← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 87

Sashe 42

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Dariya boka Saƙib yayi kafin ya daki wani ƙoƙo daga cikin ƙoƙonan dake gabansa,nan take photon Jalilerh ya bai yana tana zaune a gaban dressing mirror tana shafa lotion daga ita sai ɗan kuntun towel,
Tsora mata ido boka Saƙib da Mubarak Yahya cibo sukai ko wanne da abinda yake saƙawa a ransa,can boka Saƙib ya ƙara dukan ƙoƙon nan take photon ya ɗauke,kana ya ɗago kai ya kalli Mubarak Yahya cibo yace
"Wannan tana da muhimmanci a gareka,idan ka sameta ba governor har shugaban ƙasa sai ka zama"
Baki ya washe domin nan take ya fahimci wacce yarinya ce domin har abada bazai manta da ita ba,numfasawa yayi cikin hanzari kuma yace
"Mene muhimmanci ta a gareni?"
Miƙewa boka Saƙib yayi yace
"Ba yanzu ba sai nan gama kaɗan zan sanar dakai muhimmanci ta,da kuma abinda za'ai mata,zaka iya tafiya duk sanda na kiraka ranar zan gabatar da ƙudiri na a kanka,kada ka manta da jaririran da kuma idanuwan"
Yana faÉ—in haka ga shige cikin wani É—an ma dai-dai cin É—aki, farin ciki fal fuskarsa ya fita tunda a hanya ya sanarwar da Lamir ya kira masa p.a É—in sa..
Da daddare Jalal ya na zaune a parlour'n sa shida Jafar yana masa bayanin abubuwan da Prince Hassan ke yaɗawa a media ya wanci duk yaɗa manufa ne da kuma tunasar da al'umma muhimmanci al'ƙawari,da kuma gaya masu irin nagartarka, ajjiye glass cup ɗin hannunsa yayi,a hankali kuma ya kalli Jafar yace
"Me kake harshashe akan wannan zaɓen?"
Wayar hannunsa Jafar yayi kafin yace
"Eh to,da alama bamu da magauta, sannan kuma ya maÉ—iÉ—i da ake dakai akan abinda ya faru yay sanyi domin yanzu ba'a maganar,abu guda mutane suke yawan surutu akai wanda nima shi yake ban mamaki da kai boddy,kuma koni ina son na san mene yasa hakan?"
Lumshe idanunsa yay kafin ya buɗe su akan Jafar,cikin ƙasa da murya kuma yace
"Mene?"
Jafar ya maida hankalinsa akan Jalal sosai kafin ya numfasa yace.
"Tayaya wanda bashi da iyali wanda bai son yadda ake mulkar iyali ba har yake tunanin mulkar dubban jama'ar gari?" Wasu ana gane adalci ne a lokacin da suke adalci a cikin iyalansu,uwa uba idan mutum ya kasance yana da zuri'a masu yawa, Jalal nima yanzu ina son nasan mene yasa aduk lokacin da akai maka maganar aure saika bauɗe? Afuwa bawai ina saka maku ido a cikin gidanku bane,amma ina kula da komai kuma ina fahimtar ka,ka girman sosai amma a yanzu ace da ba Nihila nake jira ba dana manta dayin aure,kana da dukiya,kana da ilimi,kana da kyakkyawan tsohe asali kuma nagarta,babu wata ƴar mace da zata kalleka tace bata sonka,kai ko a matan ka rasa wa zaka ɗauka, aƙwai matan da dayawa zasu kawo maka tayin soyayyar su,bama ni ba maganar da ake yanzu Aryan ma shirin yin aure yake"
hannunsa ya tura cikin sumarsa ya É—an birkita ka É—an kafin ya saki wani guntun murmushi yace
"ALLAH ya sanya alkairi"
Jafar ya kalli Jalal cikin serious magana yace
"Meye damuwarka?mene yasa baka son yin aure ina son sani indan har da gaske kallo aboki nagari kake min kuma wanda yake da kusanci dakai"
Miƙewa Jalal tare da nufar cikin bedroom yana tafe yace
"Ina sharing damuwata ne da iya zuciyata"
Yana faÉ—in hakan ya shige cikin bedroom É—insa.
Da ido Jafar ya bisa yana son fahimtar abinda yake zuciyar Jalal ta hanyar ƙurawa fuskarsa ido amma bai fahimci komai ba,domin fuskar bobo wasai take. Abu alamar damuwa ko guda.
Agogon hannunsa ya duba yaga 9 saura, miƙewa yayi shima ya fice daga cikin part ɗin Jalal
A main parlour ya tarar da Mama hannunta riƙe da mahaifi gefenta kuma Nihila ce tsaye itama sanye da Orange ɗin abaya tayi rollig kanta da vail ɗin abayar, Mama ta kallesa tace
"Kai Allah dai yay wadarar rashin ƙiba,ji yadda kake tafiya babu masali,ohhh ƙilan durune ko?"
