← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 87

Sashe 34

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon lips ɗin yayi yana mamakin yadda Jafar yake bashi labari akan mace,shi dai gashi duk yadda suke kusanci da ita dai-dai da rana mai taɓa jin wani makamancin feelings ba,bawa ita kaɗai ba dukkan wasu mata babu abinda ya taɓa ji game dasu,yaga mata kala-kala a Paris amma babu wacce ya taɓa jin wani abu a kanta,me hakan ke nufi?ko dai Tabbas shi ɗin ba cikakken namiji bane mai cikakkiyar lfy?ko dai da gske shi ɗin bashi da wani abu da mace zata mura a jikinsa ne,ko dan bai taɓa tunanin yin wani abu da macen bane shi yasa baya jin komai,bisa yarda da jagorancin zcyarsa ya ƙara ƙasa da kansa tare ƙara dafe kanta ɗaya hannunsa kuma ya ɗura saman faffaɗan waist ɗinta, ware manyan idanunsa yayi yaga shi take kallo babu ko ƙiftawa a karon farko daya sakar mata wani laullasan murmushi tare da zare hannunsa ya ɗura a saman fuskarta ya rufe idanunta dashi, ƙara ƙasa yayi da kansa a dai-dai lokacin itama ta ƙara turo bakinta gaba cikasa Sa'a lips ɗinta na ƙasa ya faɗa cikin bakinsa,kansa yaji ya tsara da ƙarfin gske yayinda ita kuma ta sauke wani numfashi mai zafi da cikin bakinta ya daki nasa bakin, haɗe lips ɗinsa yayi tare mutsaso a hankali ya kuma ware laɓɓansa ya ƙara shigar da dwonlip ɗinta cikin bakinsa kafin a hankali cikin nutsuwa ya bata wani lafiyayyan hurt 😘

Uncle ne isn't free 300 for nrml grp 600 for vip 0116886423 sulaiman Naima s union bank evidence of payment 08119237616
6/12/21, 2:06 PM - Buhainat: *Uncle ne*
*End of book 1*

_Masu karantamin littafi ƙyau ta ba tare da kunyi payment ba,ina gdy masu yin payment na littafin Uncle ne nasan zallar soyayya ce sa ƙaunar littafin ina yinku a koda yaushe🥰🥰_

