← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 87

Sashe 36

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana faɗin hakan ya juya ya nufi cikin motarsa,wani lafiyayyan murmushi yyi wanda ya ƙara fidda ai nahin ƙyansa,yana tsaye drever ya buɗe masa murfin motar ya shiga back seat ya zauna,yana zama drever yaja suka bar wajan..
Yana shiga gida ya zauna a main parlour zamansa keda wahala Nusaibat tayi sallama ta shigo cikin parlour'n,can ƙasan maƙoshinsa ya amsa, durƙosawa tayi tace "yaya ina yini" ba tare daya amma sa ba ya miƙe tsaye yana shirin shiga part ɗinsa yaji Mama tace "wannan mai kirar samudawan kike gaidawa? Kekam kema anyi kinibabbiyar yarinyar uwar ƴan shisshigi,to ni kaina gaba yake dani bare kee a dangiwa da zai kula ki?a'a wlh kema kin yiwa kanki ƙarya,ga dai shi nan banda nasan lokacin da aka haifesa wlh cewa zanyi shi ba jini na bane,yooo ina dalili zaka zauna da mutum miskili wanda ƴan uwansa bai sakarwa fuska ba bare ke,nikam da zanyi aure yabar gidan ai dana huta wannan mugun halin...nafa gaya maki ɗan tsiran da yake siyomin ya daina nida inajin ba yana yaso gani sai kuma Ubangiji ya sanya ina da tsahun rai, a'a wlh wannan mugun halin bana uwarka bane bansan ubanka Kabeeru ba,ahhh too sai dai shi kayo"tunda ta fara magana yake kallonta har taje ƙarshe shi yanzu abin nata ma dry ya fara bashi,dan yana da tabbacin shekarun Mama sun ƙara jaa tsofa ya gama cinta,dryar da dake cinsa ya ɓoye yace.

"Sai kuma gashi duk halinki na kwashe a matsayinki na wacce ta haifi uwata"

Kuka tasa tace "Saibala kinji sharri da ranar Allah ko? Wlh kaf ƴar ƴar babu wanda ya taɓa gayan magana,amma gashi ina zaman zama na zai zageni,wlh tirrrr da wannan halin"

Lumshe idanunsa yayi kana ya ware su tass a kanta can ƙasa yace.

"To nida ba haifa ta kikai ba,sai na fasa gaya maki magana" ya na faÉ—in hakan ya juya da sauri yabar wajan sbd Abbou da ya gani yana shirin sakkowa daga saman upstairs.
Zama tayi a saman sofa ta saka kuka tare da share majina,kallonsu kawai Nusaibat take itama tana ɓoye dryar dake cinta, Abbou daya gama sakkowa yace.

"A'a Mama lfy dai? Badai ƙafar bace?"

Bakin zaninta tasa ta share hawaye da majinar fuskarta tace "a'a wlh Kabeeru matarka ta haifa maka jaraba"

Da mamaki yake kallonta kafin yace "jaraba kuma?" Cikin ƙufula tace "eh jaraba mana,banda gantalalle ne shi maras kunya shine zai taƙarƙare ya laftamin zagi wanda rabuna da jin wannan zagin tun kafin na fara irgar dangi,wai kamata zai ce ba uwarsa bace kawai dan ina masa faɗa a kan yayi aure" murmushi Abbou yyi tare da zama safan sofa ya kalli nusaiy dake zaune a saman carpet yace "a'a zauna mana" cike da kunya tace "ina yini Abbou" yace "lfy Allhamdulillah" Mama ta miƙe tsaye tace "a'a wlh Kabeeru kaima ban sanka da sallama ba,gwamma kawai nabar maku gidanku na huta tunda Lamir ya dawo daman rashinsa yasa na dawo nan"

Murmushi Abbou yayi yace "Mama ki ƙwantar da hankalinki,indai akan auren Jalal ne ki ɗauka yama yi"

Washe baki tayi tace "ashe,to yaushe ne?" Abbou yace "kin san yanzu za'a fara shiga har kar compaign sbd da zaɓan da yake tunkaro mu dole mutsa da komai,dan yanzu ba zai yiwu ai masa zan can aure yana cikin wannan halin ba,zai iya cewa bazai ba amma idan akai zaɓe ya samu nasara sai muyi masa mgnar"

