← Book details Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 87

Sashe 19

Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

wajan sati guda kenan bobo baya samun zama,a haka harya samu zama da shugaban jam'iyyar kana aka bashi damar siyan Form na neman takara a take a wajan ya siyi Form ɗin ya cike,kuma a ranar aka tabbatar dashi a ɗan jam'iyyar D.R.P kuma mai neman kujerar shugaban ƙasa,a gajiya ya shigo gidan yana shiga ya nufi part ɗinsa ya zare kayan jikinsa ya nufi bathroom taken shower yyi kana ya sanya wata milk ɗin jallabiya mara nauyi, bayan ya shirya ya fito sai zabga ƙamshin yake,kai tsaye part ɗin Abbou ya nufa yana zuwa main parlour ya samu Mameey ita da ƴan ukunta da kuma Mama sai zabga Shira suke,fuska ya sauya kana yyi gyaran murya yace "gida kamar club,zaku ɗauki hakkin wasu fa" haɓa Mama ta riƙe tace "yau naga ɗan nema,ni kake ma baƙin ciki sbd ina basu labarin kuruciyata,to wlh sai dai baƙin ciki ya kasheka" bai kula taba ya haura upstrais abinsa, tsayawa yyi baƙin ƙofar har sai da Abbou ya bashi damar shiga,yana shiga ya zame ƙasan kujera kusa da Abbou yace "Barka da rana Abbou" murmushi Abbou yyi tare da ajjiye jaridar daily trust a gefen sa yace "bobo na sai na kejin labari daga sama,nida nake gidan banji ba,to ina maka addu'ar samun nasara Allah ya taimaka" sosai bobo yaji daɗin addu'ar Abbou domin abinda yake son sanar dashi kenan,cikin ƙasa da murya yace "Abbou ka amince?" kansa ya shafa yace "tayaya zanƙi abinda gudan jinina keso? naji daɗi nayi farin ciki Allah ya nuna mana lokacin Election" da "Ameen" ya amsa kana ya miƙe ya nufi dwonstrais,yana gifta ɗakin Nihila yaga inuwar mutum,a hankali ya fara takawa zuwa ɗakin yana isa yaga Jalilerh tsaye bakin ƙofar hannunta riƙe da brezia,kallonta yyi yaga daga ita sai ƙaramin towel sai rarraba idanu take,fuska ya haɗe yace "gulma ko?"turo baki tayi gaba tare da ɗan buga ƙafarta tace "ba kai ne ba" ware ido yyi waje tare da nuna kansa yace "me? ok where are you hiding?" fuska ta shagwaɓe tare da nuna masa brezia hannunta tace "wannan ne ban iya sawa ba,and kuma Mummy tace dole nasa" lumshe idanunsa yyi tare dasa hannu ya jawota zuwa gabansa kana ya juyata zuwa baya yace "muga" brezia ta bashi shi kuma ya amsa,waro ido waje yyi ganin number dake jikinta,baice komai ba ya ɓalle bottle ɗin dake jiki a hankali kuma ya saka hannunsa a gadon bayanta..

UNCLE NE is'nt free if you need my book just contact me 300 for nrml grp 600 for vip 0116886423 sulaiman naima s unioun bank.

evidence of payement 08119237616 masu fiddamin book wlh ina jin daɗin hakan Allah ya saka maku da alkairi domin kuna ƙaramin customer😍😂
6/10/21, 1:05 PM - Buhainat: _Littafin *UNCLE NE* na kuɗi ne bisa farashi mai sauƙi wanda zan kammala rubutasa cikin ƙwana 30, mai buƙata zai biya 300 masu son vip posting sau biya zasu biya 600 ta wannan asusun 0116886423 sulaiman naima s unioun bank, send ur evidence of payement to 08119237616_

*#Never lie to someone who trust's you,and never trust someone who lies to you...*