Da daddare Jalal ya miƙe daga kan sofa domin harya zauna ya tuna da kiran Abbou,a parlour ya samu Mama da Nihila da kuma Jalilerh wacce take kallo,babu wanda ya kalla ya haura upstairs,kai tsaye part ɗin Abbou ya nufa yana zuwa ya samesa zaune akan sofa hannunsa riƙe da jaridar daily trust, murmushi Abbou yyi yace "na ɗauka ka manta ne" zama Jalal yyi ba tare daya tanka wancan maganar ba yace "barka da hutawa Abbou" Abbou yace "yawwa ya ƙoƙari?" Jim Jalal yayi kafin yaja numfashi yace "Allahamdulillah" Abbou yace "ma sha Allah" kana ya ɗura da faɗin "Muhammad ina son ka bani a ron hankalin ka nan"kallonsa Jalal yayi ba tare kuma da yace komai ba,hakan alama ce take nunawa Abbou cewa Jalal shike saurare, Abbou ya ƙara zama yace "ban san me kake shirya wa rayuwarka ba,nayi shuru ne sbd ban son takuraka amma yanzu lokaci ne na tuna maka abinda ka manta" a hankali Jalal ya ɗaga kai ya kalli mahaifin nasa kafin ya sauke idanunsa ƙasa, Abbou yace "kana tunanin abubuwa da yawa naci gaban wasu amma kai baka tunanin yin abinda zai ƙara maka kima da mar taba a idanun jama'ar gari,kama neman shugabancin amma kai baka son ka zama shugaba a cikin gidanka, Muhammad ban son inda tunaninka yake ba,amma tabbas ya kamata ka tsaya kayi tunanin abinda yafi da cewa da taka rayuwar"tunda ya fara magana kan Jalal yana ƙasa harya gama faɗin abinda zai ce,jin shiru yayi yawa yasa Abbou faɗin "da kai nake ka tsaya kana kallo na" kallon Abbou kafin ya sauke numfashi yace "Abbou ni maganar naka ne ban gane ba shi yasa"jinjina kai Abbou yayi kafin yace "Ina nufin yanzu lokacin yayi da zaka ajjiye iyali kamar yadda kai ma na ajjiye uwar data haifeka,nasan yanzu ka gane magana ta" da sauri ya ɗago kai ga kalli Abbou,bai ce komai ba ya sauke kansa zuwa ƙasa, miƙewa Abbou yayi yace "ko ba zaka iya ba,ok jeka ma na riga nayi abinda ya dace a kanka ai" yana faɗin hakan ya shige cikin bedroom ɗinsa yabar zaune yana kallonsa..
Tsahun wani lokaci ya ɗauka zaune yana tunanin abinda Abbou ya faɗa, lumshe idanunsa few seconds ya ƙara buɗe su,wata nauyayyiyar ajiyar zcy ya sauke,cikin ransa yake faɗin,anya Abbou yasan abinda yake damunsa? Me zai sanya a wannan lokacin zaiyi masa maganar wani aure,da zai san abinda yake damunsa da shi kansa zai janye abinda yake faɗa, tayaya zai kalli wata ƴar mace yace yana so?tayaya zai iya zama da wata a matsayin matar aure,matar ma tasa,sam ba zai iya ba yana da kyau abarshi yaji da abinda yake damunsa wanda yake ƙwana dashi yake tashi dashi,a barshi da rauninsa domin shi kaɗai zai iya sarrafa kansa,ha ɗashi da wata ƴar mace kamar tunan asiri ne a garesa,bai shirya bada ƙofar da za'a fahimci wanene shi bare har a fahimci rauninsa,yasan cewa duk ranar da wani ko wata ta fahimci damuwarsa tabbas Kashin sa ya bushe,wani zazzafan numfashi ya fesar ta cikin bakinsa kafin a hankali ya miƙe tsaye ya nufi waje harya nufi dwonstrais sai koma ya juya ya nufi part ɗin Mameey ganin babu kowa a parlour ya sanya a hankali ya nufi cikin bathroom ɗinta..
A gaban mirror ya tsaya yana mai ƙarewa kansa kallo kafin a hankali ya zare ƴar t.shirt ɗin dake jikinsa faffaɗan ƙirjinsa ya zubawa idanu kamar mai tunanin wani abu kafin a hankali yaja idanunsa ya rufe,a karan farko yayi gwaji a kanta yayi kissing ɗinta har tsayin minutuna goma amma bai yasa baiji komai game da hakan ba?bai yasa baiji feelings ɗin da Jafar yake gaya masa ba?ko ƙaramin yatsansa baiji ya sauya ba ballantana gangar jikinsa ta amshi wani saƙo nada ban,to mene matsalar? Dukkan wani gwaji da zaiwa kansa ya riga ya gama yin sa amma abu ɗaya yake nuna masa a koda yaushe shine lafiyarsa lou,shin wacce macace zata yarda ta zauna dashi a haka bayan tasan lalurar dake a jikinsa?babu wata ƴar mace da zata zauna da namijin da bazai amfane ta da komai ba,duk wata mace tana da burin ganin zuri'arta,babu macen da zata zauna da mutumin da bashi da isasshiyar lafiyar bare kuma har tasan ba zata samu ƴar ƴar dashi ba,hannu yasa ya dafe ƙirjinsa sbd zafi da raɗaɗin da ya keji a cikinsa,ga yadda zuciyarsa ke bugawa da ƙarfi,runtsa idanunsa yayi tare da kofa kansa a jikin sink a hankali kuma ya fara tari tun yana kaɗan har farin ya kusa tafiya da numfashinsa sosai ya gala bai ta,yana tsaka da wannan halin wani hayaƙi mai duhun gske ya fito ta cikin madubin zuwa cikin ƙirjinsa nan take wani gudan jini ya fito daga cikin bakinsa yayinda tarin ya tsaya cak..
A hankali ya tara hannunsa zuwa jikin sink ɗin ruwa ta zuba ya wanke bakinsa tass tare fuskarsa,yana gamawa yasa hannu ya murɗa handle ɗin jikin ƙofar ya fito,ganin babu kowa ya nufi kan wata kujera ya zauna yana zama Mameey ta fito hannunta ɗauke da damammiyar dakakkiyar fura wacce tasha cikui,zama tayi a kujerar dake gefensa tace "a'a yau bobo ne a part ɗina wajan 2weeks rabon ka da leƙoni,shuru yayi mata can yace "Mameey zan sha furar Nima" kallonsa tayi na wani lokaci kafin tai murmushi tace "wannan aita Abbou Jalal ce,ka jira na dama maka wata" kai kawai ya jinjina mata gyara zama tayi tace "bobo lafiyarka lou kowa?"ɗan waro idanunsa yayi waje yana mmkin tambayar da tayi masa, tace "ka rame sosai duk wannan ƙimar da tumbin sunyi ƙasa ina tsoran wannan ramar ta shafi lafiyarka" ba tare da yace mata komai ba ya miƙe tsaye ya nufi wajan ƙofa da sauri tace "furar fa?"yace "ki bawa baby ko waccen takai maki" Mameey tace "wace waccen kuma?" Ficewa yayi bako kalleta ba, murmushi Mameey tayi domin sarai tasan wa take nufi,mmkin da yake bata yadda bai taɓa cewa Jalilerh ba,ko sunan nata ne bai sani ba ohuuu? Yana fita ya yayi downstairs a main parlour ya samu Mama zaune da farfesun kaza a gabanta hucewarsa yayi yana ƙoƙarin shigewa yaji ta saki salati tare da faɗin "huuuuu yanzu Ni kakarka wacce ta haifi uwarka kake gaba dani Jalalu,toni mene laifina a wannan abun yarinya ta fita da ganta kawai sai naje na kurotu sbd nice gantalalliya uwar bibico,yoooo wannan ma ai san zcy salon ace bani da imani yanzu gashi yarinya ta fara gaba dani sbd taga ubanta ya nayi"sai lokacin ya kalleta kamar zai shuru sai kuma yace "yaushe na haife ta to?" Cikin kumfar baki Mama tace "toooo sannu Tijjiani ina shine dai ubana kuma shi zai gayan naji,zoka matse bakina na gaya maka"bai ce mata komai ba yay shigewarsa part ɗinsa, Mama ta zauna tare da fashewa da kuka tace "OHHH ashe da gske Muhammadu gaba yake dani banda yaran zamani ubanwa zai gaba da kakarsa wlh Allah ya kaimu safiya saina haɗaka da ubanka Kabeeru,dan naga wacce gantalailliyar bayanka take bi kadama Salamatu taji labari..