Shuru Mama tayi Kafin tace "to nidai dan Allah ka kallaɓa ya siyomin ɗan tsiran nan,naga ɗazo yaje shufin"

Nihila dake sakkowa daga saman upstairs tace "ai fa,ke kullum idanunki yana kansa to bari naje nace masa karya siyo" Mama ta kalli Abbou tace "a'a wlh babu ruwana dake, Kabeeru ka rabani da wannan fitsararriyar ƴar taka,kai kam wlh har tausayinka nake domin ba kayi dacen yara ba" Imran da zuwansa wajan kenan yace "tunda ke kin haifi ka milallu basai ki barmu a fitsararrunmu ba" kallonsa Abbou yayi tare yi masa daƙuwa yace "ƙaniyarka Imran" Mama tace "shi wannan ai bana saka lissafi dashi" tana faɗin hakan ta miƙe tare da shigewa part ɗinta.

Nihila tace "shifa bobo azumi yake,yace ma Mummy zai je ya ɗauko ni amma ya manta" miƙewa tayi tace "bari naje wajansa..

_Na kasa jure hutun ƙwana 7 ɗin😂ga shi nan zanna posting sau ɗaya kafin mu idda 1 week ɗin,ko nrml grp ba yi masu zanyi ba🌚a wannan tafiyar sosai nake buƙatar comments ɗinku 👏🏻_

_Littafin UNCLE NE isn't free is 300 naira 600 for vip, ki turo kuÉ—in ki ta number asusun 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616_

*By*
*NIMCYLUV*
6/18/21, 11:49 AM - Buhainat: A zaune ta samesa jikinsa jiƙe da ruwa yana sanye da farar singlet sai wando three gaiter, gabansa system ce yana ta faman dannawa kana ganinsa kasan wani muhimmin abu yake.

Zama tayi gefensa tana kallon cikin system É—in kafin ta kallesa tace "bobo shine baka É—akko ni ba"

Ba tare daya kalleta ba bare da saka ran zai tanka ta,yaci gaba da operating system ɗinsa,yana yi yana duba tym abd gaf ake dayin magrib,baki ta turo gaba tace "bobo ni ko?" A ɗan zafafe ya ɗago yace "out..!" da sauri ta miƙe tsaye cikinta na rawa tabar ɗakin,kansa ya sunkuyar yaci gaba da danna system ɗin.
Cikin kuka Nihila ta shiga parlour'n tana zuwa ta faɗa jikin Mameey tana ƙara sautin kukan ta, Mama dake zaune tayi shewa tace "huu huu Allah na gode maka, buba ya daki shila yooo daman ai mugune mene ya iya banda haɗe rai,mutum kamar wanda ake masa albishir da wani nasa ya mutu,bashi da aiki sai cin magani,idan zafin kai ne da taurin zcy wlh mijina ya gada wato kakansa,bashi da ake sai kunci da ɓacin rai,ni ban taɓa ganin wannan masifar ba sai a wajansu, a'a wlh koda mijina ya gada shi yana da ƙyauta da sun ƴan uwansa sam sam abin hannunsa bai rufe masa idanu ba, a'a wlh babu ruwansa" ta ƙare maganar ta jijjiga ƙafa.

Mameey ta kalli Nihila tace.

"Me kuma bobo yaywa babynsa?"

Cikin kuka Nihila tace "ba shine yayimin tsawa ba,wai na fice na bar masa part ɗinsa" Mameey tace "eyeee! Haka akai?" Nihila ta gyaɗa kai tamkar wata ƙaramar yarinya, Mameey tace "barni dashi zai zo ya saman kinji beb"
Mummy take zaune tana faman damawa Jalal fura wacce zai buɗe baki da ita tace "ƙilan laifinta ai,kin san da shegen surutu yana azumi taje ta ta kurasa" Mameey tace "a'a Oum Jalal kedai kawai kina bayan yaronki ne,amma tabbas zai gamu dani" murmushi kawai Mummy tayi tare da miƙewa ta nufi kitchen Laure ta samu tana haɗawa mutan gidan dinner, Laure tace "Hajiya me za'ai wa yallaɓai Jalal?" Ba tare data kalleta ba tace "a'a Laure basshi,idan kin gama naki aiki jeki kawai" Laure tace "to Hajiya sai da safe" har ta tafi Mummy tace "baba babu fa? Kin kai masa nasa?" Laure tace "laaa kinga kam ma manta" ta faɗin hakan tana ɗaukan plate ɗin da ake zuba masa abincin dare a ciki,bayan ta ɗiba tayiwa Mummy sallama ta fita a part ɗin gaba ɗaya.

