← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 87

Sashe 16

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

send ur evidence of payement to 08119237616
ka biya ka karanta..idan ka zaɓi na...🤷🏻‍♀�
6/10/21, 1:05 PM - Buhainat: Ya saka hannunsa ya dafe saman kansa,a zuciyarsa yana mai karantu sunayen Allah guda 99,har kan ya lafa masa,kana ya fara karatun cikin nutsuwa da kuma kamala,a haka suka idar da sallah zuhur ɗin, bayan an sallame anyi azkar wasu suka buƙaci Jalal da yayi masu ƙarin karatu haka ya fara karatun nan kowa ya zauna yana sauraran sautin daddaɗar muryarsa,kowa yaja Kur'ani gabansa yana kalla amma shi idanunsa lumshe yake yana karatun cikin ƙwarewa.

bayan sun kammala sukai masa gdy shima miƙewa yyi tare da ficewa daga masjid ɗin, ƙofar get ɗin gidansu ya samu Abbou tsaye shida Alhaji muktar suna tattaunawa,suna ganinsa sukai shuru,kallon Abbou yyi kana ya kalli abokin Abbou yace "barkan ku da hutawa" cikin nuna kulawa Alhaji muktar yace "yawwa Muhammad Jalal yaya karatun" lumshe ido yyi tare da pouting lips ɗinsa yace "Allahamdulillah" yana faɗin hakan ya kalli Abbou cikin ƙasa da murya yace "Abbou ban key ɗin motarka zani duba motar dana saka a kawomin sbd gobe aƙwai inda zani mai muhimmanci" hannu Abbou yasa a aljihunsa yace "to! aikam na bar key ɗin a main parlour bari na kira Aryan ya kawo maka" girgiza kai Jalal yyi tare dayin hanyar ƙaramin get yana tafe yana faɗin "no bari naje" ya ƙarasa maganar yana shigewa cikin gidan.

Bayan shigewarsa Alhaji Kabeeru ya kalli Abbou cikin damuwa da maganar da suke yace "anya Jalal lfy yake? naga ya faɗa ko kuma a haka yake ne,kasan rabona dashi tun yana ƙarami" numfashi Abbou ya sauke cikin damuwar shima yace "Ni kaina lamarinsa yana bani mamaki,amma tun ranar daya dawo gida nasan baya cikin nutsuwarsa kuma lfy bata ishe sa ba,lamarin Jalal yana damuna shiyasa ma yanke shawarar abinda naga ya dace banda kai da liman babu wanda ya san da wannan lamarin hatta shi Jalal ɗin banso ya sani, nasan wata rana zaiyi alfahari da abinda nayi masa"
murmushi Alhaji muktar yyi domin ya fahimci manufar abokin nasa,da kuma babban dalilinsa akan wannan lamari,kuma shima yana tare dashi "yanzu yaushe za'ai kenan?"
"dole mu jira sanda liman zai dawo masjid sabida ina son komai ya tafi yadda mukeso" da wannan maganar Alhaji muktar yace "shikenan Allah ya taimaka yyi jagora" sallama sukai kowa ya shige cikin gidansa.

tura ƙaramin get Abbou yyi ya shiga cikin gidan nasa,yana shiga ya samu baba habu da Laure suna cece kucan nasu da suka saba, girgiza kai kawai yayi ya nufi cikin gidansa.

yana shiga cikin gidan ya samu Aryan da Jalilerh suna magana wacce ta shinta kenan daga bacci, duk irin baccin da tayi akan idanunsa,sabida ko cikin part ɗinsa baije ba,zama yyi akan sofa yana mai kallon Jalilerh wacce itama shi take kallo kansa ya ɗauke yace "dear naji Mummy tana kema ba kiji daɗi ba, Allah ya baki lfy ya jikin yanzu?" cikin jin daɗin kulawar daya bata tace "naji daɗi yanzu Abbou" dry Aryan ya fara yi sabida Hausar da yaji tayi Turo baki tayi tare da shagwaɓe fuska cikin Muryar shagwaɓa tace "Abbou ka ganta ko" shima Abbou danne dryar dake shirin ƙwace masa yyi yace da ɗan haɗe rai yace "rabo dashi kinji, Jalilerh shima ai bai iya magana ba" yana faɗi hakan yana juyawa bayansa sabida takun da yaji a bayansa,shima Aryan juyawar yyi, Jalilerh kuma saurin sunkuyar da kai ƙasa tayi sabida tun kafin ya ƙarasu daddaɗan turarensa yyi mata sallama, miƙewa Aryan yyi yace "Abbou zan raka yaya" da sauri Jalilerh ta riƙe hannun Aryan tace "zani" wani banzan kallo Jalal ya watsa ba wanda ya sanya tayi saurin zame hannunta daga jikin Aryan,shi kuma Aryan san bai kula da hakan ba,hannunta ya riƙe tare da sunkuyawa kaɗan yace "yanzu yaya zan raka,ki bari week end yazo sai mu fita tare da Nihila kinji beb" kanta ta gyaɗa masa alamar yadda,wani tsakin Jalal ya kuma yi ba tare kuma da yace komai ba yyi ficewarsa daga cikin gidan,yana fita ya ƙarasa jikin motar Aryan ya sanya ke ya buɗe kai tsaye mazaunin drever ya zauna,hannu yasa yaja murfin motar yyiwa motar key,da sauri Aryan ya ƙarasu yace "am sorry na tsayar dakai" lumshe ido Jalal yyi tare da fesar da wani zazzafan numfashi ta cikin bakinsa kafin yyiwa motar revers yace "no na fasa fitar dakai,naga kana abu mai muhimmanci" yana faɗin hakan yaja motar da gudu daman tuni baba Habu ya buɗe masa get,kai tsaye ya fice daga cikin gidan.