ÆŠan haÉ—e rai yayi sabida ganin Nihila tsaye yace
"Ke kuma sa'ido Mama,banda haka mene naki da rashin ƙibata dan Allah?"
Taɓe baki tayi tana gyara zaman kalbin kanta tace
"Kaga bana da lokacin surutu yanzu, ni ba asa rariya bace maza jeka kira min Jalalu ya kaini shufin"
Waje ya nema ya zauna yace
"Tab ai sai dai kiji da kanki,nidai aka gama yiwa ba'a"
Da sauri ta juya tace
"Waye yay maka ba'a kuma? a'a wlh babu ƙyau ai haramun ne,kamar wani yay maka jikin ba Ubangiji ba"
Kusan a tare Jalilerh da Aryan suka fito daga parts É—insu,da sauri Mama ta washe baki tace
"Yawwa takwarar Jalalu ki kiramin malamin naki"
Aryan dake tsaye yay saurin faÉ—in
"Malami kuma Mama?"
Ta gefen ido ta kallesa tace
"Ehmn,ba ankul naji tana faÉ—a ba?duk da dai ba makaranta nayi ba amma nasan ai malami ake faÉ—awa"
Jafar ya miƙe tsaye yana kallon Nihila kafin ya maida direction ɗinsa zuwa ga Mama yace
"Kin faÉ—i gsky da kikace maki makaranta ba,wanda yay yasan ma'anar ta"
Bata kulasu ta kalli Jalilerh wacce har yanzu take tsaye da riga da wando sai vail da tasa ta yane sumar kanta tace
"Maza jeki kinji yarinyar kirki,na maki alƙawarin wannan lemon na zuƙa"
Kanta a ƙasa jikinta kuma sanyaye ta nufi hanyar da zata kaita part ɗin,da hanzari kuma Aryan yace
"Mama bari na kira maki shi,ita aƙwai abinda zata"
Haɓa Mama ta riƙe tace
"Kaji kinibibi,to ba sallamammiya bace ni,maza ban waje"
Bisa dole ya matsawa Jalilerh hanya ta shige ya bita da ido yana mai jin wani raÉ—aÉ—i a ransa,musamman da yay duba da kayan data saka.
Zama Mama tayi a saman kujera ta tattauna dakakken goran data zuba a bakinta, Nihila tayi dariya tace
"Me yasa kike daka goro ne bayan ya haƙora nan a bakinki?"
Harara Mama ta watsa mata kafin tace
"Sabida ban samu haƙori ba ina uwarki, yooo inama ruwanki danine ba dai ni kikaiwa ruwan dubulan ba,kawai dai nafi jin daɗin cinsa a haka,ba kiga har ƙashi nake taunawa ba"
Nihila ba tace komai ba saboda alama da Jafar yay mata da hannu da tayi shuru
Ƙwance ta samesa ya ɗaga kansa sama yana kallon silin dake cikin bedroom ɗinsa,tunani ne fal cikin ransa akan abubuwa da suke faruwa dashi,wato bayan ahhalinsa dake ƙwalla fa ran yay aure yadda al'ummar gari,to duk mene yasa hakan ke faruwa ne? Shi kaɗai ne namiji wanda bai da aure?ko kuma mulki da yake nema yasa duk hankali mutane ya dawo kansa? Yasan da ba'ai masa wannan surutu,to inama za'ai masa tunda gaba ɗaya ba'a ƙasar yay rayuwa ba,rabin rayuwarsa a yanzu haka a Paris yayi ta sai dai kuma nan gaba,kuma yasan cewa abune mai wahala yakai adadin shekarun da yay a Paris da ransa,yasan bashi yake tsara rayuwa ba amma yana roƙan Allah ya ɗauki ransa akan ya ƙara adadin shekarun da yayi a Paris,mene a duniyar da har za kaji daɗin zama a cikinta? Aure! Aure! Aure bayan da yawan mutane ba kowa yasan darajar aure ba...,"
Daga ƙofa yaji ance
"Kayiwa aure mummunar fahimta,duk ba sanin al'adun ku na sani ba da kuma yanayin zaman aurenku,amma da yadda su Mummy ke rayuwa a nan gidan zaka fahimci ba duk aka taro aka zama É—aya ba,ko anamu Yaren ya nuna mana yadda ake zaman aure da kuma yadda ake daraja auren kuma na tabbatar da hakan wajan Ammi na"
Lumshe idanunsa yay kafin ya sauke numfashi a hankali yace
"Me kika sani akan auren ke?"
