Sashe 67
Uncle Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Murmushi Mameey tayi wanda ya zame mata jiki tace "tubarkallah,wannan gashin kamar ana ƙara masa tsayi halan ke bafulatana ce ko"shiru tayi tana ƙara sadda kanta ƙasa,sai da ta gama gyara mata gashin ta naɗesa kamar alƙaki,kana ta tace "maza shirya bobo na kiranki,kuma zaki tafi masa da abun buɗe baki,kin san azumi yayi" gabanta taji ya faɗi zuciyarta ta buga da ƙarfin gaske, marai-raice fuska tayi tace "ayya Mameey kin kallo bana da lfy" wata duguwar riga mai ɗan santsi ta ɗauko mata tare da hijab tace "babu ruwana ni,idan baki jeba ki tanadi amsar bashi"tana faɗin hakan ta fita, Jalilerh kamar tai kuka haka ta shiga sanya rigar hawaye na bin fuskarta,bayan tasa rigar harta ɗauki parfume sai kuma ta ajjiye,hijab ɗin ta ɗauka tasa har ƙasa kana ta nufi waje ido duk hawaye sai tura baki take gaba,a hankali take sauka daga benen zuwa downstairs,tana zuwa ta samu Aryan zaune shida Jafar suna magana,gaba ɗaya kallonta sukai, Musamman Jafar rabon daya ganta harya manta,sosai yay mmkin girmanta ta zama cikakkiyar budurwa,ga wani sihirtaccen ƙyau mai ɗaukan hankali data ƙara, chocolate skin ɗinta sai sharning yake yaji mayoka masu ƙyau da tsada, lipstick ɗinta yay jajir kamar ta shafa jambaki, kanta a ƙasa ta nufi kitchen tana zuwa Laure tace "yawwa yanzu daman Hajiya ta gama shirya masa"Murmushi kawai taiwa Laure kana ta ɗauki tray tai waje, shira ta mesu sunayi nan ma bata kulasu ba tai side ɗin samarin gidan, zuciyarta na bugawa ta tura ƙofar parlour'n a hankali ta shiga, lumshe idanunta tayi sbd daddaɗan ƙamshin daya daki hancinta,murya can ƙasa tai sallama,amsa mata yay kana yaci gama da danna system ɗinsa yana matse cinyoyinsa,kamar wacce ƙwai ya fashewa ta fara tafiya zuwa inda yake,tana zuwa taja ƙaramin table ɗin gabansa ta ɗura babban tray ɗin a kai,juyawa tayi zata fita kamar daga sama taji muryarsa yace "nemi waje gida zauna"tsayawa tai kamar ba taji abinda yake cewa, zuciyarta banda lugude babu abinda take,sanin cewa bazai ƙara magana ba kuma bata da ikon fita yasa ta nemi waje kusa da ƙafafuwansa ta zauna saman carpet,tana ta shiga wasa ta yatsun hannunta,duk abinda take yana kula da ita yay banza da ita,tana nan zaune harya kammala abinda yake,kana ya kashe system ɗin bai kula ta ba ya fara buɗe warmers ɗin da aka zuzzuba abincin,sakwara ce da biyar Agushi,miyar tasha nakakƙen agushi,ganyen ugu,(ki wanke,ki yanka) Sai Alaiyahu sai kifi sukumbiya,Tafarnuwa,Attaruhu,Albasa kifi banda,Nama (soyayye)sai maggi, Curry, gishiri,kayan kamshi,manja da man gyaɗa,onga,sune kayan da akai amfani dasu wajan haɗa miyar,a hankali ya sanya yatsun hannunsa ya fara cin sakwarar guda biyu kawai yaci kana ya wanke hannayensa,tare da ɗaukan malt ya fara sha ko takan farfesun da akai masa da kuma dambun naman bai bi ba,yana shan malt ɗin ya ɗan kalleta Kafin ya ɗauke kai yace "zo nan"da sauri ta kallesa sai kuma ya sunkuyar da kanta ƙasa,hawayen daya gani ƙwance a cikin idanunta yasa ya kalleta kana ya Miƙe tsaye a hankali tare da ƙarasawa inda take zaune,yana zuwa ya sanya hannunsa gaba ɗaya ya ɗagota tsaye,kallonta yay tun daga sama har ƙasa,sosai red hijab ɗin yaywa baƙar fatarta ƙyau, lumshe idanunsa yay kafin ya buɗe su a kanta, Murya can ƙasa yace "meye kike kuka?"girgiza kai tayi hawaye na ƙara bin fuskarta, haɗe rai yay sosai kafin ya ƙara saita muryarsa yace "meye?ke dawa?wani abin ke maki ciwo?"kuka ne ya ƙwance mata hakan yasa ta saki kuka ta shiga rerawa kamar ranta zai fita, ƙasa hanata yay sai ajjiyar zuciya daya sauke,cikin sanyin jiki ya saka tattausan hannunsa ya jawota zuwa gabansa a hankali kuma ya sanya hannunsa ya shiga zare zumbulelen hijab ɗin data sanya,cillashi yay saman sofa, kallonta ya shigayi from head to toe,kama ya leƙa fuskarta cikin murya mai sanyi yace "gaya min mene?"kasa magana tai sai jikinsa data faɗa ta shiga rera kuka, lumshe idanunsa yay yana jin kukanta har tsakiyar kansa,jin kukan yay yawa yasa ya sanya hannunsa duka biyun ya rungome ta a jikinsa tare da ɗura kansa a shoulder ɗinta ya shiga sauke ajjiyar zuciya.