← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 87

Sashe 65

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

jinin da take zubarwa ga wani zazzafan zazzaɓi dake damunta kullum, lokacin da yaji labarin zaɓen su Jalal da kuma samun nasarar sa sosai yay murna, Abba Papa ya ƙwance wayarsa koda wasa yaƙi bashi bai son kuma dalilin hakan ba, ɓangaren Papa kuma uwa sundu ce ta sanya shi yin haka,ya rasa yaya zai yi idan yace zashi Ibadan ba lalle ya samu ganawa da Jalal ba, musamman yanzu daya samu babban matsayi ganinsa zai wahala,idan kuma ya tafi wa zai barwa Zulfa, Papa ya hana kowa zuwa inda take bare har yay tunanin bada riƙon ta zuwa wajan wani har yaje ya dawo,hatta Katarina Papa ya hanata zuwa wajan Zulfa,shi yake mata komai,dalilin hakan yaso Papa ya sahale masa auran Zulfa,amma yaƙi,yana jin baƙin cikin yadda yake samun kusanci da ita,amma yasan bashi da nufi tunda taimako yaya kuma baiyi da wata niyyar ba, Joshua ne zaune gaban Uwa sundu tana sauraran abin yake faɗa, "Allah ya taimaki Uwa sundu, Uwar mu maganin kukanmu,kiyi min izini naje neman wancan yaron da kaina,nasan zuwa yanzu ya girma,shekara wajan huɗu ai ba wasa bace,na gaji gashi har watan haɗa aure ya kusa kamawa"dry Uwa sundu ta ƙyaƙyace da ita,sai da tayi mai isar ta kafin tace "wannan aiki nane,na kira aljanun da suka shiga jikinta domin su azallata ta dawo garemu,amma sun ƙasa sbd wahalar da wanda take tare dashi yake bata,shiyasa nima na fara lalata masa tasa rayuwar ta hanyar amfani da mazantakarsa,amma maganarka ta sanya naji ina son tura mata da wasu baƙaƙen ALJANU wanda zasu tunzaruta su ɗaga mata hankali taji babu inda take son zuwa sai wannan birnin nawa,a kuma lokacin zamu samu damar haɗaka da ita domin ka amshi budurcinta.dukkan abinda aka sanya rana babu shakka zaizo sai dai idan ba'a sanya masa ba,kamar yau Deen yaci zaɓe gashi yau ake shirin rantsar dashi a matsayin Governor Ibadan,harabar gidan gwamnatin cike da dubban jama'a baƙi da kuma na cikin garin,kowa ka gani yasha sabbin kaya,wasu ma kallar tutar jam'iyyar suka sanya a jikinsu,su Abbou suna can cikin bayan baƙi kowa yasha ado cikin sabbin kaya masu tsadar gske, Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo kowa yana zana saman wata lafiyayyiyar kujera,gabansa da bayansa wasu sabbin securities kuma manya wanda gwamnatin garin ta turosu,sanye yake cikin wata jumper fara tass mai manyan zane, ya ɗura wata baƙar hula a saman sumarsa,ga farin bluetooth daya maƙala cikin kunnansa,yay wani ƙyau na musamman,amma ya faɗa idanunsa sun janye sbd masifar daya tsinci kansa ciki, yanzu haka ma azumi yake,taro yay taro baka ganin komai sai securities da ƙarar jiniya,su Mameey na can ɓangaren manyan baƙi na mata ita da Nihila wacce tasha ado cikin wani Maroon ɗin lace, Jalilerh kama cewa bata jin daɗi, Jalal bai san bata zo wajan ba, a hankali Jalal ya miƙe tsaye sbd umarnin da Cheap joji ya bashi,kana ya riƙe Alkur'anin a aka mashi,cikin harshen turanci Cheap joji ya umarce Jalal ya dinga maimaita abinda zai faɗa,tsaiwarsa ya gyara tare da lumshe idanunsa yana fesar da iska ta cikin bakinsa,kafin ya ware idanunsa ya sauke saman dubban jama'ar da suke sauraransa, idanunsa ya mayar ya rufe kafin ya buɗe bakinsa cikin wani wata iriyar murya mai daɗin sauraran ji yace "Ni Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo nayi al'ƙawarin kare haƙƙin al'ummar da kuma kula da dokiyoyinsu cikin yadda da aminci,na rantse da Alkur'ani mai girma zanyi aiki tsakani da Allah kamar yadda na ƙudiri niyyar yi, zanyi mulki cikin ja..ja.",shiru yay sabida kasa faɗar kallamar da yay,a Cheap joji yay magana ba tare da kowa yaji mai yace bai ba,kallonsa Jalal sbd still kalmar bata zauna bakinsa ba,sai da Cheap joji ya ƙara faɗin JAJIRCEWA, lumshe idanunsa kana ya buɗe su ya saita bakinsa saman speaker yace...
Chapter 65 · 0% Book details