← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 87

Sashe 51

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

I'm sorry bana iya ƙarasawa,ina typing with tears a idanuna..

Uncle ne isn't free is for sale just pay before you read 300 naira asusun biya 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616

By
NIMCYLUV
7/3/21, 8:11 AM - Buhainat: _74-75_
Sau wajan uku motar na mirginawa tsakiyar titi, Abbou na cikin motarsa yay saurin yin baya cikin tashi hankali tsoro firgici dana sani, da suka masa rufdugu lokaci guda, Nihila tuni ta fasa ihu ta fara kiran sunan Mummy, Mameey kam tashin hankalin abinda ke faruwa yasa ta kasa kwakkwaran mutsi sai numfashi take saukewa, Abbou yana parking a gefen titi yama rasa me zai yi gashi dai a zahiri motar yake amma gaba ɗaya tunaninsa baya ga motar,can yay ƙarfin halin ƙarasawa wajan motar domin ba ƙaramin tension yake ciki ba,a lokacin da zaka tsaga jikinsa ba lalle jini ya fita ba, kasancewar ranar zaɓe ne sai ya tashi babu kowa a titin domin ko babura basa hucewa balle motoci,wayarsa ya ɗauka yama rasa wacce number zai kira,kawai yay shahada ya dannawa ambulance kira,tare dayi masu ƙwatance,suna nan tsaye domin ba zasu iya mirgina motar ta dawo dai-dai, ba wajan 20minutes Abbou ya fara jiyo jiniyar ambulance ɗin,kafin cikinar 22minutes ambulance ɗin sun ƙara su wajan,dasu da Abbou aka haɗu waje guda aka tayar da motar,da sauri Abbou ya nufi side ɗin Jalal yana zuwa ta wajan glass ɗin daya fashe ya zura hannunsa tare da buɗe murfin motar, zuciyarsa ce ta bada sauti da ƙarfi dammmm sbd ganin Jalal da yay zaune akan kujera ya kifa kansa akan motar,cikin sauri Abbou ya shiga kukawar ɗaga Jalal wando ko mutsi bayayi,sai daya ɗaga sa sannan yaga Jalilerh ƙwance a jikin Jalal ashe daman Jalal ɗin shiyasa rufeta da jikinsa,gaba ɗayansu babu mai numfashi a jikinsu kuma ko ɗigwan jini babu a jikinsu,gaba ɗaya aka fito dasu daga cikin motar zuwa cikin ambulance ɗin,gaba ɗaya kan Abbou ya kulle yama manta tare da Mummy suke gaba ɗaya tunaninsa tana motarsa,dai da wani police yace "aƙwai wani a back seat ne?" Da sauri Abbou ya dawo wajan motar shida wasu ƴan sanda kasa buɗe ƙofar yayi sbd jinin da yaga yana zuba ta ƙasan murfin motar,suna motar murfin motar suka samu Mummy ƙwance jini na zuba ta gefen kanta a gani glass daya caketa a wuya,da sauri aka ɗura ta a kan bed zuwa cikin ambulance ɗin, Nihila na ganin Mummy ta ƙara fasa wani ihun tana kiran sunanta tare dayin wajanta,da sauri Abbou ya riƙe,gaba ɗaya aka sanyasu a ambulance sai zuwa babban asibitin dake IBADAN,kasa driving Abbou yayi sai wani daga cikin police ɗin ne yaja motar zuwa asibitin.
Lamir suna zaune shida Governor Mubarak Yahya cibo da Hon Faisal Lawan da wasu manyan mutane,suna zaune suna tattaunawa akan yadda zaɓen ke wakana da kuma alamomin masara da suka gani,wayar Hon Faisal Lawan ce ta fara ƙara yana ɗauka yace "hello.."shiru yay kafin yace "what..?ok bari mu kunna"yana faɗin hakan ya kashe wayar yace "kirana akai wai mu kunna redio an saki breaking news" Lamir yace "kai ma dai da wahala,kasan ko labarin mene" Hon Faisal Lawan yace "bari dai muji"ya faɗi hakan yana kunna redio'n ƙaramar wayarsa,babu jimawa aka fara labaran kamar yadda aka gaya masa,da sauri Lamir ya miƙe yace "what..? ubanwa ya faɗi wannan abun?" da mamaki suke kallonsa kafin Governor Mubarak Yahya cibo yace "kai mene naka?koma waya faɗa ai ya ƙara taimakon mune" cikin ɓacin rai Lamir yace "waya fada wannan labarin a cikinku?idan kun san kuna da hannu ko faɗa min wanene?" Hon Faisal Lawan yace "haba Lamir,babu wanda yabar a cikinmu gaba ɗaya muna tare,sannan dukkan abinda ake shiryawa ai dakai ake komai,munsan cewa munyi niyyar watsa photo nan,amma kuma ba'a samu ba,banda haka ai babu abinda muka tsara wanda kai baka sanshi ba" da kallo kawai ya bisu kafin ya ɗauki key ɗin motarsa ya fice daga cikin gidan.
