Sashe 25
Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A ƙwance suka sameta ƙasan carpet kumfa na fita ta cikin bakinta kamar mai dafara,da sauri Aryan ya ƙarasa inda take ƙwance babu numfashin kafin yayi wani yunƙuri Jalal ya sanya duka hannunsa ya ɗauketa cak zuwa jikinsa,ba tare daya kalli kowa ba, ya nufi wani part yana shiga ya buɗe ɗan ma dai-dai cin room ɗin wanda yake tamkar chemist,wani ƙaramin bed na marasa lfy ya ƙwantar da ita,yana gamawa ya nufi waje a baƙin room ɗin ya samu duk ƴan gidan, fuska ya haɗe yace "me kuke a nan to?" kafin kowa yyi magana Aryan yace "yaya kalli fa ko numfashi ba tayi,dan Allah bari na shiga naganta Please" banza yyi masa yyi huce zuwa part ɗinsa wata box ya ɗauka ya koma part ɗin lokacin sun koma parlour ya rage Nihila ce da Aryan wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa kamar mai nazarin wani abun,babu wanda ya kula cikinsu,ya shige cikin room ɗin tare da rufe ƙofar,yana zuwa ya sameta kamar yadda ya ƙwantar da ita, zuwa yyi ya zauna bakin bed ɗin tare da ɗaukan hannunta yana dubawa,bayan ya duba ya miƙe ya fara duba inda zaiga allurar suma, kafin ya ɗauka yaji ta kira sunan da ƙarfi da sauri ya juya ya sameta tsaye tana kokawar kama wani abu ƙarasawa yyi kusanta,a hankali ya sanya hannunsa a saman waist ɗinta ya riƙe ta ƙam a jikin jikinsa,still ba ta daina abinda take ba,da kƴar ya ɗauketa ya nufi inda bed ɗin yake,zama yyi da ita a jikinsa kafin yasa hannu ya tallafo haɓarta, ɗan waro idanu yyi waje kafin ya saka hannu ya ranƙwashi kanta yace "eyee kune ashe" cikin ƙasa da murya yace "Jalery" ƙasa ɗaga idanu tayi ta kallesa,kuma bata bar kokawar da take ba,sai wani ihu take ƙasa-ƙasa gaba ɗaya ta yaƙoshe masa ƙirjinsa sbd singlet daya saka, ƙara jawota jikinsa yyi ya matse ta a hankali kuma ya saka tafin hannunsa ya a saman goshinta ya fara murzawa, ƙasa ya ƙarayi da bakinsa dai-dai saitin kunanta yyi bisimillah kana ya fara karanta Ayatul-qursiyyo tun tana bige-bigen har jikinta yyi laƙwasar ta fara sauke masa numfashinta a ƙirjinsa,hura mata iskar bakinsa yyi kafin yace "Jalilerh" wannan shine karan farko daya taɓa kiran sunanta,can yaji tace "ba ita bace" waro idanu yyi waje alamar mmki,kafin ya shafa sumar kanta yace "ashe? koma waye ita nake nema ba wani ba" ƙara shigewa jikinsa tayi tace "meye haɗin ka da ita? ka daina wasa da jinnu ɗan yaro" lumshe idanu yyi yace "canta matse maku, maganar meye haɗina da ita ku uban mene haɗinku da ita" ya ƙare maganar yana dungure mata kai" ihu tayi tace "wayyo ka tsokanan idona ka rabu damu muyi aikinmu,ka fita sabgar da babu ruwanka" gyara zama yyi yace "gaba ma idon zan cire,dalla ware nina gaji da ganinka,banza mara tsoran Allah" itama cewa tayi "idan kaga muntafi to mun kammala aikinmu,sannan bamu shiga jikinta danmu cutar da ita ba, muma aikomu akai" ƙara ware manyan idanunsa yyi waje cikin gajiyawa yace "to baku da wajan zama jikinta,domin ita ɗin rayuwa tace,duk wanda ya turoko kuce ni Muhammad Jalal bobo nafi ƙarfin sa" dry tayi tace "koda mun tabi wasu zasu dawo domin baza mu taɓa barinta ba" murya ya gyara ya fara karatu cikin nutsuwa yana tofa mata a kunne,ihu ta kurma har saida ya saka hannu ya toshe mata baki,cikin wata murya tace "to wai kai na taɓa ganin musulmi ya zauna da arne ne?" cije lips yyi yace "to ai yanzu kaga alama ko? to maza jeka kafin na sauya maka ka manni" kaita ɗago a hankali ta kallesa sai kuma ta kwaɓe fuska tace "me mukai maka, shikenan zamu tafi amma ka shirya dawowarmu a ko wanne lokaci" tana faɗin hakan tayi atishawa sau uku sai kuma tayi ƙwance jikinsa luff tana sauke numfashi, ƙara shigar da ita jikinsa yyi sbd zafin da jikinta ya ɗauka,a hankali yaci gaba da shafa sumar kanta yana ƙara tofa mata addu'a.
Uwa sundu ce ke tsaye hannunta sai fidda wani irin haske yake,ta ɗauki wajan 5minutes kafin hasken ya ɗauke,tana a tsaye jushoa ya shigo yana zuwa ya baje gabanta tare da ɗaga hannunsa sama,kansa ta shafa tare da zana masa wani jan abu, dry tayi tace masa "komai yyi dai-dai daga yanzu zuwa ko wanne lokaci zata dawo zuwa birnin nufar,sai dai aƙwai babban lamari wanda nima na kasa ganesa,mun tura mata mutananmu sun zauna a jikinta domin su shiga cikin tunaninta" ƙara zubewa Joshua yyi yana ƙara ɗaga hannunsa sama yana yiwa uwa sundu jinjina" wata ƙarar rawace tayi ƙara alamar an amshi riƙonsa.