_24-25_

saurin juyowa tayi gabansa tare dasa hannunta a ƙirjinsa cikin kwaɓe fuska ta kallesa tace "Uncle baka iya ba ai" lips ɗinta ya ƙorawa idanu,kafin yaja numfashi ya sakar mata brezia a ƙasa,kana ya gyara tsaiwarsa kamar mai koyan magana yace "wake saka maki da?"turo baki tayi sai kuma ta saki dry tace "to aini bansawa" jinjina kai yyi yace "i see" bai ƙara kallonta ba ya juya yyi tafiyarsa,a main parlour ya samu samarin gidan da Mummy da Mameey da kuma Mama zaune tasa farfesun nama a gabanta,kallonsu yyi ya ɗauke kai har yaje bakin part ɗinsu ya tsaya cikin ƙasa da murya yace "time for paryer" yana faɗin hakan ya juya abinsa zuwa cikin part ɗinsa,yana shiga ana kiran sallar magrib, bathroom ya huce yyi wanka tare da ɗaura al'wala,a parlour ya samu Abbou ya fito su Irfan kuma na jiransa,a jere suka nufi masallacin bayan sunje suka samu liman ya dawo dan haka Jalal bai ƙarasa wajan tayar da sallar ba, murmushi Liman yyi yace "mu duka kai muke jira daman shekaruna sunja,bai ce komai yaje ya tayar da Sallah,bayan an idar Abbou ya buƙaci su tafi zai dawo,kallonsa Jalal yyi kamar mai son faɗin wani abu sai kawai yyi shuru ya miƙe suma sauran ƴan uwansa suka bi bayansa,haka nan kawai ya samu kansa da faɗuwar gaba wacce bai san dalilin hakanma, suna tafe su Imran na shira shidai kawai jinsu yake da kunne, Irfan ne ya kallesa yace "yaya wlh ka shiga takara a Sa'a,domin jama'a suna sonka,daman tuni suka gaji da shugabancin zalunci da shugaban ƙasa Mubarak Yahaya cibo,jiya na kunna data na kamar ance na shiga Twitter,ina shiga na fara ganin photonan ka na ibadan wasu da kayan likitoci wasu da kayan gida, jama'a sai mara maka baya suke" ya ƙare maganar yana kallon yayan nasa wanda baice masa komai ba, Aryan ne ya ɗura da faɗin "nayi mamakin yadda jama'a suka samun wannan photonan wanda komu bamu dashi,ai in sha Allah daga wannan lokacin kashin President Mubarak Yahya cibo ya bushe,zai ga yadda ake mulki mai cike da tsafta da kuma adalci" lumshe idanunsa yyi tare da fesar da iska daga bakinsa kafin ya kalli ko wannansu yace "Jafar zai zo da paster" a haka suka ƙarasa cikin gidan,suna shiga main parlour suka, zazzauna Jalal yasu shigewa part ɗinsa Mameey tayi saurin faɗin "bobo sai muke jin abin farin ciki, gsky nayi murna ƙwarai da gske, Allah ya taimaka ya kuma baka nasara" waje ya samu kusa da Mummy wacce ko inda yake bata kalla ba hakan ya tabbatar masa da fushi take dashi,bayan ya zauna ya kalli Mameey da murmushin sa na gefen baki yace "Ameen ya rabb Mameey na" hannunsa ya ɗura akan na Mummy wacce take latsa waya banza tayi masa, ganin hakan yasa ya ƙwace wayar hannunta tare da shige jikinta, ajjiyar zuciya ya sauke kafin ya fesar da numfashi yace " i missed You Mummyna,why kike fushi?" kallonsa tayi taga yadda ya faɗa idanunsa suka ƙara fitowa ga farin daya ƙara,rai ɓace tace "Muhammad tashi a jikina" zare jikinsa yyi domin tunda yaji ta ambaci sunansa yasan taje ƙarshe wajan ɓacin rai,yana tashi ta miƙe taja hannunsa har zuwa saman upstrais,da kallo su Aryan suka bisu banda Mameey wacce take murmushi daman tun ɗazo take ganin Mummy a kumbure ashe ita da bobo ne, Mama taɓe baki tayi tace "ah to shi rikon maraya ai sai mai ƙoƙari,banda haka wacce gantalalliyar ce zata iya da wannan miskilin,mutum kamar wanda akaiwa AL'BISHIR da wani nasa ya mutu,yadda zuciya take a kumbure haka fuska take kamar zai fasa ihu..,ohhh wlh da bansan shi ba bazance Kabeeru ne ya haifi Wannan basa mudan ba" Mameey data san kan zancen taja bakinta tayi shuru,su Irfan kam da idanu kawai suke kallonta domin sam basu fahimci komai a zan can nata ba.

