← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 87

Sashe 24

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

da wannan maganar suka gama taron,sannan suka zaɓi shugabansu mai suna Prince Hassan,gaba ɗaya matasan wajan sai murna suke suna ihun daɗi,lokaci guda ƙaunar Jalal bobo ta shiga zuƙatansu, Lamir bayan sun gama nasu meeting suka tsaida maganar da suke ganin za suyi amfani da ita wajan ruguje soyayyar da mutane sukewa Jalal bobo, a main parlour Jafar da Jalal suka samu Abbou da Dasu Mameey zaune sai kuma Lamir wanda yake zaune kusa da Mama an cika masa gabansa da kayan motsa baki, Lamir ne yace "wlcm son,kuma president to be" kallonsa Jalal yyi dan ganin inda maganar tasa ta dusa sai dai babu wata alamar da fuskar Lamir zata nuna baya cikin farin ciki, kansa ya ɗauke yace "wlcm uncle" Lamir yace "thanks sai na kejin abin arziƙi,ai nace zama bai kamani ba shine babu shiri na nemi ticket na dawo domin a fara shirin zaɓe dani" Abbou yace "Lamir amma naga kamar ba jam'iyyar kake ba,domin kowa ya sanka da President Mubarak Yahya cibo,shiyasa nake tunanin abun" murmushi Lamir yyi yace "haba Alhaji Kabeer ai gida yafi waje,tayaya zanyi adawa da jini na,dukkan abinda nake samu wajan President bazai kai alaƙar jini muhimmanci ba,dan haka muna nan zamu fafata" jinjina kai Abbou yyi cike da farin ciki kafin yace "kai abu yyi daɗi Allah ya taimake mu, Allah ya ƙara zumunci "gaba ɗaya suka amsa da "Ameen" murmushi kawai Lamir yake tare dacin abincin dake bagabansa,Jalal bai ƙara magana ba ya shige cikin part ɗinsa bayan yyi wanka ya sauya kaya zuwa na shan iska ya ƙarasa parlour'n ya ɗauki apple da maltina ya dawo saman sofa ya zauna, system yaja ya fara searching akan women trafficking ɗin da suka faɗa masa ɗazo da kuma drugs ɗin da ake shigowa dasu ba tare da Nafdac ta sani ba.