Mama kam tana zaune ita ɗaya sai mai aiki Laure wacce tace tazo ta zauna wajanta kafin masu gidan su dawo,tana dai zaune amma minti kaɗan zata miƙe ta leƙa waiko sun shigo, ɓangaren Aryan bawai haka nan yaƙi zuwa wajan zaɓe ba, tunda safe ya tashi da kasala da faɗuwar gaba yanzu ma yana ƙwance saman bed sai juyi yake kamar wanda bai da lfy,Imran Irfan da Jafar duk suna waje guda wajan zaɓen,ga dai alamomi nasara suna gani amma fuskokin su gaba ɗaya babu walwala,gudanar da aikin zaɓen suke babu kuzari a tare da su, Ambulance ɗin na parking a harabar asibitin nurses suka ƙarasu wajan da gadon marasa lfy, ɗaya bayan ɗaya aka dinga ɗura su akai, Nihila da Mameey banda kuka babu abinda suke, Abbou kuwa yana baka taɓa gane halin da yake ciki, lokaci zuwa lokaci yake danne saitin zcyarsa, manyan likitoci suka rufo akansu.
Lokaci kaɗan Labarin accident ɗin Dr Muhammad Jalal Kabeer bobo da iyalansa suka karaɗe Garin Ibadan da kewayanta, cikin tashin hankali Jafar da Imran da Irfan suka ƙarasu wajan,kallo guda zakai masu su baka tausayi,babu jimawa shima Lamir ya ƙarasu wajan,har yanzu babu wani labari gane da halin da suke ciki domin babu likitan daya fito,Wajan 1:40 Alhaji khamal mahaifin Nusaibat shida matarsa Hajia Atine suka ƙarasu wajan domin ko Nusaibat basu faɗawa ba, lokacin guda asibitin ya cika da mutane,sai da securities ɗin Jalal suka fara kurar mutane ya rage family ne kawai a wajan,misalin 3 dai-dai likitocin suka fito daga cikin emergency room ɗin sai share zufa suke,da sauri Abbou dasu Jafar suka miƙe tare da faɗin "Dr wanne hali suke ciki?"goge glass ɗin hannunsa babban likitan yay kafin yace "muje office tukunna" gaba ɗaya suka mara masa baya banda Alhaji khamal da Irfan wanda ya kasa mutsi dan fargaba,kujera Dr yaja ya zauna tare da nunawa Abbou waje ya zauna,amma sam Abbou bai san me Dr yake cewa ba hankalinsa yana wani wajan daban,ga wani sarawa da kansa yake yana runtsa idanunsa sai yaga abubuwa da yawa suna maza gizo a cikin idanunsa, Jafar ne ya kama hannun Abbou ya zaunar da shi a kan kujera kana yace "Dr yaya ake ciki ne Please,ka faɗa mana halin da suke ciki ka riga kasan ko waye shi a wannan garin,so Please ka faɗa mana muma hankali ya kwanta" jinjina kai Dr yay kafin yace "Allhamdulillah,da farko wajan shi Ur excellence ɗin da sauƙi,ya samu tension ne,wanda shine yaja masa ɗaukewar numfashi tun kafin faruwar accident ɗin,sannan ita yarinyar tsoro ne yay mata yawa sai kuma ɗaukewar numfashi data samu wanda yaja mata ta shiga duguwar suma,to duk su biyun nan da wani lokaci zasu farko..,"shuru yyi yana sauke numfashi ba tare da kuma da yace komai ba,Imran ne yaja numfashi yace "Mummy fa?" Kallon Dr Abbou yay abinda yake ta son cewa kenan sai kuma Allah ya taimake sa,baya Dr yayi yana sauke ajjiyar zcya kafin yace "ban san yaya zance maku ba,amma dai ita sai dai mu bita da addu'a" zcyar Abbou ce