Abbou ne zaune a main parlour suna tattaunawa akan zaɓen cikin gida daya rage ƙwana biyu a gudanar dashi, Jalal ne yace "eh Abbou an gama komai kawai lokaci ake jira" Aryan ne ya kalli Abbou yace "Abbou wani taimako na keso wajanka ban sani ba ko zakamin? kallonsa kawai Jalal yyi Abbou kuma yace "haba ƴan uku mai zai hana indai ina da iko a kansa" Aryan yace "Abbou ina son Jalilerh aurenta nake sonyi" gaba ɗaya mutanan ɗakin suka ɗago kansa suna kallansa,banda Jalal wanda yake kallon b.b.c inda ake watsa labarai akan zaɓen da za'ai na cikin gida, Abbou numfasawa yyi yace "Aryan tayaya zan baka auran yarinyar dani kaina bansan wacece ita ba?" kan Aryan a ƙasa yace "Abbou Please, i love her da gaske zan aureta babu ruwana dako wacece ita,tunda dai yaya ne yazo da ita ai shikenan" Mama dake sakkowa tayi saurin faɗin "kulll na ƙara jin wannan maganar mu zaka janyowa jafa'i,yarinyar da take da gayyar aljanu uban me zakai da ita..., ohhh banda yaran zamani wazai kalli idon ubansa yace aure ya keso,mu namu auran sai munje ɗaki muke ganin wanda aka ɗaura mana aure dashi,yana ta rarrayarmu sbd mu zauna dashi,huuuuuh!! zamani ya lalace duniya ina zaki damu" haɗe rai Aryan yyi yace "kee sbd kinƙi auren shine zaki hana wasu? kuma yaushe nace aure na keso da zakimin sharri,idanma shi nakeso meye ruwanki ne kinjini da mata" salati ta rafka tace "uwarka salamutu da ita kake bani ba,shiyasa gsky tayi ƙaranci daga nace kayi aurenka abinka yafi ka zauna Kamar wannan basa mudan shine zakai min sharri,ato ai darajar ɗa namiji sai da mata,itako mace darajarta ɗakin mijinta" ta ƙare maganar tana shirin zama kan kujera taji ta zauna a ƙafar mutum da sauri tayi baya ganin ƙafar mutum,wani ihu tayi sbd arba da Jalilerh da tayi a ƙawance jikinta ya ɗauki rawa ta fara faɗin "wa'innahu sulaimanu" wani murmushin gefen baki Jalal yyi kafin ya ɗauke kansa yaci gaba kallon labaran, Aryan ne ya kalli Abbou yace "Abbou Please" kallon sa Abbou yyi yace "tambayi yayanka" kallon Jalal yyi wanda ya ɗauke kai tamkar ba yaji abinda suke faɗa,cikin Muryar damuwa Aryan yace "Please yaya help ur biogical brother" miƙewa Jalal yyi yace "bana da lokacin wannan shirmen..
Yana faɗin hakan ya shige part ɗinsa,Hibba na zaune ita da Hajja Ayushert ta kalli mahaifiyarta tace "Hajja what should I do,ina son shi? Wannan lokacin kine na samawa gudan jininki farin cikinta,mai yasa baki son abinda na keso,ina da kuɗi ilimi,dukkan abinda na keso ina samu,mene yasa ba zaki tayani samun soyayya ba?mene yasa keda Dad bazaku tayani son abinda nake so ba" ta ƙare maganar cikin rawar Murya, kallon ta Hajja tayi tace "kuɗi na iya siyan komai Hibba,amma ban isa na siya maki soyayya da kuɗi ba,bana da wannan ikon,tayaya ma zan tayaki son abinda ban sani ba?ke kanki baki san wane shi ba" shuru Hibba tayi domin tasan abune mai wahala Hajja ta fahimci abinda da ta keji a cikin zcyarta ba,dawa zatai sharing na damunwata ko besty zata kira ta gaya masa ya rabbi ,ta wulaƙanta kowa akan soyayya taci ZARAFI n mutane da yawa akan soyayya,da ace tasan abinda su keji kenan tabbas da batayi masu haka ba, miƙewa tayi tsaye tare da ɗaukan key ɗin motar ta,ta kalli Hajja wacce hankalinta yake kan labarai sbd maganar da taji wani Prince Hassan nayi akan ɗan takarar shugaban ƙasa tace "Hajja zani school yanzu,aƙwai wanda zanwa lectures zuwa yamma" kai Hajja ta ɗaga mata, a can Haske t.v kuwa Jalal ne zaune gaban ƴan jaridu gaba ɗaya sun saita Camera a kansa wasu kuma sun saita recording domin ɗaukan maganganunsa, ɗaya daga cikin ƴan jaridai ne mai Suna Sahabi yace "Muhammad Jalal bobo muna maka barka da zuwa,a ta ƙaice menene yaja ra'ayinka harka fito takarar shugaban ƙasa?" Hibba dake ƙoƙarin fita tayi saurin juyawa sabida sunan da taji an ambata na Muhammad Jalal bobo..