A can Birnin nufar Papa ne zaune gaban uwa sundu yana kirari tare da ɗura hannunsa a sama yana jujjuyawa tare dayin sama da ƙahon kansa,sai da ya shafe awa guda kafin wani abu ya fito daga hannun uwa sundu ya sauka a nasa hannun,da sauri ya duba hannunsa abinda ya gani ba ƙaramin tayar masa da hankali yyi ba, cikin tashin hankali ya kalli jinin sannan ya kalli uwa sundu yace "Me nai maki uwa sundu mene yasa ba zaki amshi addu'a ta ba? ko laifin jikanyata ya shafan? bana da hannu a gudunta sannan bansan inda take ba kamar yadda na faɗa maki,da nasan inda take nida kaina zan kawo maki ita ki yanke mata hukuncin daya dace da ita,domin ita kaɗai ce ta fara bijirewa umarnin ki a wannan birnin mai ciki da iko da kuma tsantsar al'ada" ya faɗa cikin harshansa na Jewish, wata ƙara uwa sundu tayi tare da fiddo da hannunta ta fisciko Papa gabanta kafin ta fara magana cikin wata iriyar murya tace "kayi babban kuskure daka bar wannan matar a cikin birninmu,babban kuskuren da kayi na barin jikanyarka data gudu, kuskure uku akai a wannan birnin wanda bazai taɓa gyaruwa ba,na farkon kai da kanka ka aikatasa,babban tashin hankalin dani uwa sundu na shiga yadda naga wani babban al'amari yana shirin tunkaro mu" zufar data yankowa Papa ce yasa yyi saurin miƙewa tsaye yace "yanzu uwa sundu mene mafita? wacce hanya za'a bi a gano inda jikanyata take sannan mu bada auranta ga Jushoa" wata dryar ta ƙarayi kafin tace "tana cikin wani hasken wanda indai ba barinsa tayi ba,baza mu taɓa samun galaba a kanta ba,duk yadda za'ai mu rabata da wannan hasken sai munyi,domin idan muka barta tabbas zata rushe mana wannan daular tsakanin ita ko hasken dole za muyiwa wani turan aljanu domin su shiga jikinsa su wargatsa masa dukkan wani shirinsa,zai kasance wannan aljanun shune zai taimaka mana wajan ganin ta dawo birnin nufar..
bayan Papa da uwa sundu suka gama tattaunawa ya fice da sauri zuwa can fadarsa inda ake zaman jiransa,yana zuwa ya samu dubban mutanan da sukai na sarar karɓar budurcin wacce tayi masu,wasu kuma sukace gsky bata da daɗin mu'amala,bata da ni'ima sannan tana da raki dan haka zasu jira wata shekarar kafin nan wasu matan sun ƙara tasuwa, Jabir yana zaune ya haɗa kansa da quiwa yana kallon yadda Katarina ke kokawa da Zulfa wacce taƙi zama sai kukan kuraye take tana nunawa Jabir teddy hannunta,bawai yana fahimtar abinda take faɗa bane,amma a tasa fahimtar yana ganin kamar wani abunne ya samu teddyn hannun nata, miƙewa yyi jiki a sanyaye ya ƙarasa inda suke tsaye tare da kallon Katarina yace "matsa gefe muga" kallonsa tayi tace "amma jikin Ummi na ban tsoro kalli abinda take?" hannu yasa ya kama hannun Zulfa da sauri ya janye sbd cizon data sakar masa a hannunsa,wata tsayawa ya daka mata kafin a hankali ya fara tofa mata addu'a yana daga tsaye,idanunta ne suka fara rufewa jikinta ya saki gaba ɗaya sai wani hayaƙi daya fara fita ta hancinsa,ganin tana shirin faɗuwa yyi saurin matsowa ta faɗa jikinsa, rungome ta yyi sosai,yana shafa kanta sai a lokacin wasu hawayen tausayinta suka fara sakko masa daga cikin idanunsa gaba ɗaya jikin nata ya rikice a ƴan kwanakin nan,gashi Papa ya hanashi barin birnin bare yaje wajan malam ya amsar mata maganin.
Jalal na zaune yana operating system turo ƙofar parlour'n sa akai a hankali ya ɗaga idanunsa yaga Mummy ce, murmushi yyi yace "wlcm Mom" shuru tayi kafin tace "me kake yanzu bobo?" ba tare daya kalleta ba yace "ina bincike ne akan wani abu Mom"shuru tayi masa tana kallon sai da yaji shurun yyi yawa yace "ya dai?" numfashi ta sauke tace "Jalilerh babu lfy wajan ƙwana biyu,baka tambayeta ba sannan nima ban gaya maka ba,kuma ita ba fitowa parlour take ba,amma ciwon nata ya tsananta" yana kallon system ɗin yace "to akaita asibiti mana" kafin Mummy tayi magana Nihila ta shigo da gudu tana haki tace "Mummy Ja...Ja.. Jalilerh c...," bai jira yaji abinda za tace ba ya fice da sauri ya nufi part ɗinsu a hanya sukaci karo da Aryan wanda ya taho da gudu gaba ɗaya sukayi cikin ɗakin..
6/10/21, 1:06 PM - Buhainat: _Littafin *Uncle ne* na kuÉ—i ne, darling ki biya ki karanta abinda zai maki soo much enjoy how to subscribe send 300 to my account 0116886423 sulaiman Naima s, union bank 600 for vip idan idan tura show me ur evidence 08119237616_

_32-33_
Chapter 24 · 0% Book details