ta buga da ƙarfi kafin ya tattara nutsuwar yace "kamarya?" Jafar yace "kai mana maganar da zamu fahimta Dr kasa zuƙatanmu cikin zullumi da kuma fargaba" Dr ya fesar da numfashi kafin yace "Ta samu buguwa a kanta, ma'ana kanta ya fashe,sannan ancire mata wani ƙarfe a cikin wata sanadiyar cakarta da ƙarfan yay ya tsinka mata hanjin cikinta,abu mara daɗin kuma glasses ɗin daya caki wuyanta harya taɓa maƙoshinta"Gaba ɗaya suka haɗa baki wajan faɗin "innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"kafin Jafar yace "yanzu Dr mene condition ɗin da take ciki?" Fesar da numfashi Dr yayi kafin yace "she's critical condition,amma in sha Allah everything will be fine ok"da ƙyar ya sauke ajjiyar zcya kafin ya saita numfashinsa yace "zamu iya ganinsu yanzu?"miƙewa Dr yay yace "of course"gaba ɗaya suka miƙe tare da bin bayan Dr kowa da abinda yake tunani a ransa,wani ward suka nufa kai tsaye Dr ya shiga wani special side,wajan part biyar ne a side ɗin,room ɗin farko suka tarar da Mummy ƙwance an juna mata Oxcygen ta cikin bakinta gefen kanta an naɗeshi da bandeji haka ma wuyanta, cikinta ba an sanya anduga da filasta,kana an rufe jikinta da wani green ɗin abu, ɗakin sai ƙarar na'urori gefen hannunta an maƙala mata drip yana shiga a hankali, ƙirjinta dake ɗagawa shine kawai yake nuna tana raye,da sauri Abbou ya juya domin bazai jure ganin halin da matar tasa take ciki a halin yanzu ba,cikin zallar tausayin halin da take ciki Jafar yake kallonta yana jin ƙwalla na tarar masa a idanunsa, juyawa yay ya fita a room ɗin, Imran na fita yay ya rufe ƙofar,daga nan wajan Jalilerh suka shiga itama tana ƙwance an saka mata Oxcygen sai drip,hucin numfashin dake fita ta hancinta shike nuna tana raye,amma babu kurjewa ko ɗaya a jikinta,daga nan suka nufi room ɗin da aka saka Jalal a ciki,tun daga nesa suka hango farar fatar jikinsa data ƙarayin jaaa,ga wani haske data ƙara tai fresh,da sauri Abbou ya ƙara wajan Jalal yana zuwa ya zauna tare da kama hannunsa sai a lokacin wata ƙwalla ta sauka daga cikin idanunsa, ƙwance yake flat ko riga babu jikinsa sbd wani gumi da yake haɗawa duk da sanyin a.c dake kaɗawa a ɗakin,cikin nutsuwa yake fidda numfashi,fuskarsa ta faɗa lokaci guda kamar wanda ya shekara yana jinya,ga yadda sumar kansa ta hargitse,babu abinda aka juna masa sai drip da injection da ake masa,cikin ƙasa da Murya Abbou yace "am so sorry Muhammad,nina ja maka laifi nane,dana san wanene ni da tuni na bai yana gsky,bana da ikon faɗin komai akai na sbd sa gske ban san yaya nake ba,ina da asali bana dashi ban san komai a kaina ba Muhammad,ka yafemin kada kalleni da laifin da banawa ba,ban taɓa dana sani irin na yau ba,ban taɓa ƙunci da shiga damuwa irin na yau ba, Tabbas ni me laifi ne,bansan da wanne baki zanyi maka bayani akan wanene kai ko kuma wacece mahaifiyarka,dan Allah ka gafarta min Muhammad" ya faɗa yana ƙara ƙanƙame hannunsa,wasu siraran hawaye ne suka silalo daga cikin idanun Jalal,cikin rawar jiki kuma ya riƙe hannun Abbou'nsa nasa still hawaye na kwarara a idanunsa, Jafar tuni yabar room ɗin sbd bazai iya kallon abin tausayin nan ba,lura da halin da Jalal ke ciki yasa likitoci suka rufu akan,cikin zafin nama ya miƙe tsaye tare da fisge drip ɗin da yake hannunsa,wasu likitoci ne suka nufu inda yake suna zuwa yasa hannu ya hankaɗesu cikin sauri haɗi da gudu ya fice daga room ɗin.
Chapter 51 · 0% Book details