baki sake Aryan yabi motar da kallo harya fice daga cikin gidan,juyawa yyi ya koma yana shiga Jalilerh ta miƙe tsaye tare da ƙarasuwa wajan ta faɗa jikinsa tace "oyoyo" kanta ya shafa tare da janyeta a jikinsa yace "beb na fasa fitar ai tunda baki so" murmushi tayi har saida dimples ɗinta suka loma cikin jin daɗi ta ƙara shiga jikinsa tace "Thank You brother" hannunta ya kama yace "zauna kiyi kallo zan watsa ruwa na huta kafin ai la'asar" sakinsa tayi kafin ta tace "mene la'asar?" suit ɗin jikinsa ya cire tare da riƙeta a hannu yace " nasan a garinku kuna zuwa Church ko?to muma a nan muna zuwa masjid muyi ibadan mukaiwa Allah kukanmu tare da gaya masa buƙatun mu,kuma sai kiga alfarmar Annabi Muhammad (s.w.a) ya biya mana dukkan abinda muke nema wajansa" shuru Jalilerh tayi tana sauraran abinda yake faɗa mata,kafin tayi saurin faɗin "amma mene yasa bakwai roƙan jesus?" murmushi yayi mata tare da bata dukkan nutsuwarsa yace "jesus shine Annabi Isa Alaihissalam,kuma ɗa ga Maryam,shima Allah subhanahu wata'ala shine ya hallicesa kamar yadda ya halicci Annabi Muhammad,kuma babu wanda muke da ikon bauta wa sai Allah,sannan kuma muyi Annabi Muhammad mubaya'a domin shine Annabi gsky,kuma shine mai cetanmu ranar lahira" Mameey dake sakkowa daga upstrais ta ɗura da faɗin "kuma dukkan wanda ya yarda da Allah ya zama dole ya yarda da Annabi Muhammad (s.w.a)ko a Bible bayan an ambaci Annabi Isa,sai aka ambaci Annabi Muhammad wanda hakan na nufin babu wani Annabi bayan shi" ta ƙare maganar tana sakkowa daga saman bene nan.

waje ta samu ta zauna gefen da Jalilerh ke zaune tace "my dear babu wanda zai maki dole,amma dai addinin musulunci shine addinin gsky dole zaki hqr da zamanmu a tare dake sabida zaki dinga ganin abubuwan da maki san dasu ba,ina fatan Jalilerh ta gane nufi na" ita sam ta kasa gane maganarsu amma tana ɗaukan ta amatsayin gsky,domin ta samu zuciyarta da kwadayin jin labarin addinin Musulunci,gefe guda kuma idan ta tuna birnin nufar da kuma Papa,da uwa SUNDU sai taji bata ƙaunar jin abinda suke faɗa,sabida ba zata iya da azabar da za'a gana mata domin tasan hukuncin da akewa dukkan wanda ya musulunta a birnin nasu,hawayen da take ƙoƙarin mayarwa ne suka samu damar sakkowa ta cikin idanunta,da sauri Aryan ya tsuguna a gabanta yace "ohhh beb why Are you cry? ki daina kinji ban son ganin hawayen" ya ƙare maganar yana share mata hawayen tare da miƙewa yace "Mameey yunwa na keji fa,bari na fito amma" dry tayi masa tace "babu abinda ka iya sai raki kamar kai kaɗai ne mai ciki,kasan dole sai kowa ya dawo gida sannan za'a ci abinci" dry yyi mata yana shigewa part ɗinsu yana faɗin "i knew" bayan shigewarsa Nihila tayi sallama Mameey ce kawai da amsa mata banda Jalilerh wacce bata san muhimmancin amsa sallamar ba,zama tayi tsakaninsu tace "washh Mameeyna na gaji rana yunwa,kai Mameey karatu aƙwai wahala wlh" ta ƙare maganar tana kama hannun Jalilerh tace "sister muje ciki ko" miƙewa Nihila tayi tace "Mameey ya gidan shuru wai?ina bobo,yaya Ara
yan,yaya,Irfan,yaya imran duk suna ina?" miƙewa Mameey tayi ta nufi kitchen tana tafe tana faɗin "baby duk masa gidan fa" tana faɗin haka ta ƙarasa ciki ta samu Laure harta kammala girki,ta zuba komai cikin cular,itama part ɗinta ta koma domin yin wanka ta shirya kafin la'asar.

Nihila na shiga ta kalli Jalilerh tace "ina fatan ki sauya pat ɗin jikinki,kuma kinyi wanka kin sauya kaya?" girgiza kai Jalilerh tayi alamar "a'a" da sauri Nihila tace "kan uba,wlh wari za kina yi idan baki gyara jikinki,baki san najasa bace?" turo baki Jalilerh tayi domin sai maganar Jalal ta faɗo mata inda yake cewa wari take,ita kuma ta ɗauki al'ƙawari bashi mamaki sai yasan ita ya gayawa,cikin shagwaɓa tace "to yaya zanyi?" ta ƙare maganar hawaye na sauka daga cikin idanunta,cikin bathroom Nihila ta shiga ta haɗa mata ruwa mai zafi tare da saka mata turaren wanka da kuma wani magani wanda Mummy ta bata,tana gamawa ta fito tace "ga ruwa can kije kiyi wanka kamar yadda na gaya maki,idan kin gama kiyi brush ki busar da wannan tulin sumar,da alama ke ko damunki ba tayi" ita dai bata ce mata komai ba ta shige cikin bathroom ɗin.
Chapter 16 · 0% Book details