Tashi Nihila tayi tana goge hawayen idanunta ta nufi upstairs,kai tsaye part ɗinsu ta shige tsaye tayi sbd ganin Jalal tana tsaye gaban wardrobe sanye da hijab hannunta riƙe da casbawa,cike mmki Nihila ta kalleta tace "ohh hello" murya ƙasa irinta wanda suke tashi a bacci Jalilerh tace "hey" Nihila ta zauna bakin bed tace "hijab? Casbawa? Duk na mene?" kallo ɗaya tasowa Jalilerh ta ɗauke kai ba tare kuma da tace komai ba, Nihila tace "wannan abun shi ake kira da kafurcin mage, alwala babu salla, tayaya zaki ɗauki hijab casbawa bayan baki san me ake cewa ba,shifa addinin Musulunci ba haka yake ba,ba yadda kuke naku za kuyi shi ba,aƙwai ɗan makulin shiga musulunci,sannan aƙwai sharuɗan shiga musulunci,idan sha'awa kike abune mai sauƙi ki shiga kuma har ki rabauta da addinin" zama Jalilerh tayi idanunta na kawo ruwa cikin raunin murya tace.

"Baby what should I do, zcy ta cike take da ƙwaɗayin wannan Addinin,kuma na amince shine addinin gsky,aduk lokacin da naji babu daɗi a raina da zarar na kasance sa a lokacin da yake tsaka da bautawa Ubangijinsa,sai naji dukkan wata damunwata tayaya,haske ya maye gurbin duhun dake zcyta"

Nihila ta kalleta tace "sai ki karɓi kalmar shiga musulunci kawai,tunda har kin amince shine addinin gsky"

Hawaye na ƙara zubu mata tace "ba wannan ce matsalar ba" Nihila tace "mece?" Gyara zama tayi tace "wani gefe na zcy yana ƙaryata yardar da nayiwa addininku,sannan zcyta na cike da tsoro da kuma fargabar abinda gaba zata haifar,ban sani ba mene gobe take kira ba,amma nasan wata rana zan iya komawa birni na,kuma da zarar sun fahimci na amshi musulunci komai zai iya faruwa baby, I'm scared ina jin tsoro nasan hukuncin kisa zai iya hawa kai na" ta ƙare maganar wani kuka na ƙwace mata.

Kallonta kawai Nihila tayi tana mai nazarin maganar Jalilerh kafin taja numfashi tace.

"Ki saurari zcyrki,ki samawa kanki nutsuwa,ki cire dukkan wani kokwanto dake addabar zcyarki wanda kike ganin shine yake kawo maki wasi-wasi,dukkan abinda zcyarki ta amince da shi ne dai-dai" tana faɗin hakan ta shige cikin bathroom, kwanciya Jalilerh tayi a saman bed tana sauke numfashi,a hankali kuma taja idanunta ta rufe,cikin ƙaramin lokacin wasu tuna ne tuna ne suka fara sauka a cikin zcyarsa.

Nihila na tafi yabi bayanta da kallo harta fice daga cikin part ɗin nasa,rufe system ɗin yayi tare da shigewa cikin bedroom, system ɗin ya ajjiye a bed side, bathroom ya shiga yyi wanka tare dayin brush ya ɗaura alwala,yana fitowa ya nufi wajan dressing mirror, lotion mai sauƙi zafi ya shafa saman farar fatarsa, kafin ya ɗauki perfume ya fesa,sai da ya gama komai ya ƙarasa wajan wardrobe ya ɗauki wata maroon ɗin jallabiya ya sanya tare da ɗaukan hirami ya ɗora a saman sumar kansa,yana gamawa ana kiran sallar magrib,fita yayi daga cikin bedroom ɗin ya ƙarasa wajan fridge ya ɗauki dabinon ajwa yay bisimillah ya sanya cikin bakinsa, lumshe idanu yayi sbd zaƙi da garɗin dabinon sai da yaji guda bakwai ya kora da ruwa.
Chapter 36 · 0% Book details