← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 87

Sashe 54

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Irfan yana shiga ward ɗin ya tarar har an ɗaurawa Jalal drip ga wani bandeji da aka saka masa a gefen ƙoshinsa sbd bigewar da yay lokacin daya faɗi har kansa ya fashe,waje ya samu ya zauna yana mai ƙarewar fuskar yayan nasa kallo,banda yana da zcyar imani ai da sai zcyarsa ta buga amma tunda ya aka fara wannan abun bai nuna wani abu ba sai yanzu da rasuwar Mummy ta bugasa da ƙasa, ajjiyar zcyar Irfan ya sauke yana ta tunanin abubuwa da yawa da suka dinga faruwa,yana zaunan yaji an buɗe ƙofa ganin Dr yasa ya ɗauke kansa, Dr na ƙara zuwa ya kalli Irfan yace "Madam tana shirin farkawa ya kamata ace da wata ko wani kusa da ita" miƙewa Irfan yay kana yace "babu damuwa za'a iya barinsa shi ɗaya ko?" Dr yace "eh babu damuwa" bayan Dr yabi har zuwa room ɗin da aka ƙwantar da Jalilerh,tana ƙwance sai juya kanta take tana sauke numfashi tare dafe kanta,tsayawa yay a kanta yana mai nazarin halinda take ciki,ganin tsaiwar nada yawa yasa a hankali yaja kujera ya zauna kana ya ɗauki wayarsa ya shiga dannawa,kai tsaye I.G ya shiga ya ɗauki photon Jalal wanda ya ɗauka shida Mummy tana Murmushi kana yay sign akan photon ya rubuta R.I.P Mummy,sai kuma wasu sauran baya nan,kana yay posting,yana gamawa ya shiga twitter nan ma yay posting kusan gaba ɗayansu babu wanda yake facebook da whatsapp shiyasa daga nan ya kashe datar wayar ya shiga istigifari a ransa yana mai nemawa Mummy sauƙi wajan Ubangiji..
Tun kafin su isa gidan labari yaje wajansu Mama nan ta ƙara rikicewa ta shiga kuke kamar ranta zai fita,a haka har suka samu Mama nan aka sanya gawar Mama cikin part ɗin Abbou ana shiga matan maƙota suka fara zuwa aka shiga yiwa Mummy suttura akaci sa'a babu kitso a kanta,da sauri aka fara shiryata sbd magrib daya tawo kai,bayan an kammala shiryata Mameey taje wajan Abbou da muryarta da baya fita tace "ba za'a kira Jalal ba?haka za'a kaita?" Kallonta kawai sai kuma yace "shima yana ta kansa ne,idan kun kammala bari mu ɗauke ta" tace "an kammala daman ku ake jira" baice komai ba ya fita can ya suka shigo shida Aryan da Imran sai kuma Alhaji khamal, Lamir yazo Abbou yace "kada ka sake naga hannunka a gawar matata" fita yay daga gidan gaba ɗaya haka aka sallaci Mummy aka kaita gidanta na gsky, Nihila kowa tayi suma yakai uku data farka taga gawar Mummy ko taji ana maganar sai ta ƙara ficewa daga hayyacinta,a haka Abbou yay mata allurar bacci tana surutai..
Misalin 8 na dare a can asibiti Irfan yana can tare da marasa lfy haka yay ta zirga-zirga daga wajan Jalal zuwa wajan Jalilerh,yanzu ma yana zaune gaban gadon Jalilerh ta fara mutsi kafin a hankali ta ɗan fara shura ƙafafunta miƙewa yay ganin kamar ta farka a hankali kuma yaji tana surutai kasa kunne yay yaji tana faɗin "Uncle... Uncle..kai na...ciwo...zai fashe...,"sai kuma yaji ta fasa ihu da ƙarfi tace "Uncle wayyo za muyi accident" a dai-dai lokacin shima Jalal ya mutsa ya shiga buɗe idanunsa a hankali amma ko mutsa kansa ya kasa sbd yadda ya kejin kansa yana sara masa da ƙarfin gaske,bayar da idanunsa yay ya rufe da sauri yana mai danne saitin zcyarsa sbd ihun Jalilerh daya jiyo,sai kuma yaji an buɗe ƙofa da gudu an shigo kafin yay wani tunani yaji ta faɗo kansa tana fasa ihu tare da ƙanƙamesa ta shiga faɗin "Uncle please wake up...dan Allah ka tashi.."kasa mutsawa yay sai hannunsa ɗaya ɗaga a hankali ya ɗura a bayanta ya rungome yana sauke numfashi cikin kuka ta kifa kanta a fuskarsa ta shiga taɓa wajan da yake masa ciwo kafin kuma a hankali ta ɗura lips ɗinta saman goshinsa tana sakin wani sabon kukan...
Chapter 54 · 0% Book details