine ya rungome ta ba?to idan ba shi bane waye? Tabbas shine tunda gashi taji muryarsa kuma shi ta gani tsaye,to mene yake cikin kitchen É—in?ganin tai shiru tana kallonsa yasa yace "what wrong?" Nan ma shiru tai masa hannu ya miÆ™a zai riÆ™e ta tayi sauri matsawa baya tana girgiza kanta,kallon fararan kayan baccin dake jikinta yay sai kuma ya É—auke kai tace "You are Staired" da sauri ta kalli jikin ta sai kuma tai waje da gudu bayanta yabi da kallo yana sauke É“oyayyiyar ajjiyar zuciya. washegari kamar yadda aka buÆ™ata Jalal ya shirya cikin wata jumper mai shegen Æ™yau maroon color ya saka babbar rigar,sai Black hula da black covert shoe,hannunsa ya É—aura agogon gucci ga farin bluetooth daya saka,da sauri ya Æ™arasa fesa parfume É—in hannunsa,kana ya É—auki wayoyinsa ya riÆ™e,fita yay yana fita ya zamu Mameey ita É—aya a main parlour kowa ya tafi wajan aiki dake Monday ce, Nihila kuma na makaranta Jalilerh na É—aki tana bacci sbd bata jin daÉ—i, Abbou yana wajan masu karÉ“ar gaisuwar da suka zo masa,kallon Mameey yay yace "Mameey I'm going,a gyaran part É—ina before I'm coming back" murmushin jin daÉ—i tayi ganin yay fesa kamar ango sai zabga Æ™amshi yake,ga wata cikar zati haiba kwarjini daya Æ™ara fitowa saman fuskarsa,tace "in sha Allah, Allah ya tsare ya kiyaye" da Ameen ya amsa kana yay waje,yana fita securities suka rufa masa baya,wata lafiyayyiyar mota aka buÉ—e masa back seat ya zauna kana driver ya shiga,su kuma su shiga taso motar guda biyu,suka saka motar Jalal a tsakiya a hankali motocin suka fara barin gidan,da yammacin ranar Mubarak Yahya cibo ne zaune a gaban boka SaÆ™ib yana sauraran abinda yake faÉ—a,boka SaÆ™ib yaci gaba da faÉ—in "kayi kuskure domin abinda mukace ka aikata bashi kai ba,dole ne ka samu matsala akan zaÉ“en ka,dole ne kujerar tai rawa,kaci Sa'a kazo da wuri banda haka da bazan iya komai akai ba"da sauri Mubarak Yahya cibo yace "Ni dai burina kawai bai huce na Jalal a Æ™asa ba, farin ciki na shi ne dukkan abinda ya sawa hannu a harkar mulkinsa ace ya lalace abun bai albarka ba,ai tasa masa É“arnar kuÉ—i,idan har zai yiwu ma kawai a sa ya zama Mazinaci..