Duk yadda zcyarta ke bugawa akan abinda yake addabar ta a Æ´an lokutan nan bai yana tace
"Ban san yaya aure yake ba,sabida bana da tabbacin zanyi sa,amma yadda Ammina keyi duk da ba komai take ganewa ba nasan aure a wajan hausawa yana da daraja"
Miƙewa zaune yayi kafin ya ɗan kalleta da hannu yay mata nuni data ƙarasu ciki,hannu tasa ta danne saitin zcyarta,kafin tayi ƙarfin halin shiga ta ƙarasa inda yake zaune,a gefen ƙafarsa ta zauna saman carpet tace
"Uncle Mama tace kaje"
Zamuwa yayi daga saman bed É—in ya É—ura kansa bisa shoulder É—inta yace
"Meyasa ke baza kiyi auren ba tunda kin isa?"
Runtsa idanunta tayi da ƙarfi ka ta ɗan ware bakinta tace
"Tayaya wani zai ganni a halin da nake a yanzu har yayi sha'awar aure na, muna da saɓanin addini kuma babu wani na mijin da zai sha'awar aure na,koda yayi danginsa ba lalle su aminta ba,kuna Sallah,azumi,kuna sadaka kuna bada zakka kuna ziyartar ɗakin ALLAH,uwa uba wanda babu yadda dashi ba ku kun yarda dashi,kaga muna da banbanci mai yawan gaske,wazai yarda ya ajjiye guba cikin abu mai ƙyau,na sani koda na amshi musulunci wata rana zan haɗu da fushin uwa sundu,zan fuskanci zalunci wajan jama'ar birninmu, mutum biyu zasu samin garkuwa a birnin"
Ta ƙare maganar muryarta na rawa,wajan 10seconds yace
"Su waye?"
Cikin rawar murya tace
"Uncle Jabir da Ammi"
Ta ƙare maganar tana sakin kuka,a hankali yaja idanunsa ya lumshe kukan nata da yaji ya tsananta yasa ya jawo ta jikinsa tare da rungome ta ya shiga bubbuga bayan ta,shuru sukai gaba ɗaya kafin ta miƙe da sauri daga jikinsa tace.
"Uncle ina son komawa gida, Please ka mai dani kaji"
Hannunsa yasa ta tallafo haɓarta tare da cewa
"Look at me"
Kasa kallonsa tayi sai idanunta dake zubar da ƙwalla, murmushi yay dan yasan daban ba zata kallesa ba,komai nata ya sauya saɓanin da,tana da kunya hankali nutsuwa,komai nata daban yake kallonsa a yanzu, ƙasa yay da murya yace
"Why kike son haka? Ko kin mata da saurayin naki na can me jiran ki?"
Turo baki tayi tana ƙara sautin kukanta, baya yayi ya jingina da jikin bed jin tare da zuba mata shanyayyun idanunsa,
Ajjiyar zuciya Aryan ya sauke da sauri lokacin daya gama kallonsu,tunda ɗazo ya shigo da Mama tace taji shuru yaje ya duba,fita yayi daga part ɗin yana tafe yana dailing wata number kana yay kira, ɗauka akai daga can ɓangaren Lamir yace
"Lafiya kira a wannan daren?"
Aryan kamar zai sanya kuka yace
"Aƙwai matsala Daddy Lamir"
Lamir ya kalli p.a dake kusa dashi tana driving yace
"Yanzu ina hanya,amma meke faruwa ne haka?"
Aryan ya kwashe komai ya faÉ—awa Lamir,shuru yayi yana sauraran abinda Lamir ke faÉ—a masa,cike da murna yace
"Ngd sosai Daddy Lamir"
Camerar wayar ya kunna tare da komawa É—akin
Jalal yace
"Iya jeki ƙwanta"
Kanta a ƙasa tace "me zan cewa Mama to?kasan masifa zatai min"
ÆŠan haÉ—e rai yayi yace "kakar tawa take masifa Jaalilerhhhh"
Da sauri ta É—aga kanta dan rabon da taji ya kira sunanta ta manta,da mamaki tace
"Uncle kasan sunana daman?" Juyawa idanunsa yayi yace "a'a"
Ta kwaɓe fuska tace "gashi ka faɗa yanzu" hankalinsa akan agogon ɗakin yace "a'a" turo baki tayi tace "Amma Mama tace sunanmu iri guda ne" ɗan waro idanunsa yay cike da mamaki yace "laaa haba!? Ni meye nawa sunan" sunkuyar da kanta tayi a cinyarsa tana dry ƙasa-ƙasa,hannu yasa ya ɗago ta yace "ohhyaaa out" turo baki tayi tare da marairai ce fuska girgiza kai kawai yayi kafin yasa hannu yaja lips ɗinta,baki ta buɗe zatai kuka yayi sauri bata light kiss a gefen lips ɗinta a dai-dai nan kuma yaga haske kamar na wuta ya bai yana a ɗakin.
Chapter 42 · 0% Book details