← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 87

Sashe 41

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Da yamma wajan biyar da rabi governor Mubarak Yahya cibo ne zaune gaban wani mutumi dake sanye da wasu jajayen kaya jikinsa duk anyi rubutu da jan fenti, idanunsa manyan manya wanda ƙwayar cike ta kasance jajir tamkar zata zubar da jini,gabansa ƙasa ce da kuma wasu manyan ƙoƙuna,dariya bokan yay yace
"Kana cikin halaka wacce idan kayi sake ta faɗa maka ka shiga uku babu mai iya cireka daga cikin ta, abubuwa da yawa suna shirin faruwa amma ba zaiyu na faɗa maka yanzu ba,sai dai abu guda zakai wanda zaka iya tseratar da kujerarka da kuma mutuncinka,idan kai hakan babu shakka zaka daumawa ne tare da kujerarka babu wani wanda ya isa ya karɓa daga wajanka"
Mubarak Yahya cibo jikinsa na rawa yace
"Na maka al'ƙawarin ko mene zan aikata dukkan abinda kake so zan baka muddin ba rayuwata ka nema ba,burina ni bai huce a dauwamar dani a matsayin zaɓaɓɓe kuma shugaban dake wakilan wannan yankin na IBADAN ba,na mulki kowa na juya kowa yadda nakeso,na zama shararre tako wanne ɓangare"
Boka Saƙib yace
"Abubuwa uku muke nema wajanka,biyun farko buƙatun aljanu ne wanda suka saba maka aiki,na ukun kuma buƙata tace,domin aikin da zan maka ba ƙarami bane zan sanya kaina cikin hatsari,Amma muddun ka biyamu abin da muka ɓukata kai da mulki sai mutuwa"
Jikin Mubarak Yahya cibo yana rawa yace
"FaÉ—i abinda kake so zan baka,ko mene shi kuma komai girmansa"
Boka Saƙib yayi wata mahaukaciyar dry nan take wani hayaƙi ya fara fita ta cikin bakinsa,wajan mintuna biyar sannan yayi shuru tare da tsuke fuskarsa yace
"Muna buƙatar jarirai guda biyar sabbin haihuwa,sai kuma idanun yara masu wayo guda biyu...,"
Shuru yay na wani lokaci kafin ya É—ora da faÉ—in
"Buƙata ta ƙarshe kai da matarka muke buƙata,zanyi amfani dakai kuma zanyi amfani da matarka ne bayan kaci zaɓen"
Cikin hanzari Mubarak Yahya cibo ya ɗaga kai ya kalli boka Saƙib kana ya maida kan zuwa ƙasa yace
"Ban gane mene kake son faÉ—a ba"
Wangalelen bakinsa bokan ya buÉ—e yace
"Ina nufin zanyi amfani dakai ma'ana zamuyi luwaɗi (Astagafirullah) sannan idan kaci zaɓen zaka kawo min matarka na ƙwanta da ita,wannan bawai shawararka nake nema ba kusan dole ne sabida ka riga ka aminci da abinda nace tun kafin na gaya maka abubuwan da muke buƙata,idan kaƙi kuma zaka kaga abinda zai faru da kai"
Tunani Mubarak Yahya cibo ya fariyi,shin boka Saƙib nada cuta ko bai da ita? Kullum zasu dinga aikata hakan ko kuma na wani lokaci ne,sannan idan yaci zaɓen zai iya ƙin kawo masa matar tasa sbd burinsa ya riga daya gama cika bashi da ikon da zai sanya a ƙwace masa mulkinsa, numfashi ya sauke kana yace
"Buƙatar ka a gareni na yini guda ne? Ko kuma na wasu ranaku ne?"
Zane boka Saƙib yayi a jikin ƙasa kafin ya ɗago kai yace
"Na Sa'a biyu ne kacal,da zarar mungama shikenan ka gama aikinka sai bayan zaɓe"
Murmushi Mubarak Yahya cibo yayi yana mai jin wani farin ciki tare da anushuwa a cikin zcyarsa, gani yake tamkar ya yaci wannan zaɓen ne hakan tasa cikin sauri yace "na amince..

By
NIMCYLUV
6/26/21, 2:43 PM - Buhainat: *UCL NE*
BOOK 2

60-61
Chapter 41 · 0% Book details