← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 87

Sashe 70

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Mameey tace "don't question me Irfan" da sauri yace "ok I'm sorry" kashe wayar tayi sannan ta kalli Laure dake shiga kitchen tace "ki cewa ta kitchen ɗin nan kada nazo na sameta ciki"da sauri Laure tace "to Hajiya" ana kiran sallar issha'i Aryan yay sallama shida su Ikram da Anty Sajida da kuma Firdausi sai wasu twisn guda biyu duk mata shekarunsu bazai huce 3 ba,sosai sukai murna da ganin ƴar uwar tasu,Anuty Sajida yayace a wajan Mameey, Firdausi kuma ƙanwa, Ikram kuma ƴar gidan Anty Sajida ce wacce Irfan ya keso, twins ɗin kuma yaran Firdausi ne,da gudu baby ta fito tama manta abinda bobo yay mata,tana zuwa ta faɗa jikin Anty Sajida rabonta da ita tun sau ɗaya da da Mameey taje da ita tana ƙarama, buɗe ido Anty Sajida tayi tace "Hajiya Salmerh don't tell me baby ce wannan,wow ma sha Allah"dry Mameey tayi tace "wlh fa gata nan tana shirin Aure"Anty Sajida tace "kai kice munzo a dai²?" Firdausi ce tai Murmushi tace "Allah dai ya jiƙan Mummy" gaba ɗaya suka amsa da ameen, ƙamshi da kuma alamun tafiyar da sukaji yasa gaba ɗaya sukai kai dubansu zuwa upstairs,a hankali Jalilerh ke sakkowa kanta ƙasa,ta sanya zumbulelen hijab har ƙasa wanda ya kance blue sai fararen idanunta da take juya,ga jajeyen lips ɗinta da suke ta ƙyalli, Firdausi ce tace "tubarkallah bisimillah,ma sha Allah, Anty wannan kyakkyawar fa?kai gsky na daɗe banga beauty irinta ba"Anty Sajida ce tace "Jalilerh right?"Mameey tace "eh kam kin ganeta kenan?" Anuty Sajida tace"gsky ta huce tunani na,hatta ɓakar fata wlh banga mai ƙyan nata ba,ko fari bazai nuna mata ƙyau ba,gashi Hajia Salmerh tana shirin kamaki a halitta" dry sukai Mameey tace "ai tubarkallah ni kina mmkin girman daughter nake,nan fa baby ta girmeta amma Yanzu bata goye baby a baya ba" Firdausi tace "itace wacce Aryan zai aura ko? gsky na tayashi murna ya samu baƙar balarabiya" ita dai tana jinsu bata iya cewa komai ba,sai da taji sun ambaci Aryan sannan ta ɗaga kai aikam ido biyu sukai tashi yana zaune saman kujera ya harɗe hannayensa yana aika mata da wani irin kallo, zamewa tayi a ƙasa cikin ƙaramar muryarta tace "Fatan kun sauka lfy?"gaba ɗaya suka amsa da lfy lou,baki baby ta taɓe kama da haura upstairs, Mameey kuma taja su Anty Sajida zuwa inda zasu sauka, parlour ya rage daga Jalilerh sai Aryan, miƙewa yay tare ƙarasawa inda take zaunan yana zuwa ya ɗuka wajanta yace "meyake faruwa dake ne?"shiru tai masa ba tace komai ba,cije lips ɗinsa yayi yace "ok tashi kije"kamar jira take ta miƙe da sauri tare dayin upstairs ne,iska ya fesar daga cikin bakinsa kafin ya juya ya nufi part ɗinsa zuciyarsa duk babu daɗi, Mama daman tunda taja Asabe ɗakinta tace "yi zamanki a nan,bayan ɗan naki gantalalle ne,yooo banda sallamamme ne tayaya zai zuba ido matarsa tana hulaƙantaki?Keba uwarsa bace?bazan manta ba a haihuwarsa har kusa makancewa kikai sbd wahala,wata rana da kwana tara yana cikin amma dake bashi da liffasi yake bari ana maki haka, a'a dama can dai ba'a san zuciyarsa ba"Asabe tace "kuma kuɗi garesa"a fusace Mama tace "uban me kuɗin nasa ya amfana maki Asabe?kina dai kallo jibi zamu koma gidan gwamnati, sabon gida da motoci da masu tsaro haka aka bawa Muhammad,haba² ai Allah ya ƙara Annabi daraja,shifa jikane a wajena amma ba kiga yadda ya kemin ba,nidai abinda na keso dake kiyi zamanki nan sai ya nemeki,kee ko nan yazo zance masa kawai kin mutu ko?"zaro ido Asabe tayi tace "mutuwa kuma?a'a adai sauya haka nan kuma nazo na mutum?"dry Mama tace "taje ji ido?kai Asabe har yau kina nan da tsoran mutuwa"daga nan kuma suka ɗura da hira suna zaune Mama tasa Laure ta cika mata ƙatuwar warmer da soyayyan naman rago,ga dafaffiyar ganda,ga farfesun kifi,haka suka cika ɗakin da nama sai ci suke,a nan sukai sallar magrib da issha'i a nan kuma bacci ya ɗauke su. Washegari da yamma Jalal da Abbou suna zaune suna maganar yadda za'a koma gidan gwamnati gaba ɗayansu, shi kuma Abbou yace a'a ya koma shi ɗaya sai baby idan an ɗaura masu aure,tunda gaba ɗaya auren saura kwana biyu,kamar daga sama suka fara jiyo ihun Jalilerh, miƙewa sukai a tare,chan kuma sukaji ta ƙara fasa wani ihun ai Jalal bai tsaya Abbou ya bashi umarni ba ya ruga da gudu zuwa upstairs,a hanya sukaci karo da ita daga ita sai wata ƙaramar riga idanunta a rufe bakinta sai kumfa yake fitarwa,tana ganinsa tayi kansa da gudu.
Chapter 70 · 0% Book details