Yana shiga part ɗinsa ya samu Aryan zaune a saman kujera shi ɗaya kallonsa yayi yace "lfy?" Cikin damuwa Aryan yace "na kasa jurewa abin na neman illar zcyta ban san mene yasa kaƙi fahimtar abinda na keji ba,amma ba lallai ka fahimta ba yaya musamman idan baka da interest akan abu amma duk yadda zanyi na ya kice abin yafi ƙarfin tunani na,dan Allah yaya ka fahimta ko yaya ne" ya ƙare mgnar zcyarsa tana nuna zallar damuwar da yake ciki,cikin nuna ko in kula yace "tunda ni ba mutum bane dole bazan gane ba"girgiza akai Aryan yayi yace "yaya ba haka bane,zata iya yiwuwa baka taɓa shiga halin da nake a yanzu ba, ban san yau shene hakan ya faro dani ba,sannan ba san yaushe ne zan samu sauƙin abinda na keji a cikin zcyta ba,ban san yaya akai sonta yyimin yawa a ko ina ba, gashi dalilinka ina son na rasa abinda nakeso,dan Allah yaya ka bani izini da zan bai yana soyayyar Jalilerh ga Abbou na riga na faɗa masa komai yace na nemi izininka"kallonsa Jalal yayi kafin jaa numfashi yace "amma kasan cewa baby ma ta girmi Jalilerh ko?tayaya zaka fara soyayya da ƙaramar yarinya yana da kyau kaje ka nemi age mate ɗin ka"yana faɗin hakan yayi shigewarsa part ɗinsa.
Chapter 34 · 0% Book details