Mummy na shiga ta zaunar dashi a ƙaramin parlour'n ta,bata ƙara kallon inda yake ba ta shiga kitchen ɗin dake part ɗin ta juna hiter tare da zuba kayan ƙamshin,sai daya tafasa ta sauke,ta haɗa masa tea mai kauri wanda yaji bonvita da madara,plat ta ɗauka ta cika masa shi da cips,cikin parlour'n ta dawo hannunta ɗauke da tray,table ta jawo gabansa tare da ajjiyesa a saman table ɗin,fuska a ɗaure ta kallesa tace "eat,kada ka rage komai" kallonta kawai yyi harta fice daga parlour'n ta nufi cikin bedroom ɗinta,ganin abincin gabansa ya sashi jin yunwar bawai dan yana so ba,shi sam bai san mene yasa abinci bai damesa ba,bai san mene yasa a duk sanda yaci abinci ya cika cikinsa ba ya kejin cikinsa nayi masa zafi,mararsa ta kumbura tana masa zugi,yana ɗaya daga cikin abinda yasa bai son cin abincin,table ɗin ya jawo gabansa tare saka spoon ya ɗauki cips ɗin yakai bakinsa,saurin lumshe idanunsa yyi sabida daɗin ɗaya ziyarci kunansa,a hankali ya dinga cin cips ɗin yana haɗawa da tea ɗin gabansa,har sai da ya cinye tas,domin bai son ya karya mata rantsuwar da tayi,yana gamawa tana shigowa hannunta ɗauke da wata damammiyar fura, zaro idanu waje yyi kana ya miƙe tare da kwaɓe fuska yace "Mummy i'm done" itama haɗe rai tayi duk da irin dariya da yaso bata,domin tasan ganin furar ya sashi miƙewa, zaunar dashi tayi tare da zama kusansa tace "haa" tsuge bakinsa yyi ba tare da yace komai ba, ajjiye furar tayi ta kama hannunsa cikin nuna ta isa dashi da kuma nuna ita ɗin uwace garesa tace.

"Rayuwa tana da sauƙi bobo,sannan kuma tana da wahala,a lokacin dakai kake tunanin abinda zakai mai sauƙi ne,wani a lokacin yake ganin mai wahala ne...,"tsayawa tayi da maganar tana kallonsa, idanunsa a rufe suke amma dukkan wani attention ɗinsa yana akanta, ɗurawa tayi da faɗin.

"wani zai maka kallon maƙiyi,dalili kana son ka mallaki abinda yake dashi lokacin,da zarar kuma ka mallaka shi zai zama koma baya sabida burinsa da dukkan abinda yake samu ya na ga wannan abun daka rabashi dashi,hakan zai sanya yaga baƙinka yaga babu wanda ya tsana sama dakai,kuma zaiyi alwashi rabaka kaima da naka farin cikin kamar yadda ka rabashi da nasa,zai sadaukar da komai nasa in dai zai dawo da farin cikinsa.." tsayawa ta ƙarayi sabida ajjiyar zuciyar da taji ya sauke, kansa ta shafa tace.

"ina jin tsoron abinda gaba zata haifar, Jalal bana son ganin wani abun ya sameka,kaine Garkuwa Nihila,nasan a yanzu ba zaka gane abinda nake nufi ba sai nan gaba,amma siyasa babu sauƙi kamar yadda kai kake tunani,kai muradin kai ne,shi kuma farin cikin sane,a naka tunanin mutum zai yarda ya rasa farin cikinsa ne..no! Jalal bazai taɓa yiyowa ba,zakai farin ciki a duk lokacin da kakeso,ina gaya maka wannan ne da nake a raye yanzu,wata rana bazan faɗa maka ba, aƙwai ranar daza tazo kayimin kallon muguwa ko azzaluma duk kana da hujjar da zakai hakan,amma hujjarka mutum biyu ne,bazan iya faɗa maka so ba sabida ni kaina ban sansu ba,amma dai an tabbatar min da hakan,kayi ƙoƙarin kula da lafiyarka, domin wata rana mutum biyu kake da ikon riƙewa kuma ƙarƙashin inuwarka.."
Chapter 19 · 0% Book details